Amaechi Ya Fadi Tallafin da Atiku Zai Sake Dawo da Shi bayan na Man Fetur
- Rotimi Amaechi ya bayyana tallafin da Atiku Abubakar zai dawo da shi idan ya zama shugaban kasar Najeriya
- Amaechi ya yi ikirarin cewa kuɗin wutar gidansa ya tashi daga N500,000 zuwa N4m bayan cire tallafin wutar lantarki da gwamnatin Bola Tinubu ta yi
- Tsohon gwamnan Rivers ya kuma danganta cire tallafin man fetur da tashin farashin sufuri da abinci, tare da cewa matsalar tsaro na hana manoma zuwa gonakinsu.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Port Harcourt, Rivers - Mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), Rotimi Amaechi, ya ce Atiku Abubakar zai dawo da tallafin wutar lantarki idan ya lashe zaɓen 2027.
Amaechi ya bayyana hakan ne ranar Alhamis, 3 ga watan Satumban 2026 yayin ziyarar wasu unguwanni a ƙaramar hukumar Omuma ta Jihar Rivers, inda ya isar da saƙon yaƙin neman zaɓen Atiku ga mazauna yankin.

Kara karanta wannan
Atiku ya yi alkawarin ba dan Najeriya da zai biya kudin haya idan ya zama shugaban kasa?

Source: Twitter
Ya yi zargin cewa cire tallafin wutar lantarki da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta yi ya haifar da gagarumin ƙarin kuɗin da ’yan Najeriya ke biya, cewar rahoton jaridar TheCable.
Kuɗin wutar Amaechi ya tashi zuwa N4m
Amaechi ya ce Atiku ya umarce shi da ya sanar da jama’a cewa zai dawo da tallafin wutar lantarki idan ya zama shugaban ƙasa.
"Atiku ya ce na gaya muku cewa zai dawo da tallafin. Tinubu ya cire tallafin kuɗin wutar lantarki. Ya ce Band A, B da C.” In ji shi.
Tsohon gwamnan na Rivers ya yi ikirarin cewa kuɗin wutar gidansa ya tashi daga N500,000 zuwa N4m bayan sauye-sauyen tsarin kuɗin wutar lantarki.
Ya ce idan Atiku ya zama shugaban ƙasa, zai koma biyan N500,000, yana mai cewa gwamnati za ta ɗauki wani ɓangare na kuɗin.
Ya soki cire tallafin man fetur
Amaechi ya kuma zargi cire tallafin man fetur da haddasa tashin farashin sufuri da kayan abinci a Najeriya.
Ya ce ’yan Najeriya ne suka ɗauki babban nauyin tasirin manufofin, musamman saboda tashin farashin kayayyakin masarufi.
“Tun da ya cire tallafin, sufuri ya ƙaru, farashin abinci ya ƙaru, tumatir, masara, komai.” In ji shi.
A cewarsa, matsalar rashin tsaro ma ta ƙara tsananta, lamarin da ya sanya manoma ke fuskantar matsala wajen zuwa gonakinsu.
Amaechi ya ce tallafi zai rage tsadar rayuwa
Amaechi ya ce dawo da tallafin wutar lantarki da na man fetur a ƙarƙashin gwamnatin Atiku zai taimaka wajen rage tsadar rayuwa.
“Atiku ya ce zai dawo da tallafin. Idan Atiku ya dawo da tallafin, komai zai sauko.” In ji shi.
Yadda tsarin farashin wutar lantarki yake
A Najeriya, an raba masu amfani da wutar lantarki zuwa Band A, B, C, D da E, bisa adadin sa’o’i na wutar lantarki da suke samu.
Masu amfani da Band A ana sa ran za su samu aƙalla sa’o’i 20 na wuta a kullum, yayin da Band B, C, D da E ke da ƙananan matakan samar da wutar lantarki.
An ƙirƙiri tsarin ne domin masu samun wutar lantarki mai ɗorewa su biya kuɗi mafi yawa, yayin da waɗanda ke samun ƙarancin sa’o’i na wuta su biya kuɗi kaɗan.

Source: Facebook
Wike ya ce Atiku ba zai ci zabe ba
A wani labarin kuma, kun ji cewa Nyesom Wike ya bayyana dalilin da ya sa yake ganin Atiku Abubakar ba zai iya lashe zaɓen shugaban ƙasa da za a gudanar a ranar 16 ga Janairu 2027 ba.
Wike ya ce burin Atiku na neman shugabancin ƙasar ƙarƙashin jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ya saɓa wa tsarin karba-karba na mulki tsakanin Arewa da Kudu.
Asali: Legit.ng

