Jihohin Arewa 15 Za Su Durkushe idan Aka Dawo da Tallafin Man Fetur a Najeriya
- Farfesa Jami'ar Obafemi Awolowo (OAU), Tunji Ogunyemi ya hango gagarumar matsala ga jihohin Arewa 15 idan aka dawo da tallafin mai
- Malamin jami'ar ya ce komawa tsarin tallafin zai rage kudaden da ke shiga Asusun Tarayya, wanda yawancin jihohi ke dogaro da shi
- Ogunyemi ya bayyana Lagos, Delta da Rivers a matsayin wasu jihohin da za su iya jurewa ba tare da dogaro sosai da rabon kudaden tarayya ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Wani farfesa a Jami'ar Obafemi Awolowo (OAU), Tunji Ogunyemi, ya ce jihohi 15 na Arewacin Najeriya za su durkushe cikin watanni uku idan aka dawo da tallafin man fetur.
Ya ce komawa tsarin tallafin zai rage kudaden da ke shiga Asusun Tarayya, wanda yawancin jihohi ke dogaro da shi wajen gudanar da ayyukansu.

Source: Facebook
Ogunyemi ya bayyana hakan ne yayin wata hira a shirin Open Forum 360 da aka wallafa a Youtube, wani dandalin tattaunawa da Dare Adekanmbi ke gabatarwa.
Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya ce zai dawo da tallafin man fetur idan aka zabe shi shugaban kasa a shekarar 2027.
Farfesan OAU ya hango illar dawo da tallafi
Sai dai Ogunyemi ya gargadi cewa dawo da tallafin zai haifar da mummunan tasiri ga tattalin arzikin Najeriya.
Farfesan ya ce:
“Ina ganin zai zama bala'i matuka idan muka janye matakin cire tallafin mai a Najeriya muka koma tsarin tallafi.
“Wannan zai haifar da matsaloli guda hudu. Na farko, kudaden da ke shiga Asusun Tarayya za su ragu.
“Asusun Tarayya shi ne ginshikin rayuwar jihohi fiye da 30 a Najeriya. Jihohi kusan hudu ne kadai za su iya rayuwa ba tare da dogaro da Asusun Tarayya ba.”
Ogunyemi ya bayyana Lagos, Delta da Rivers a matsayin wasu jihohin da za su iya jurewa ba tare da dogaro sosai da rabon kudaden tarayya na wata-wata ba.

Kara karanta wannan
Shirin dawo da tallafin man fetur ya firgita shugaban APC, ya fadi illar shirin Atiku
Jihohin Arewa 15 za su durkushe
Ya kawo jihar Taraba a matsayin misalin jihar da ba za ta iya rayuwa ba tare da rabon kudaden tarayya.
Ya ce:
“Idan kuka ce a rage kudaden da ke shiga asusun, ina tabbatar muku da cewa jihohi fiye da 15 a Arewa za su durkushe. Za su durkushe cikin watanni uku.”
Farfesan ya ce tasirin zai yi muni sosai, inda jihohi za su fuskanci matsala wajen biyan albashin ma'aikata da kuma fansho.
Tasirin hakan ga gwamnatin tarayya
Ogunyemi ya kuma gargadi cewa raguwar kudaden shiga za ta shafi ikon gwamnatin tarayya wajen biyan bukatun kashe kudinta.
Ya ce tsakanin kashi 60 zuwa 70 cikin 100 na dukkan kudaden da gwamnatin tarayya ke kashewa suna tafiya ne wajen biyan bukatun yau da kullum.

Source: Facebook
Farfesa Ogunyemi ya ce mai yiwuwa Atiku yana neman samun farin jini da kuri'un jama'a ne da alkawarin dawo da tallafin man fetur.

Kara karanta wannan
Shirin Atiku na dawo da tallafin man fetur ya sake gamuwa da cikas gabanin zaben 2027
Ya ce Atiku, kasancewarsa tsohon mataimakin shugaban kasa, ya kamata ya yi karin haske kan illar da manufarsa za ta iya haifarwa.
Tsohon gwamna ya soki shirin Atiku
Kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Plateau , Ambasada Fidelis Tapgun, ya ce duk wani yunkurin dawo da tallafin man fetur zai jawo babban koma baya ga Najeriya.
Ya kuma tambayi inda dan takarar shugaban kasa na ADC, Atiku Abubakar zai samo kudaden da zai rika kashewa wajen biyan tallafin idan aka dawo da tsarin.
Asali: Legit.ng