Miyetti Allah Ta Kaɗa Hantar Tinubu, Ta Fada Masa Sharaɗin Sake Zaɓensa a 2027
- Kungiyar iyetti Allahta bayyana sharaɗin sake zaben shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a zaben 2027 da ke tafe a Najeriya
- Shugaban ƙungiyar a Nasarawa, Akhajo Abubakar, ya ce ba su zaɓi APC ba domin kama shugabanninsu, don haka za su zaɓi masu son ci gabansu
- Abubakar ya yi ikirarin cewa Fulani na da sama da masu zaɓe miliyan ɗaya a Nasarawa, amma bai gabatar da wata hujja ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Ƙungiyar al’ummar Fulani mai suna Miyetti Allah ta gargadi Bola Tinubu game da zaben shekarar 2027.
Kungiyar ta ce za ta goyi bayan jam’iyyar APC ne kawai a babban zaɓen 2027 idan aka saki shugabanta na ƙasa, Bello Bodejo, wanda Hukumar DSS ke tsare da shi.

Source: Facebook
Barazanar da Miyetti Allah ta yi wa Tinubu
Ƙungiyar ta bayyana matsayinta ne yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a gidan Bodejo da ke Uke, a ƙaramar hukumar Karu ta Nasarawa, cewar Premium Times.
Shugaban Miyetti Allah a Nasarawa, Akhajo Abubakar, ya ce ƙungiyar za ta tattara ƙuri’un mambobinta ne domin shugabannin siyasar da suka nuna damuwa da muradun al’ummar Fulani da ci gabansu.
Ya ce:
“Ba mu zaɓi APC ba domin ta kama shugabanninmu. A wannan karon, ƙuri’unmu za su tafi ne ga waɗanda suke son ci gabanmu.”
Abubakar ya yi ikirarin cewa al’ummar Fulani na da sama da masu zaɓe miliyan ɗaya a Nasarawa kaɗai, sai dai bai gabatar da wata hujja ko bayanan da za su tabbatar da wannan ikirari ba.

Source: Facebook
Wanda Miyetti Allah za ta zaba a 2027
Matsayar ƙungiyar Miyetti Allah ta zo ne yayin da ake fara samun ƙarin maganganun siyasa da shirye-shiryen jam’iyyu da ƙungiyoyin al’umma gabanin babban zaɓen ƙasar da za a gudanar a shekarar 2027.
A baya-bayan nan, kotu ta rage kuɗin bel ɗin Bodejo daga Naira biliyan biyu yayin da yake fuskantar shari’ar da ta shafi zargin halatta kuɗaɗen haram.
Ƙungiyar ta jaddada cewa goyon bayanta a zaɓen 2027 zai dogara ne kan yadda ’yan siyasa za su nuna kishin ci gaban al’ummar Fulani da kare muradunsu.
Ta kuma bayyana cewa ta shirya tsaf domin duba wanda ya fi dacewa a jagoranci na gari saboda kawo ci gaba da kuma mutunta tsarin kungiyar, cewar Daily Post.
Shugaban Miyetti Allah a Abuja ya rasu
A wani labarin, an ji cewa shugaban kungiyar Miyetti Allah, MACBAN na Abuja, Alhaji Ardo Wokili Madugu, ya rasu bayan tirela ta faɗa kan motar da yake ciki a hanyar Lambata-Izom.
Hatsarin ya faru da misalin ƙarfe 4:38 na yammacin Lahadi, lokacin da tirela ta faɗa cikin rami, ta faɗa kan motar kasuwanci.
An birne marigayin a gidansa da ke Gwako, inda shugabannin MACBAN da sauran manyan jami’ai suka halarci sallar jana’izarsa tare da iyalansa.
Asali: Legit.ng

