Dan Takarar Gwamnan APC Ya Lashe Amansa, Ya Magantu kan Nasarar Adeleke
- Dan takarar APC a zaben gwamnan Osun, Bola Oyebamiji, ya yi martai game da zaben gwamnan jihar da aka gudanar
- Oyebamiji ya yi Allah-wadai da tashe-tashen hankulan da suka faru yayin zaben, yana neman hukumomin tsaro su gudanar da bincike
- Dan takarar APC ya bukaci ’yan jam’iyyar su hada kai, su karfafa tsarin jam’iyya domin tunkarar zaben 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Osogbo, Osun - Dan takarar gwamnan APC a zaben Osun, Bola Oyebamiji ya amince da sakamakon zaben, tare da kira ga ’yan jam’iyyarsa su hada kai gabanin zaben 2027.
Ademola Adeleke, dan takarar jam’iyyar Accord, ya lashe zaben gwamnan Osun da aka gudanar ranar 15 ga watan Agusta, inda aka bayyana shi a matsayin wanda ya yi nasara.

Source: Twitter
A cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar, Oyebamiji ya gode wa ’yan APC bisa tsayawa tsayin daka wajen mara masa baya a lokacin yakin neman zabe, cewar TheCable.

Kara karanta wannan
Ministan Tinubu da ya yi murabus ya rungumi ƙaddara bayan rasa tikitin takara a zaben 2027
Dan takarar APC ya yabawa Bola Tinubu
Ya yaba musu kan “sadaukarwarsu, jajircewarsu, addu’o’insu da cikakken imanin da suka yi da shi”.
Oyebamiji ya kuma nuna godiya ga Shugaba Bola Tinubu, tsohon gwamnan Osun, Bisi Akande, da kuma ministan harkokin ruwa da tattalin arzikin teku, Adegboyega Oyetola, saboda jagoranci da goyon bayan da suka ba shi.
Dan takarar APC ya ce yayin da yake amincewa da sakamakon zaben tare da taya wanda ya yi nasara murna, bai kamata a manta da tashin hankalin da ya faru yayin zaben ba.
Ya ce:
“Yayin da muka amince da sakamakon zaben tare da taya wanda ya yi nasara murna, ba za mu iya manta da munanan abubuwan tashin hankali da suka faru da rayukan da aka rasa ba.”
Oyebamiji ya ce yana jimamin duk wadanda suka rasa rayukansu sakamakon tashin hankalin siyasa, tare da nuna goyon baya ga iyalansu.
Ya kuma yi kira ga hukumomin tsaro da abin ya shafa da su gudanar da cikakken bincike kan abubuwan da suka faru.
Oyebamiji ya bayyana cewa duk da kammala zaben, har yanzu ya kuduri aniyar ci gaba da yi wa Osun hidima, cewar Punch.
Ya kara da cewa idan akwai wasu korafe-korafe masu inganci, tawagarsa za ta ci gaba da neman “adalci da gaskiya ta hanyoyin da doka da kundin tsarin mulki suka tanada”.
Yayin da ake karkata hankali zuwa babban zaben 2027, Bola Oyebamiji ya bukaci dukkan ’yan APC da magoya bayanta su hada kai, su karfafa tsarin jam’iyyar, sannan su sake sadaukar da kansu wajen gudanar da ayyukan da ke gabansu.
Ya ce babban abin da ya fi muhimmanci a yanzu shi ne tattara magoya baya domin sake zaben Shugaba Bola Ahmed Tinubu da kuma samun nasarar dukkan ’yan takarar APC a Osun.
Bangaren Adeleke ya karyata shirin shiga APC
Mun ba ku labarin cewa Majalisar Yaƙin Neman Zaɓen Imole ta yi magana kan rahotannin cewa Gwamnan Osun, Ademola Adeleke, na shirin koma wa APC.
Ta ce ziyarar Adeleke ga Tinubu al’ada ce bayan zaɓen gwamna na musamman, kuma ba ta da alaƙa da shirin sauya jam’iyya.
Majalisar ta tabbatar wa magoya bayan Adeleke cewa gwamnan zai ci gaba da mulkin Osun da kuma yi wa al’ummar jihar hidima.
Asali: Legit.ng
