Bayan Sabon Zaɓen Fitar da Gwani, Tsohon Sufeta Janar Ya Zama Ɗan Takarar Gwamna

Bayan Sabon Zaɓen Fitar da Gwani, Tsohon Sufeta Janar Ya Zama Ɗan Takarar Gwamna

  • Tsohon Sufeto-Janar na ’Yan Sandan Najeriya, Mohammed Abubakar Adamu, ya zama ɗan takarar gwamnan Nasarawa
  • Kwamitin zaɓen SDP ya ce wakilai 28,637 sun kada kuri’a, inda Adamu ya samu mafi yawan ingantattun kuri’u a zaɓen da aka gudanar cikin lumana
  • Adamu ya yi alkawarin inganta ababen more rayuwa, kiwon lafiya, noma da ma’adinai, tare da kawo sauyi ga shugabanci da kuma amfanin jama’ar Nasarawa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Lafia, Nasarawa - Tsohon Sufeto-Janar na ’Yan Sandan Najeriya, Mohammed Abubakar Adamu, ya zama ɗan takarar SDP na gwamnan Nasarawa.

Hakan ya biyo bayan sake zaɓen fitar da gwani da jam'iyyar SDP mai adawa ta yi a yau Asabar 5 ga watan Agustan 2026.

Tsohon Sufeta Janar ya zama ɗan takarar gwamna
Tsohon sufeta-janar na yan sanda. Mohammed Adamu Abubakar. Hoto: Wali Vanguard.
Source: Facebook

An sake zaben fitar da gwani na SDP

Kara karanta wannan

Zaben 2027: ADC ta fitar da sunayen 'yan takararta na gwamna a jihohi 28

An gudanar da zaɓen ne ranar Asabar a Lafia, babban birnin Nasarawa, domin zaɓar ɗan takarar SDP da zai wakilci jam’iyyar a zaɓen gwamna na 2027, cewar Daily Trust.

Da yake bayyana sakamakon zaɓen, shugaban kwamitin zaɓen SDP na Nasarawa, Barrister Joseph Achille, ya ce an gudanar da zaɓen a ƙananan hukumomi 13.

Ya ce an tattara sakamakon zaɓen daga dukkan ƙananan hukumomin jihar, kafin a haɗa su domin fitar da sakamakon ƙarshe.

Ƙananan hukumomin da aka gudanar da zaɓen sun haɗa da Akwanga, Awe, Doma, Karu, Keana, Kokona, Nasarawa da Nasarawa Eggon.

Sauran ƙananan hukumomin sun haɗa da Lafia, Obi, Toto da Wamba, yayin da aka gudanar da aikin tattara sakamakon cikin bin ƙa’idojin zaɓe.

Achille, wanda sakataren kwamitin, Ibrahim Ahmad, da mamba Adeyemi Abimbola Esq. suka kasance tare da shi, ya ce wakilai 28,637 ne suka halarta kuma suka kada kuri’u.

Shugaban kwamitin zaɓen ya kuma bayyana aikin a matsayin wanda ya kasance “mai ’yanci, adalci kuma abin yarda”, kafin ya gayyaci wanda ya yi nasara zuwa wajen taron.

An gudanar da zaɓen fitar da gwani ne domin zaɓar ɗan takarar SDP a zaɓen gwamnan Nasarawa na shekarar 2027.

Kara karanta wannan

Tsakanin Atiku da Obi waye zai iya ƙalubalantar Tinubu? an fadi wanda ya zo da gaske

Tsohon IGP ya samu takara a SDP
Taswirar jihar Nasarawa da ke Arewacin Najeriya. Hoto: Legit.
Source: Original

Jawabin karɓar takarar gwamna SDP

A jawabinsa bayan karɓar takarar, tsohon IGP Mohammed Abubakar Adamu ya yi alkawarin yin aiki tukuru domin “sauya mummunan shugabancin da ake yi” a jihar.

Adamu ya yi wannan jawabi ne jim kaɗan bayan an bayyana shi a matsayin wanda ya yi nasara a zaɓen fidda gwani na maye gurbin ɗan takara.

Adamu ya ce:

"Na yi farin ciki da aka gudanar da zaɓen fidda gwani. Haka kuma ina farin ciki da aka bayyana mu a matsayin waɗanda suka yi nasara.
"Iyalina da mutanen Nasarawa suna farin ciki da aka gudanar da wannan zaɓe, kuma aka bayyana mu a matsayin waɗanda suka yi nasara.”

Ya ce idan aka zaɓe shi, gwamnatinsa za ta bai wa ababen more rayuwa da ayyukan jin daɗin jama’a muhimmanci a faɗin jihar.

INEC ta cire sunayen yan takarar gwamna

An ji cewa Hukumar INEC ta fitar da sunayen ’yan takarar gwamnan a fadin Najeriya baki daya yayyin da ake shirin zabe.

Kara karanta wannan

Amaechi ya fadi tallafin da Atiku zai sake dawo da shi bayan na man fetur

Daraktan yaƙin neman zaɓe, Mohammed Adamu ya ce tsohon IGP ya koma SDP bayan ya fice daga APC mai mulki.

Ya ce Adamu yana cikin takarar gwamna kuma suna da takardun da ke tabbatar da rajistarsa, duk da cewa INEC ta sanya wani suna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.