NDC Ta Nesanta Kanta daga ‘Yan Takaran da INEC Ta Wallafa da Sunan Jam’iyyar
- NDC ta nace cewa ba ita ta mika sunayen 'yan takara 10 na majalisar dokokin jihar Anambra da ke shafin INEC ba
- Jam'iyyar ta bukaci INEC ta gudanar da bincike na na'ura mai kwakwalwa domin gano yadda aka shigar da sunayen
- Agada Abuh Theophilus ya fitar da jawabi yake cewa ba su mika wa hukumar zabe fam din wadanda aka tsaida masu ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abuja - Jam’iyyar NDC tana nan a kan bakarta cewa ba ta san da ‘yan takaran da INEC ta yi ikirarin za su yi mata takara a Anambra ba.
An samu matsala a jam’iyyar NDC musamman a jihohin Anambra da Kano da ‘yan takararta na zaben shugaban kasa suka fito.

Source: Facebook
Jawabin darektan sadarwar jam'iyar NDC
Agada Abuh Theophilus ya fitar da jawabi a shafin X (Twitter) a yammacin Laraba, 2 ga watan Satumba 2026 yana yi wa INEC martani.
Jam’iyyar adawar ta ce ba ta san daga ina aka zakulo mata ‘yan takara 10 da za su yi takarar majalisar dokoki na jihar Anambra ba.
Mista Agada Abuh Theophilus ya ce sam ba su ne suka gabatar da sunayen wadannan ‘yan takara wajen hukumar zabe ta kasa ba.
Darektan harkokin sadarwan ya ce NDC ba ta mika wa INEC fam na EC9E na wadannan ‘yan takara da aka fitar da sunayensu ba.
Yake cewa jam’iyyar hamayyar ba ta taba aika wa da sunayen ‘yan takaran ba, kuma ba a zabe su ba bayan korafin takarar tsaida gwani.
Jam'iyyar NDC ta nemi karin bayanin INEC
A madadin jam’iyyar, Agada Abuh ya bukaci hukumar INEC ta yi wa duniya bayani yadda ta samu sunayen wadanann ‘yan takara 10.
The Nation ta rahoto shi yana cewa tsarin fito da ‘dan takara a bayyana yake, jam’iyya ce za ta gabatar da sunayen wadanda ta tsaida.

Kara karanta wannan
Atiku ko Obi: Yan adawa sun fara ɗaukar matsayan da za ta iya kayar da Tinubu a zaben 2027
Agada ya ce daga nan kuma sai INEC ta duba ta yi aiki a kai, a karshe ta amince da su, daga nan sai hukumar ta wallafa sunayen su.
NDC ta hakikance cewa ita ta kai sunayen wasu mutane da aka zaba ne bayan an gama sauraron korafin da ya biyo bayan neman tikiti.
A cewar jam’iyyar, hukumar zabe ta kasa ta yi fatali da sunayen nan da aka aika mata, amma sai ita ta yi mata gaban kanta a Anambra.
NDC tana so hukumar INEC ta yi bincike
Jawabin ya bukaci a gudanar da bincike na musamman da nufin gano yadda aka canza wa NDC wadanda za su rike mata tuta a 2027.
NDC tana zargin ta shafin INEC aka sauya mata sunayen wadanda ta ke so su yi mata takara a zabe mai zuwa da za a yi a shekarar badi.
Shugaban NDC ya bi bayan Atiku Abubakar
An karanta rahoto cewa alkawarin Atiku Abubakar ya sa shugaban NDC na shiyyar Arewa ta yamma ya bi bayan sa, yana sukar Peter Obi.
Muhammad Bakinzuwo daga Kano ya bar Peter Obi ya koma bayan Atiku Abubakar saboda alkawarin da dawo da man tallafin fetur.
Saboda 'dan takaran NDC ya nuna bai adawa da cire tallafin fetur, Alhaji Bakinzuwo ya yi watsi da shi duk da jam'iyyarsa ta tsaida shi.
Asali: Legit.ng

