2027: 'Yan Adawa Sun Kafa Kwamitin Fitar da Tsarin Kayar da APC a Kwana 30
- Jam’iyyun adawa sun kafa kwamitoci biyar na musamman domin samar da takardun farko kan yadda za su cimma burinsu na samar da ɗan takarar shugaban ƙasa daya
- Kwamitocin za su mayar da hankali kan yarjejeniyar farfaɗo da dimokuraɗiyya, tsarin gwamnat na wa’adin shekaru huɗu, shirin gyaran ƙasa da sauran abubuwa
- An bai wa kwamitocin wa’adin kwanaki 30 su kammala rahotanninsu, wanda za a gabatar domin share fage ga taron tuntuba na biyu da za a gudanar daga baya a Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Jam’iyyun adawa a Najeriya sun kafa kwamitoci biyar na musamman domin samar da tsarin da zai taimaka wajen cimma matsayar tsayar da ɗan takarar shugaban ƙasa na bai ɗaya a zaɓen 2027.
An kafa kwamitocin ne a wani taron da ƙungiyar G-100 tare da kungiyar ’yan majalisar wakilai ta 'yan adawa suka shirya a Abuja, inda aka kuma tattauna yiwuwar kafa gwamnatin sauyi mai wa’adin shekaru huɗu.

Source: Facebook
Za a gama aikin a kwana 30
The Nation ta wallafa cewa kwamitocin da aka kafa sun haɗa da na yarjejeniyar farfaɗo da dimokuraɗiyya, yarjejeniyar gwamnatin wa’adi guda.
Sauran sun hada da shirin gyaran kasa, tsarin haɗin kan jam’iyyun adawa da taswirar samun dan takarar shugaban kasa na bai daya.
A cewar sanarwar da aka fitar bayan taron, an bai wa kwamitocin kwanaki 30 domin gabatar da rahotanninsu.
An ce gabatar da rahotannin zai share fage ga gudanar da taron tuntuba na biyu, sai dai ba a bayyana ranar da za a gudanar da taron ba.
Tsarin tattaunawa da za a bi
Kakakin kungiyar ’yan majalisar wakilai ta adawa, Afam Ogene, wanda ya karanta sanarwar taron, ya ce mahalarta sun amince da fara tsarin tattaunawa mai tsari gabanin zaɓen 2027.
Vanguard ta rahoto ya ce shugabannin jam’iyyun sun amince da fifita matsalolin ƙasa kan muradun kowace jam’iyya:
“Mun amince, a matsayin shugabannin ƙasa da manyan jagororin jam’iyyunmu, mu himmatu ga tsarin tattaunawa mai tsari kan tsarin haɗin gwiwar adawa gabanin babban zaɓen 2027,”

Source: Facebook
Ogene ya ce rashin tsaro, tsadar rayuwa da ƙarancin ayyukan yi na buƙatar haɗin gwiwar siyasa da ya wuce muradun kowace jam’iyya.
ADC ta yi Allah wadai da Atiku
A wani labarin, mun ruwaito cewa tsagin ADC na Nafiu Bala ya yi Allah-wadai da abin da suka bayyana a matsayin amfani da sunan jam’iyyar da Atiku Abubakar ke yi.
Atiku ne ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC a zaɓen 2027, yayin da Sanata David Mark yake matsayin shugaban jam’iyyar na ƙasa, kuma hukumar INEC ta amince da Atiku a matsayin ɗan takara.
Sai dai ɓangaren ADC da Nafiu Bala Gombe ke jagoranta ya kuma soki Atiku kan kai batun ofishin shugaban Najeriya zuwa kotunan ƙasashen waje.
Asali: Legit.ng

