Gwamna Ya Yi Barazana ga Sarakunan Gargajiya kan Shiga Siyasa, Ya Fadi Abin da Zai Faru da Su

Gwamna Ya Yi Barazana ga Sarakunan Gargajiya kan Shiga Siyasa, Ya Fadi Abin da Zai Faru da Su

  • Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya gargadi sarakunan gargajiya da su guji tsoma baki cikin harkokin siyasa domin kare mutuncin masarautunsu
  • Makinde ya ce ya kamata sarakuna su kasance iyaye ga kowa, su karɓi ’yan siyasa daga dukkan jam’iyyu ba tare da nuna son kai ba
  • Gwamnan, wanda zai tsaya takarar shugaban ƙasa a 2027, ya ce zai zagaya Najeriya domin neman goyon bayan ’yan ƙasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Oyo - Gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde, ya gargadi sarakunan gargajiya da su kasance 'yan ba ruwanmu a harkokin siyasa.

Gwamna Makinde ya bayyana cewa dole ne sarauta ta zama uwa da uba ga kowa ba tare da nuna bambamci ba.

Makinde ya ja kunnen sarakunan gargajiya
Gwamna Seyi Makinde na Oyo zaune a ofis Hoto: Seyi Makinde
Source: Twitter

Makinde ya yi magana a Eruwa

Makinde ya yi wannan gargaɗin ne ranar Asabar, 5 ga watan Satumban 2026 a Eruwa, yayin bikin cikar shekara guda da nadin Samuel Adegbola a matsayin Eleruwa na Eruwa, cewar rahoton jaridar TheCable.

Kara karanta wannan

Zaɓen 2027 ta fara zafi, Obi da Kwankwaso sun tura ƙalubale ga ƴan Najeriya

An karrama gwamnan a wajen taron da sarautar gargajiya ta Aare Asoludero na Ibarapaland.

Gwamnan ya ce sarakunan gargajiya ya kamata su nisanci siyasa, tare da karɓar dukkan ’yan siyasa ba tare da nuna bambanci ba.

Ya ce masarauta ta zama 'yan baruwanmu

Makinde ya bayyana cewa idan sarakuna suna son jama’a su ci gaba da girmama masarautun gargajiya, bai kamata su tsoma kansu cikin harkokin siyasa ba.

“Masarautun gargajiya ya kamata su karɓe mu baki ɗaya a matsayin ’ya’yansu,” in ji shi.

Sai dai ya yi gargaɗin cewa duk masarautar da ta shiga siyasa, za ta iya fuskantar suka daga gwamnati.

“Amma duk masarautar gargajiya da ta tsoma baki cikin siyasa, za mu zage ta. Idan za su shiga siyasa, za mu yi musu suka,” in ji Makinde.

Makinde ya yi magana kan takarar shugaban ƙasa

Da yake magana kan burinsa na neman shugabancin Najeriya, Makinde ya ce a matsayinsa na ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APM a zaɓen 2027, a shirye yake ya zagaya ko’ina cikin ƙasar.

Kara karanta wannan

Babbar magana: Abin da zai faru da masu zagi da sukar gwamnatin Tinubu

Ya ce ba zai takaita yaƙin neman zaɓensa zuwa wani yanki na musamman ba, domin yana son gabatar da manufofinsa ga ’yan Najeriya a sassan ƙasar, jaridar Vanguard ta kawo labarin.

Makinde ya ce zai mayar da hankali kan shugabanci nagari da ci gaban ƙasa yayin da yake neman goyon bayan ’yan Najeriya.

“Burina na zama shugaban ƙasa zai buƙaci na gana da jama’a sosai, tare da gabatar musu da hangen nesana na Najeriya mafi kyau a sassa daban-daban na ƙasar,” in ji shi.

Eleruwa ya yaba wa Makinde

Gwamnan ya gode wa Eleruwa da al’ummar Ibarapaland bisa karrama shi da sarautar gargajiyar, yana mai cewa taken ya zo da ƙarin nauyi.

Ya ce karramawar za ta ƙara masa ƙwarin gwiwa wajen ci gaba da yi wa jama’a hidima da kuma ba da gudummawa wajen ci gaban Najeriya.

A nasa jawabin, Eleruwa ya ce sun karrama Makinde ne saboda dimbin ayyukan ci gaba da manyan nasarorin da gwamnatinsa ta samu a faɗin Jihar Oyo.

Makinde ya ja kunnen sarakunan gargajiya
Taswirar jihar Oyo, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Makinde ya yi magana kan farashin fetur

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya yi kira da a sake duba tsarin kayyade farashin man fetur a Najeriya.

Gwamnan ya kuma yi watsi da hujjar cewa dole ne farashin fetur a cikin gida ya kasance mai tsada domin hana fitar da mai zuwa kasashen makwabta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng