Okonkwo Ya Haska Dalilin da Ya Sa ba a Son Atiku Ya Zama Shugaban Kasa

Okonkwo Ya Haska Dalilin da Ya Sa ba a Son Atiku Ya Zama Shugaban Kasa

  • Kenneth Okonkwo ya ce ana farfado da tsoffin zarge-zargen da ake yi wa Atiku ne domin hana shi tsayawa takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027.
  • Lauyan ya ce binciken da aka gudanar a baya bai tabbatar da cewa Atiku ya nemi ko ya karɓi cin hanci daga tsohon ɗan majalisar Amurka William Jefferson ba
  • Okonkwo ya ce Atiku ya ƙalubalanci Shugaba Bola Tinubu su yi muhawara domin ’yan Najeriya su ji shirye-shiryen ’yan takarar kai tsaye

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Mai magana da yawun ɗan takarar shugaban ƙasa na African Democratic Congress (ADC), Kenneth Okonkwo, ya yi maganganu kan Atiku Abubakar.

Kenneth Okonkwo ya yi zargin cewa ana farfado da tsofaffin zarge-zargen Atiku Abubakar ne domin hana shi takara a zaɓen 2027.

Okonkwo ya ce ana shiryawa Atiku makarkashiya
Atiku Abubakar na jawabi a wajen taro Hoto: Atiku Abubakar
Source: Facebook

Okonkwo, wanda lauya ne, ya bayyana hakan ne ranar Alhamis, 3 ga watan Satumban 2026 yayin wata hira da aka yi da shi a shirin Sunrise Daily na tashar Channels Tv.

Kara karanta wannan

Amaechi ya fadi tallafin da Atiku zai sake dawo da shi bayan na man fetur

Ya mayar da martani ne kan sabunta bincike game da harkokin Atiku a Amurka, musamman zarge-zargen da suka shafi tsohon ɗan majalisar wakilan Amurka, William Jefferson.

Batun ya samo asali ne daga binciken da hukumomin Amurka suka gudanar a shekarun 2005 da 2006, wanda ya shafi alakar Jefferson da wasu jami’an Najeriya.

Okonkwo ya kare Atiku

Okonkwo ya yi watsi da zarge-zargen, yana mai cewa siyasa ce ta haddasa sake dawo da batun cikin harkokin yau.

Ya dage cewa binciken da aka gudanar a baya bai tabbatar da cewa Atiku ya nemi ko ya karɓi cin hanci daga Jefferson ba.

“An wanke Atiku Abubakar gaba ɗaya daga zarge-zargen.” In ji shi.

Kenneth Okonkwo ya kuma tambayi dalilin da ya sa aka sake dawo da batun a wannan lokaci, yana mai cewa irin waɗannan zarge-zargen kan sake fitowa fili a duk lokacin da zaɓe ya matso.

EFCC da batun zaɓen 2027

Kara karanta wannan

Bayanai sun fito kan yadda FBI ta taba bincikar Atiku, lalube gidansa a 2005

Okonkwo ya kuma soki Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Najeriya (EFCC) kan ci gaba da nuna sha’awa ga batun.

A cewarsa, irin wannan mataki na iya yin tasiri ga tsarin zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

"A kowace shekarar zaɓe za mu sake dawowa kan wannan batu. Amma shin hakan zai iya rage nasarar da ake ganin zai samu a rumfunan zaɓe? A’a, ba zai yi hakan ba.”

Okonkwo ya ƙara zargin cewa wasu muradun siyasa ne ke bayan yunƙurin hana Atiku shiga takarar shugaban ƙasa.

"Dalilin da ya sa suke son hana Atiku Abubakar shi ne kawai saboda yana son zuwa ya kyautata rayuwa tare da sauƙaƙa wa ’yan Najeriya.” In ji shi.

Atiku ya ƙalubalanci Tinubu

Da yake magana kan takarar Atiku da Shugaba Bola Ahmed Tinubu, Okonkwo ya ce ɗan takarar ADC a shirye yake ya yi muhawara da shugaban ƙasar gabanin zaɓen 2027.

Ya ce Atiku ya riga ya ƙalubalanci Tinubu zuwa muhawara, yana mai cewa shi ne ya sanya hannu a kan sanarwar da ta fito a hukumance.

Kara karanta wannan

Tirkashi: An hango abin da zai hana Atiku zama shugaban kasa a 2027

"Atiku ya ƙalubalanci Tinubu zuwa yin muhawara. A hukumance ma, ni ne na sanya hannu kan wannan sanarwa.”

Ya bayyana cewa ya kamata ’yan Najeriya su samu damar jin shirye-shiryen da manufofin manyan ’yan takarar shugaban ƙasa kai tsaye kafin su yanke hukuncin wanda za su zaɓa.

Kenneth Okonkwo ya yi magana kan Atiku
Mai magana da yawun bakin Atiku Abubakar, Kenneth Okonkwo Hoto: @realkenokonkwo
Source: Twitter

Atiku zai dawo da tallafin lantarki

A wani labarin kuma, kun ji cewa dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam'iyyar ADC, Rotimi Amaechi, ya yi wa 'yan Najeriya albishir.

Rotimi Amaechi ya bayyana cewa Atiku Abubakar zai dawo da tallafin wutar lantarki idan ya zama shugaban kasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng