Tsakanin Atiku da Obi Waye Zai Iya Ƙalubalantar Tinubu? an Fadi Wanda Ya Zo da Gaske
- Wani jigo a jam'iyyar LP, Abayomi Arabambi ya yi magana kan wanda zai ba shugaban kasa, Bola Tinubu ciwon kai a zaben 2027
- Ya ce Atiku Abubakar ne ɗan takara mafi muhimmanci da zai iya kalubalantar Shugaba Bola Tinubu a zaɓen shugaban ƙasa na 2027
- Ya kuma bayyana Peter Obi a matsayin ɗan dirama yana zargin cewa wasu ƙididdigar da yake amfani da su wajen tattauna al’amuran ƙasa ba daidai ba ne
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Mataimakin Shugaban Jam’iyyar Labour na Kudu maso Yamma, Abayomi Arabambi, ya yi hasashen zaben 2027.
Arabambi ya bayyana tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar a matsayin ɗan takara mafi muhimmanci da zai iya kalubalantar Shugaba Bola Tinubu a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Source: Twitter
Arabambi ya bayyana hakan ne ranar Alhamis yayin wata hira da aka yi da shi a shirin Politics Tonight na TVC, inda yake nazarin yadda harkokin siyasa ke sauyawa gabanin zaɓen.
An bayyana Atiku a matsayin dan takarar gaske
A cewarsa, Atiku shi ne ɗan takarar da yake ganin ya shirya tsaf domin fuskantar shugaban ƙasa mai ci a zaɓen.
Ya ce:
“Muna da shugaban ƙasa mai ci, sannan muna da ɗan takara guda ɗaya da zai iya kalubalantarsa. Wanda na sani kuma yake da gaske wajen fafatawa da shugaban ƙasa shi ne Alhaji Atiku Abubakar.”
Sai dai ya yi watsi da yiwuwar Peter Obi, ɗan takarar shugaban ƙasa na NDC ya tsaya takarar 2027, yana bayyana shi a matsayin ɗan siyasar da ya fi mayar da hankali kan sharhi kan al’amura fiye da neman shugabancin ƙasa.
Arabambi ya kuma soki yadda Obi ke amfani da ƙididdiga yayin tattauna matsalolin ƙasa, yana zargin cewa an gano wasu daga cikin alkaluman da yake ambata ba daidai ba ne.
Jigon Jam’iyyar Labour ɗin ya ce:
“Mutum ne da yake zuwa da nau’o’in ƙididdiga iri-iri, daga baya kuma sai a gano cewa ba gaskiya ba ne.”

Source: Twitter
'Peter Obi bai shirya yin takara ba'
Ya ƙara da cewa Obi ba ya shirin tsayawa takarar shugaban ƙasa a 2027, yana mai cewa shugabannin ƙungiyar adawa sun san matsayinsa kan wannan batu.
Ya ce:
“Ba ya takara. Hatta shugabansu ya san cewa Obi ba ya takara. Za ku sake nuna abin da na faɗa yau. Ba ya takara. Ya san dalilin da ya sa ya fita can.”
Jigon Jam’iyyar Labour ɗin ya kuma yi magana kan muhawarar rabon kujerar shugaban ƙasa tsakanin yankunan ƙasar gabanin zaɓen 2027, cewar Punch.
Ya ce a halin yanzu an ware shugabancin ƙasa ga Kudu, don haka ya kamata yankin ya samu damar kammala wa’adinsa na shekaru takwas kafin a mayar da mulki wani yanki.
Arabambi ya tuna cewa Atiku Abubakar ya tsaya takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023 bayan tsohon Shugaba Muhammadu Buhari ya kammala shekaru takwas yana mulki, amma bai samu nasarar lashe zaɓen ba.
Atiku ya bukaci Tinubu ya janye daga takara
An ji cewa dan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya shawarci Bola Tinubu da ya janye daga takarar shugaban ƙasa ta shekarar 2027.
Atiku ya kuma buƙaci Shugaba Tinubu da ya ba shi da kuma 'yan Najeriya hakuri saboda raina shawarar da ya bayar ta tallafawa fannin tace man fetur na cikin gida.
Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya bayyana hakan ne biyo bayan kiran da IPMAN ta yi wa gwamnatin tarayya na tallafa wa kamfanonin tace mai na gida.
Asali: Legit.ng


