Ministan Tsaro Ya Gargadi Gwamnoni kan Raba Babura, Ya Fadi Illar Haka ga Tsaro

Ministan Tsaro Ya Gargadi Gwamnoni kan Raba Babura, Ya Fadi Illar Haka ga Tsaro

  • Ministan Tsaro, Christopher Musa, ya gargadi gwamnonin jihohi su kan rabon babura a matsayin tallafi da suke yi
  • Musa ya ce manyan babura masu ƙarfi na bai wa ’yan ta’adda damar shiga yankunan da ke da wahalar isa
  • Ministan ya bayyana cewa hare-haren Boko Haram da ISWAP sun ragu, yayin da ayyukan ƙungiyoyin suka koma satar mutane

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa (mai ritaya), ya gargadi gwamnonin jihohi kan rabon babura a matsayin tallafi ga al’umma.

Ya ce ana iya karkatar da irin waɗannan babura zuwa hannun ’yan ta’adda, inda za su yi amfani da su wajen sauƙaƙa ayyukansu.

Ministan tsaro ya gargadi gwamnoni kan rabon babura
Ministan tsaro a Najeriya, Christopher Musa. Hoto: HQ Nigerian Army.
Source: Facebook

Musa ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da aka yi da shi a shirin Politics Today na gidan talabijin na Channels.

Kara karanta wannan

Kwamishina ya yi amai ya lashe kan barazana ga masu adawa da APC

Matsalolin raba babura ga al'umma

Ya ce baburan da gwamnati ke rabawa a shirye-shiryen tallafawa jama’a na iya bai wa ’yan ta’adda damar zirga-zirga cikin sauƙi.

Ministan ya bukaci gwamnonin su sake duba wannan tsari, musamman rabon manyan babura masu ƙarfi da za su taimaka wa ’yan ta’adda wajen saurin kaiwa wurare daban-daban.

Ya ce gwamnatocin da suka dage kan rabon babura ya kamata su duba yiwuwar samar da ƙananan babura waɗanda ba za su kasance da amfani sosai ga masu aikata laifuka da ’yan ta’adda ba.

Ya ce:

"Muna rokon duk wani gwamna da ya bar raba babura a matsayin tallafi saboda a karshe yan bindiga ne ke amfani da su wurin ayyukan ta'addanci.
“Ko da za ku bayar, kada ku bayar da manyan babura masu ƙarfi; ku bayar da ƙananan babura waɗanda ba za su iya amfani da su wajen yawan zirga-zirga ba, domin hakan yana ba su damar yin ƙarfi."

Kara karanta wannan

Peter Obi ya ba 'yan Najeriya shawara da ya sanya kansa cikin wadanda suka jefa kasar a matsala

Kokarin da gwamnatin Tinubu ke yi kan tsaro
Shugaba Bola Tinubu na Najeriya. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Facebook

Tsaro: Kokarin da gwamnatin Tinubu ke yi

A cewar Musa, ’yan ta’adda na iya amfani da sauri da sauƙin zirga-zirgar babura wajen shiga yankunan karkara, kai hare-hare da tserewa kafin jami’an tsaro su samu damar mayar da martani.

Gargadin ministan ya zo ne yayin da yake magana kan halin tsaro a ƙasar, inda ya ce Najeriya ta samu ci gaba a ƙarƙashin Shugaba Bola Tinubu.

Musa ya ce hare-haren da ƙungiyoyin Boko Haram da Islamic State West Africa Province (ISWAP) ke kaiwa sun ragu idan aka kwatanta da shekarun baya.

Ya bayyana cewa matsin lambar da sojoji ke ci gaba da yi wa ƙungiyoyin ’yan ta’adda ya tilasta musu sauya salon ayyukansu daga manyan hare-haren ta’addanci zuwa satar mutane domin neman kuɗi.

Ministan tsaro ya yaba kokarin Tinubu

Mun ba ku labarin cewa Ministan Tsaro Christopher Musa ya bayyana kokarin da gwamnatin Bola Tinubu ke yi a bangaren tsaro.

Kara karanta wannan

"Gwamnatinmu ce"; Kwamishina ya yi barazanar guntile 'yan yatsun masu adawa da APC

Musa ya ce gwamnati na ƙarfafa rundunar soji, zamanantar da kayan tsaro da amfani da fasahohin zamani domin tunkarar barazanar tsaro.

Ministan ya bayyana cewa barazanar tsaro na shafar ƙasa, teku, sararin sama da yanar gizo, yana mai buƙatar haɗin gwiwar hukumomin tsaro.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.