2027: Jam'iyyar NDC Ta Su Kwankwaso Ta Fitar da Sunayen Yan Takarar Gwamna a Jihohi 12

2027: Jam'iyyar NDC Ta Su Kwankwaso Ta Fitar da Sunayen Yan Takarar Gwamna a Jihohi 12

  • Jam'iyyar NDC ta musanta rahoton cewa ba ta da yan takarar gwamna a jihohi 12 yayin da zaben 2027 ke kara kusantowa
  • Mai magana da yawun NDC na kasa ya tabbatar da cewa jam'iyyar ta tsaida yan takarar gwamna a jihohi 28 da za a fafata a zaben 2027
  • NDC ta ce ita kungiyar siyasa ce ta kasa baki daya mai tsari, 'yan takara da magoya baya a dukkan jihohi 36 da Babban Birnin Tarayya, Abuja

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Jam'iyyar adawa ta NDC ta karyata rahotannin da ke cewa ba ta da 'yan takarar gwamna a jihohi 12 gabanin babban zaben 2027.

Jam'iyyar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da sakataren yada labaranta na kasa, Osa Director, ya fitar ranar Asabar, 5 ga watan Satumban 2026.

Kara karanta wannan

Trump ya gano wadanda suke son ƙasar musulunci ta Iran ta yi nasara kan Amurka

Jam'iyyar NDC.
Tutar jam'iyar adawa ta NDC a Najeriya Hoto: NDC Party
Source: Facebook

Mai magana da yawun NDC ya bayyana rahotannin a matsayin karya da kuma masu yaudarar jama'a, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.

NDC ta tsaida yan takara a jihohi 28

NDC ta jaddada cewa ta tsayar da 'yan takarar gwamna yadda ya kamata a dukkan jihohi 28 da za a gudanar da zaben gwamna a cikinsu a shekarar 2027.

Mist Osa Director ya ce:

“Domin kawar da duk wata shakka, NDC ta tsayar da 'yan takarar gwamna yadda ya kamata a dukkan jihohi 28 da za a gudanar da zaben gwamna a cikinsu a shekarar 2027.”

Jam'iyyar ta ce ita kungiyar siyasa ce ta kasa baki daya mai tsari, 'yan takara da magoya baya a dukkan jihohi 36 da Babban Birnin Tarayya, Abuja.

Ta ce:

“NDC ba jam'iyyar wani yanki ba ce. Mu yunkuri ne na kasa baki daya mai 'yan takara, tsari da magoya baya a dukkan jihohi 36 da FCT.”

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya ware gwamnonin Arewa, ya fadi matsalan da za su fuskanta a zaben 2027

Sunayen takarar NDC a jihohi 12

Jam'iyyar ta bayyana sunayen 'yan takararta na gwamna a jihohi 12 da aka ce rahotannin sun yi ikirarin ba ta da 'yan takara kamar haka:

  1. Jihar Zamfara – Sanata Kabiru Marafa
  2. Jihar Borno – Rear Admiral Ibrahim Sanusi Kasim mai ritaya
  3. Jihar Cross River – Hon. John Odey
  4. Jihar Akwa Ibom – Babanta Michael Okon
  5. Jihar Ebonyi – Nwofe Boniface
  6. Jihar Filato – Yakubu Solomon Ndam
  7. Jihar Katsina – Ilu-Barde Aliyu
  8. Jihar Kebbi – Alhaji Umar Usman Besse
  9. Jihar Yobe – Jonga Yahaya Gabakau
  10. Jihar Jigawa – Dutse Aminu Sani
  11. Jihar Taraba – Farfesa Yahaya Mohammed Sani
  12. Jihar Neja – Abdu Sidi Bomi

NDC ta ja hankalin yan jarida

NDC ta kuma bukaci kafafen yada labarai, 'yan jarida, masu rubutun shafukan intanet da masu kirkirar abubuwan da ake yadawa a kafafen sada zumunta su tabbatar da sahihancin bayanai kafin wallafa su.

Jam'iyyar NDc.
Dan takarar shugaban kasa na NDC, Peter Obi da abokin takararsa, Rabiu Kwankwaso Hoto: Peter Obi
Source: Twitter

A riwayar Vanguard, jam'iyyar ta ce:

Kara karanta wannan

Christopher Musa ya yi wa Kwankwaso da Obi raddi, ya ce Tinubu zai zarce

“Muna kira ga gidajen yada labarai, 'yan jarida, masu rubutun shafukan intanet da masu kirkirar abubuwan da ake yadawa su binciki majiyoyinsu tare da tabbatar da sahihancin bayanai kafin wallafa su.

Ta yi gargadin cewa yada bayanan da ba a tabbatar da sahihancinsu ba na iya raunana amincewar jama'a da kafafen yada labarai da kuma tsarin dimokuradiyya.

Peter Obi ya shirya kare kuri'un NDC

Kun ji cewa dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Nigeria NDC, Peter Obi, ya bayyana cewa a shirye yake ya rasa ransa domin kare kuri'unsa a zaben 2027.

Obi ya sha alwashin cewa duk waɗanda ke.shirin murɗe zaɓe mai zuwa ba za su samu nasara ba, inda ya ƙara da cewa babu wanda zai sake tsoratar da mutane.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262