'Za a Mutu,' Obi Ya Yi Gargadi Mai Zafi kan Magudi a Zaben 2027

'Za a Mutu,' Obi Ya Yi Gargadi Mai Zafi kan Magudi a Zaben 2027

  • Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Nigeria NDC, Peter Obi, ya bayyana cewa a shirye yake ya rasa ransa domin kare kuri'unsa a zaben 2027
  • A bayanin da ya yi Obi ya bukaci 'yan Najeriya da su tabbatar ba a sake maimaita maguɗan zaben da aka gani a lokacin babban zaben shekarar 2023 ba
  • Dan takarar tare da abokin takararsa, Rabiu Musa Kwankwaso, sun bayyana cewa jam'iyya mai mulki ba za ta samu damar tsoratar da masu zabe ko maguɗi ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar NDC, Peter Obi, ya fito fili ya bayyana cewa yana tsaye tsam kuma a shirye yake ya rasa ransa wajen kare ƙuri'unsa da na magoya bayansa a zaɓen shekarar 2027.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Ministan tsaro ya yi zarge zarge kan El Rufa'i da ke tsare

Obi ya yi kiran ne yayin wani taron tattaunawa da aka shirya a birnin Port Harcourt na jihar Rivers, inda ya ƙalubalanci 'yan Najeriya da su tashi tsaye domin hana maimaituwar irin "maguɗi da kuskuren" da aka samu a zaɓen 2023.

Peter Obi da Rabiu Musa Kwankwaso
Dan takarar shugaban kasa, Peter Obi da Rabiu Kwankwaso a wajen taron NDC. Hoto: Mr Peter Obi
Source: Facebook

Daily Trust ta rahoto cewa Obi ya sha alwashin cewa duk waɗanda ke shirin murɗe zaɓe mai zuwa ba za su samu nasara ba, inda ya ƙara da cewa babu wanda zai sake tsoratar da masu zaɓe a rumfunan zaɓe.

Ya bayyana cewa:

"Babu wanda zai sake tsoratar da mu a rumfar zaɓe. Idan ka je kowace rumfa a yau, mafi yawan jami'ai da za ka gani su biyar ne. Mafi yawan masu zaɓe kuma sun kai 40 zuwa 50.
"Babu ta yadda mutane biyar za su tsoratar da mutum 50. A wannan karon dukkanmu za mu ceto ƙasarmu. Wani ya ce, 'A shirye muke mu mutu.' Bari na gaya muku, ni ma a shirye nake na mutu."

Matsayar Obi kan tsarin IReV

A cewar Obi, za su samar da ingantaccen tsarin gudanarwa domin tabbatar da cewa babu wata barazana ko murɗiya ta kafar na'urar IReV ta hukumar INEC kamar yadda aka zarga a baya.

Kara karanta wannan

Tirkashi: An hango abin da zai hana Atiku zama shugaban kasa a 2027

Punch ta wallafa cewa ya gargaɗi cewa a wannan karon, duk wata matsala ta hanyar yanar gizo da za a kawo da gangan ba za a amince da ita ba.

A nasa ɓangaren, mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa na NDC, Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi kira ga masu ƙuri'a da su guji maimaita kuskuren baya wajen zaben tumun dare.

Jagororin NDC a Najeriya
Peter Obi da wasu manyan NDC a Najeriya. Hoto: Mr Peter Obi
Source: Facebook

Maganar zaben 2023

A wani labarin, mun ruwaito cewa a zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2023, Shugaba Bola Tinubu na jam'iyyar APC ne ya samu nasara da ƙuri'u 8,794,726.

Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya bayyana cewa a zaɓen na 2023, an yi amfani da takarar Peter Obi wajen raba ƙuri'un 'yan adawa da Atiku Abubakar.

Wike ya bayyana cewa an bar Obi ya yi nasara a sawun jihohin Kudu-maso-Kudu domin rage wa Atiku ƙarfi, inda kuma duk 'yan takarar guda uku ke haramar sake fafatawa a zaɓe mai zuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng