‘Ka da Ku Biye wa Yan Siyasa’: Gargadin Matar Tinubu da Minista ga Matasa
- Uwargidan shugaba Bola Tinubu da Ministan Tsaro, Christopher Musa sun gargadi matasan Najeriya game da yan siyasa
- Oluremi Tinubu ta bukaci matasa su guji zama karnukan ’yan siyasa da ke watsar da su bayan sun cimma burinsu
- Musa ya ce rashin aikin yi, talauci, kwayoyi da bayanan karya na sanya matasa cikin saukin amfani da su wajen aikata laifuka da tashin hankali
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Uwargidan Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, da Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa mai ritaya, sun shawarci matasa.
Mutanen biyu sun gargadi matasan Najeriya gabanin babban zaɓen 2027 inda suka bukaci su guji bari yan siyasa na amfani da su.

Source: Twitter
Oluremi da Musa sun yi wannan gargadin ne daban-daban a wajen taron Matasa Kiristoci na Ƙasa kan Tsaro da Godiya da aka gudanar a Abuja, cewar The Nation.

Kara karanta wannan
Dan Majalisa ya kai ƙorafi gaban shugaban Amurka kan abin da ake wa Tinubu a Najeriya
Sun bukaci matasa kada su bari ’yan siyasa su yi amfani da su tare da lalata makomarsu saboda bukatun siyasa na kashin kai.
Sanata Tinubu ta gargadi matasan Najeriya kada su zama “abin sadaukarwa” ga ’yan siyasar da ke son amfani da su wajen cimma manufofinsu.
Ministan tsaro ya ja hankalin matasa
Shi kuwa Musa ya yi gargadin cewa masu aikata laifuka da ’yan siyasa za su iya amfani da kwayoyi, kuɗi da sauran abubuwan jan hankali wajen jawo matasa cikin tashin hankali.
Ministan Tsaro ya ce yadda matasan Najeriya ke kasancewa cikin saukin amfani da su ya zama babban abin damuwa ga tsaron ƙasa.
Musa, wanda mai ba shi shawara kan tsaro da leƙen asiri, Musa Likita, ya wakilta, ya ce ƙarfafa matasa ya kamata ya zama wani muhimmin bangare na dabarun tsaron ƙasa.
A cewarsa, matashin da ya samu ilimi, kwarewa da damar dogaro da kansa ta fuskar tattalin arziki ba shi da saukin fadawa tarkon ’yan siyasa, masu laifi da ƙungiyoyin masu tsattsauran ra’ayi.

Kara karanta wannan
'Matsala ne dawo da tallafin mai': Malamin Musulunci ya gargaɗi ƴan siyasa kan kamfe

Source: Facebook
Gargadin uwargidan shugaban kasa
Da yake wakiltar Uwargidan Shugaban Ƙasa, Babban Sakatare na Hukumar Aikin Hajji ta Kiristoci ta Najeriya, Stephen Adegbite, ya ce ƙasar na gab da wani muhimmin lokacin zaɓe.
Ya ce ya kamata matasan Najeriya su koyi darasi daga kura-kuran da aka aikata a baya, tare da kin mika rayukansu da makomarsu ga ’yan siyasar da za su yi watsi da su bayan sun yi amfani da su.
Ta ce dole matasa su ƙi amincewa da ’yan siyasar da za su yi amfani da su don biyan bukatunsu na kashin kai.
“Wannan ya kamata ya zama lokacin da babu ɗayanku da za a yi amfani da shi a matsayin abin sadaukarwa, ba ma son wani ɗan siyasa ya yi amfani da ku ya kuma ɓata rayuwarku.”
Uwargidan Shugaban Ƙasa ta bukaci matasa su rungumi shiga harkokin dimokuraɗiyya cikin lumana da kuma ayyukan gina ƙasa maimakon tashin hankali.
Ta kuma bukaci matasa su yi addu’a ga ƙasar da shugabanninta, ciki har da Shugaba Bola Tinubu, gwamnoni, sanatoci da sauran zaɓaɓɓun jami’an gwamnati.
Ta ce bai kamata a bari ’yan siyasa da sauran masu ruwa da tsaki su yi amfani da addini ko ƙabila wajen haifar da ƙiyayya da tashin hankali ba.
Ta ce:
“A matsayinsu na Musulmi da Kiristoci a Najeriya, dole ne mu yi aiki tare. Mu ’yan’uwa ne, kuma dole mu ɗauki kanmu a matsayin tsintsiya ɗaya. Sai mun samu zaman lafiya kafin mu iya magana kan ci gaba."
Uwargidan Shugaban Ƙasa ta tambayi yadda Najeriya za ta samu ci gaba cikin yanayin kisa, rikici, gaba da rashin jituwa tsakanin mabiya addinai.
Ta ce Kiristanci da Musulunci addinai ne na zaman lafiya, don haka bai kamata a yi amfani da su wajen tabbatar da tashin hankali ba, cewar Punch.
Kokarin Tinubu kan matsalar tsaro
An ji cewa Ministan Tsaro, Christopher Musa, ya gargadi gwamnonin jihohi su kan rabon babura a matsayin tallafi da suke yi.
Musa ya ce manyan babura masu ƙarfi na bai wa ’yan ta’adda damar shiga yankunan da ke da wahalar isa.
Ministan ya bayyana cewa hare-haren Boko Haram da ISWAP sun ragu, yayin da ayyukan ƙungiyoyin suka koma satar mutane.
Asali: Legit.ng
