Takaitaccen tarihin Alhaji Shehu Shagari

Takaitaccen tarihin Alhaji Shehu Shagari

Shehu Usman Aliyu Shagari ya kasance shugaban kasar Najeriya na farko tsakanin shekarar 1979 da 1983, lokacin da aka fi sani da jumhuriya na biyu kafin sojoji su yi masa juyin mulki.

An haifi Shagari a ranar 25 ga watan Fabarairun 1925 cikin iyalan Magaji Aliyu da Mariama dukkaninsu Fulani a yankin arewacin Najeriya.

Shagari ya fara karatun kur'ani tun yana dan shekara hudu, kuma daga bisani ya je makarantar Elimentari dake garin Yabo kusa da kauyen Shagari, daga nan kuma ya tafi makarantar Middle a Sokoto, daga nan kuma ya je kwaleji ta Kaduna.

Bayan da ya kammala karatun sakandire, ya shiga harkar malunta a makarantun middle daban-daban a matsayin malamin kimiyya da ma tarihi.

Takaitaccen tarihin Alhaji Shehu Shagari
Takaitaccen tarihin Alhaji Shehu Shagari
Asali: UGC

Tun yana kwaleji ya fara nuna sha'awar shiga harkar siyasa, inda a shekarar 1946 shi da Malam Gambo Abuja suka kafa wata kungiyar matasa a Sokoto, kuma sun samu goyan bayan dattijai kamar Sir Ahmadu Bello da Ibrahim Gusau da kuma Malam Ahamdu Dabbaba.

A shekarar 1948 ne kuma aka amince da a hade dukkanin kungiyoyin siyasar yankin zuwa kungiyar NPC wadda daga bisani ta zama jam'iyyar da ta tsaya takara a zaben shekarar 1959.

KU KARANTA KUMA: Yanzu-yanzu: Allah ya yiwa Alhaji Shehu Shagari rasuwa

Kafin wannan shekarar ne aka zabi Shagari a matsayin wakilin mazabar Kudu-maso Kudancin Sokoto, kuma a shekarar 1958, an zabe shi a matsayin sakataren majalisar Fira minista, Sir Abubakar Tafawa Balewa.

Daga bisani Shagari ya rike mukaman minista daban-daban da suka hada da na ci gaban tattalin arzuki (1960), na kula da harkokin cikin gida (1962) da kuma na ayyuka da safiyo (1965).

Bayan juyin mulkin farko da sojoji suka yi, Alhaji Shehu Shagari ya koma gida Sokoto.

Da hawan janar Gowon ya baiwa Shagari ministan kula da harkokin tattalin arziki daga bisani kuma aka bashi ministan kudi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel