Babbar Magana: Atiku Ya Bukaci Tinubu Ya Janye daga Takarar 2027
- Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya shawarci Bola Tinubu da ya janye daga takarar shugaban ƙasa ta shekarar 2027
- Atiku ya kuma buƙaci Shugaba Tinubu da ya ba shi da kuma 'yan Najeriya hakuri saboda raina shawarar da ya bayar ta tallafawa fannin tace man fetur na cikin gida
- Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya bayyana hakan ne biyo bayan kiran da IPMAN ta yi wa gwamnatin tarayya na tallafa wa kamfanonin tace mai na gida
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya shawarci Shugaba Bola Tinubu da ya fice daga takarar zaɓen shugaban ƙasa na 2027 ko kuma ya shirya fuskantar kaye a rumfunan zaɓe.
Atiku ya kuma buƙaci Shugaba Tinubu da ya nemi gafara a wurinsa da kuma 'yan Najeriya baki ɗaya kan gargaɗi da subucewar bakin da aka yi lokacin da ya ba da shawarar gudanar da tsarin tallafin fetur ta hanyar haɓaka sarrafa shi a gida.

Source: Facebook
Vanguard ta rahoto cewa Atiku ya bayyana hakan ne ta hanyar wata sanarwa da hadiminsa, Phrank Shaibu, ya fitar a ranar Alhamis.
Kiran Atiku Abubakar ga Bola Tinubu
Atiku ya bayyana cewa cire tallafin fetur da Tinubu ke takama da shi ne ya jawo halin ƙunci da 'yan Najeriya ke ciki, inda ya jaddada cewa tsarin tallafawa sarrafa mai a gida shi ne matakin da zai dogara kan sauƙata rayuwa.
Ya bayyana cewa:
"Akwai zaɓi biyu masu kyau a gabansa yanzu: Ya ba Atiku Abubakar da kuma 'yan Najeriya haƙuri saboda kin karbar tsarin da manyan 'yan kasuwar fetur suka fara karɓa baki, sannan ya janye daga takarar shugaban ƙasa ta 2027; ko kuma ya jira a ƙwarfe shi a zaɓen 2027.
"Wannan ba batun Tinubu ko Atiku ba ne, batun 'yan Najeriya ne."
Bambancin tsarin tallafin mai
The Sun ta wallafa cewa Atiku ya jaddada cewa shawararsa ta tallafin mai ta bambanta da tsohon tsarin da ake shigo da mai daga waje.

Kara karanta wannan
Atiku ya ɗauki alkawarin da zai faranta wa ɗaliban Najeriya rai kan kuɗin NELFUND
Ya ce Najeriya tana da ɗanye mai saboda haka rashin hikima ne a gaza sarrafa shi a gida sannan a tilasta wa 'yan ƙasa sayan man fetur a kan farashi mai tsada.
Ya ƙara da cewa:
"Farashin fetur na iya zama mai sauƙi idan aka kwatanta shi da dalar Amurka zuwa ƙasashen waje, amma 'yan Najeriya ba albashin Amurka ko na Turai suke samu ba."

Source: Facebook
Gargaɗin INEC kan 2027
A wani labarin, mun ruwaito cewa INEC ta yi gargaɗi cewa amfani da dabarun fasahar zamani (AI) wajen yaɗa labaran ƙarya na zaman babbar barazana ga ingancin zaɓen 2027.
Shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan, ya bayyana cewa hukumar tana gudanar da gyare-gyare da bincike kan na'urorin fasaharta, tare da tsara gudanar da zaɓen gwaji.
Sanarwar da aka fitar ta ruwaito Amupitan na fadar hakan ne ta bakin kwamishinan INEC, Sani Adam, yayin wani taro da aka gudanar a birnin tarayya Abuja.
Asali: Legit.ng
