Jam'iyyu 2 Sun Garzaya Kotu, Sun Ce ba Su Yarda da Sakamakon Zaben Gwamnan Osun ba
- Kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan jihar Osun ta manna kararrakin APC da PDP da ke kalubalantar nasarar Gwamna Ademola Adeleke
- Jam’iyyun biyu suna kalubalantar sakamakon zaben gwamnan jihar Osun da aka gudanar ranar 15 ga watan Agusta, 2026
- Hukumar INEC ta bayyana Adeleke, wanda ya tsaya takara a jam’iyyar Accord, a matsayin wanda ya lashe zaben da kuri’u 511,067
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Osogbo, Osun - Kotun sauraron karafe-korafen zaben gwamnan jihar Osun ta manna kararraki biyu da jam’iyyun APC da PDP suka shigar gabanta.
Jam'iyyun biyu sun dhigar da kara gaban kotun zaben ne domin kalubalantar nasarar Gwamna Ademola Adeleke a zaben gwamnan da ya gabata.

Source: Facebook
Premium Times ta rahoto cewa an manna kararrakin a allon sanarwa na sakatariyar kotun da ke Osogbo ranar Litinin, lamarin da ya fara tsarin shari’a a hukumance kan zaben gwamnan da aka gudanar ranar 15 ga watan Agusta.
APC da PDP sun shigar da kara
Wannan mataki ya biyo bayan tabbatarwar da sakataren kotun, Pefe Belemore, ya yi cewa an shigar da kararrakin da ke kalubalantar sakamakon zaben.
Belemore ya shaida wa jaridar The Nation tun da farko cewa za a manna sanarwar da ta dace a allon sanarwa na kotun kafin tsakar rana ranar Litinin.
A lokacin bude zaman kotun da safe, Belemore yana cikin harabar kotun tare da sauran jami’ai yayin da ake shirye-shiryen fara sauraron kararrakin.
Jam’iyyun APC da PDP suna kalubalantar sakamakon zaben da ya bai wa Adeleke damar sake zama gwamna karo na biyu.
Ana sa ran manna kararrakin zai bude hanya wajen mika takardun shari’a ga bangarorin da abin ya shafa kafin a fara zaman sauraron karar a kotun.
Bayanai kan kararrakin jam’iyyun
Dan takarar APC, Asiwaju Munirudeen Bola Oyebamiji, ne ya shigar da koragim jam’iyyarsa ta APC mai lamba EPT/OS/GOV/01/2026.
Oyebamiji ya shigar da karar ne a kan Adeleke, jam'iyyar Accord da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC).
A bangaren PDP kuwa, Adebayo Olugbenga Adedamola ne ya shigar da karar mai lamba EPT/OS/GOV/02/2026.
Adedamola ya shigar da karar ne a kan Adeleke, INEC da kuma jam'iyyar Accord.

Source: Getty Images
Yadda Adeleke ya lashe zaben Osun
Gwamna Ademola Adeleke, wanda ya tsaya takarar zaben a karkashin jam’iyyar Accord, hukumar INEC ta bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben da kuri’u 511,067.
Adeleke ya doke babban abokin hamayyarsa, Munirudeen Bola Oyebamiji na jam’iyyar APC, wanda ya samu kuri’u 444,815.
Gwamna Adeleke ya ziyarci Tinubu
Kun ji cewa Shugaba Bola Tinubu ya karɓi bakuncin gwamnan Osun, Ademola Adeleke, a Fadar Shugaban Ƙasa bayan ya sake lashe zaɓen gwamna.
Da yake magana bayan ganawar da suka yi, gwamnan ya ce ya ziyarci Tinubu ne domin nuna godiya gare shi kan rawar da ya taka wajen tabbatar da adalci a zaben Osun.
Asali: Legit.ng

