Dan Majalisa Ya Kai Korafi gaban Shugaban Amurka kan Abin da Ake Wa Tinubu a Najeriya

Dan Majalisa Ya Kai Korafi gaban Shugaban Amurka kan Abin da Ake Wa Tinubu a Najeriya

  • Mataimakin mai magana da yawun Majalisar Wakilai, Philip Agbese, ya ce yada wasu takardun Amurka kan Bola Tinubu na iya bata sunan Najeriya
  • Agbese ya ce rikicin siyasa bai kamata ya zama sanadin lalata martabar ’yan Najeriya masu karatu, aiki da kasuwanci a kasashen waje ba
  • Dan majalisar ya bukaci gwamnatin Donald Trump ta binciki manufar masu kai bayanai kan Najeriya ta hanyar masu fafutukar siyasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Mataimakin mai magana da yawun Majalisar Wakilai, Philip Agbese, ya soki yadda wasu ’yan adawa ke yada zarge-zargen da suka danganci wasu takardun gwamnatin Amurka kan Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Hon. Agbese ya ce wannan yunkuri wani kokari ne na bata sunan Najeriya a idon kasashen waje.

Agbese.
Mataimakin mai magana da yawun majalisar wakilai, Hon. Philip Agbese Hoto: Philip Agbese
Source: Twitter

Dan majalisar ya bayyana haka ne yayin ganawa da manema labarai a Abuja ranar Laraba da yamma, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Tinubu ya yi wa gwamnoni umarni su inganta rayuwar talaka

Ya yi martani ne kan kokarin wani kamfani da ke Washington na jawo hankalin jami'an gwamnatin Donald Trump da ’yan majalisar dokokin Amurka kan wasu zarge-zargen da suka shafi Tinubu.

Agbese ya gargadi ’yan adawa

Agbese, wanda ya yi magana a madadin wasu ’yan majalisa da kungiyoyin fararen hula, ya ce bai kamata sabanin siyasa ta hanyar lalata martaba da jin dadin ’yan Najeriya da ke zaune, aiki da gudanar da kasuwanci a kasashen waje ba.

Ya ceq yada tsofaffin takardu da zarge-zargen da ba a tabbatar ba a fagen siyasar kasashen waje na iya haifar da matsala ga ’yan Najeriya da dama.

Ya ce:

“Wannan batu ya wuce siyasa. Idan ’yan siyasa masu neman mulki suka fara fitar da yakinsu na siyasa zuwa kasashen waje tare da bayyana Najeriya a matsayin kasa da ake zargin shugabancinta ya ginu kan aikata laifuffuka, ba Shugaba Tinubu kadai suke cutarwa ba.

Kara karanta wannan

Lauya ya tsage gaskiya, an ji dalilin da ya sa Amurka ba ta kama Shugaba Tinubu ba

“Suna bata sunan kowane dan Najeriya da ke tafiya, karatu, aiki, kasuwanci ko neman wata dama a kasashen waje.”

Agbese ya tura sako ga Amurka

Agbese ya ce bai kamata gwamnatin tarayya ta bari abin da ya bayyana a matsayin yunkurin siyasa na kirkirar wata badakal kan shugaban kasa ya dauke mata hankali ba.

Dan majalisar ya bukaci Shugaba Donald Trump da gwamnatinsa su binciki manufar da sahihancin mutanen da ke gabatar da kansu a matsayin masu kare muradun Najeriya kafin su dauki mataki.

Trump.
Shugaban Amurka, Donald Trump da takwaransa na Najeriya, Bola Ahmed Tinubu Hoto: Donald J. Trump, Bayo Onanuga
Source: Twitter

Ya ce:

“Muna kira ga Shugaba Trump da gwamnatinsa da su yi watsi da masu yunkurin bata wa gwamnatin tarayyar Najeriya suna, da ’yan Najeriya baki daya masu neman rayuwa mai tsafta a kasashen waje.”

APM ta nemi Amurka ta saki rahoton Tinubu

Kun ji cewa APM ta bukaci hukumomin Amurka su bayyana sakamakon rahoton FBI kan zarge-zargen safarar miyagun kwayoyi da ake wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

APM ta ce hukumomin Amurka za su iya fitar da sassan rahoton da ba za su “jefa rayuka cikin hadari, tona asirin shaidu, masu bincike ko hanyoyin da aka yi amfani da su wajen gudanar da binciken” ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262