Trump Ya Gano Wadanda Suke Son Kasar Musulunci Ta Iran Ta Yi Nasara kan Amurka
- Shugaba Donald Trump ya zargi mambobin jam'iyyar Democrats da son Amurka ta sha kashi a yakin da take yi da kasar musulunci ta Iran
- Trump ya ce bangaren siyasar da ke adawa da gwamnati mai ci zai fi son Amurka ta sha kashi fiye da White House ta yi nasara
- Kuri'ar Pew Research ta nuna amincewar jama'ar Amurka da Trump ta sauka zuwa kashi 34 cikin 100
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
United States - Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya zargi yan jam'iyyar Democrats da son Amurka ta sha kashi a yakin da take yi da Iran.
Trump ya ce bangaren siyasar hagu zai fi son ganin White House ta gaza a "yakin Amurka" fiye da ganin kasar ta samu nasara.

Source: Getty Images
Amurkawa sun fara juyawa Trump baya
Tashar Al-Jazeera ta rahoto cewa wannan na zuwa ne yayin da jam'iyyar Republican ta Trump ke shirin fuskantar zaben tsakiyar wa'adi na watan Nuwamba, a daidai lokacin da yakin Amurka da Isra'ila da Iran ke ci gaba.
Yakin ya zo da tsadar abinci da man fetur, lamarin da ya zama babban kalubale ga gwamnatin Trump kafin zaben.
Wata kuri'ar jin ra'ayin jama'a da cibiyar Pew Research ta gudanar a watan da ya gabata ta nuna cewa amincewar jama'a da Trump ta sauka zuwa kashi 34 cikin 100.
Yawancin Amurkawa da aka gudanar wa binciken sun kuma nuna rashin amincewarsu da yakin da ake yi da Iran.
Kasashen Turai sun taso Iran
A wani bangare kuma, Amurka, Birtaniya, Faransa da Jamus na neman goyon bayan kasashe a hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya, IAEA, domin a zartar da wani kuduri kan Iran.
Kudurin zai iya kai ga kai karar Iran gaban Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya bisa zargin karya wasu alkawurranta da suka shafi makamashin nukiliya.
A watan Yunin shekarar da ta gabata, hukumar IAEA ta zartar da wani kuduri da ya bayyana cewa Iran ta saba alkawurranta saboda rashin cikakken hadin kai wajen binciken wasu alamun uranium da aka gano a wuraren da ba a bayyana ba.
Iaran ta nanata matsayarta
A matsayinta na kasa da ta rattaba hannu kan yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya, NPT, ba a amince Iran ta kera makaman nukiliya ba.
Sai dai gwamnatin Tehran ta sha nanata cewa ba ta kokarin kera makamin nukiliya.
Rahoton Reuters ya ce tun bayan fara yakin a watan Fabrairu, Iran ba ta bai wa jami'an IAEA damar duba wasu cibiyoyin uranium da Amurka da Isra'ila suka kai wa hari ba.

Source: Getty Images
Wannan mataki ya kara dagula dangantakar Iran da kasashen Yamma yayin da ake ci gaba da nuna damuwa kan shirin nukiliyar kasar.
An karyata labarin mutuwar Trump
Kun ji cewa fadar White House ta tabbatar da cewa shugaban Amurka Donald Trump yana raye bayan yaduwar jita-jita a kafafen sada zumunta.
Jita-jitar ta samo asali ne bayan sanarwar cewa mataimakin shugaban kasar Amurka, JD Vance zai yi wa manema labarai bayani maimakon Trump da aka saba gani.
Asali: Legit.ng

