Kwankwaso Ya Yi Amfani da Gwamnoni 30, Ya Yi Maganar da Za Ta Tsorata Tinubu kan Zaben 2027

Kwankwaso Ya Yi Amfani da Gwamnoni 30, Ya Yi Maganar da Za Ta Tsorata Tinubu kan Zaben 2027

  • Dan takarar mataimakin shugaban kasa na NDC, Rabiu Kwankwaso ya ce yawan gwamnoni da jam'iyya ke da su ba tabbacin lashe zaben 2027 ba ne
  • Ya ce wasu gwamnoni musamman na Arewa sun gaza wajen gudanar da ayyukan gwamnati da za su taimaki rayuwar talaka
  • Tsohon gwamnan Kano ya ce rashin tsaro da fushin jama'a na kara zama barazana ga gwamnati mai ci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Rivers, Nigeria - Dan mataimakin shugaban kasa na NDC, Rabiu Kwankwaso, ya gargadi jam'iyyun siyasa da kada su dauki yawan gwamnoni da suke da su a matsayin tabbacin lashe zaben 2027.

Kwankwaso, tsohon gwamnan jihar Kano, ya bayyana haka ne ranar Alhamis, 3 ga watan Satumba, 2026 a taron jam'iyyar NDC a jihar Rivers.

Kwankwaso.
Dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam'iyyar NDC, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso Hoto: @KwankwasoRM
Source: Facebook

Tsohon gwamnan ya ce wasu gwamnoni, musamman na Arewacin Najeriya, ba su gudanar da ayyukan da suka dace ga talakawa ba, kamar yadda Vanguard ta rahoto.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC ya tona gaskiya, an ji yadda gwamnoni suka amfana da cire tallafin fetur

Kwankwaso ya gargadi gwamnoni

Kwankwaso ya ce tarihin zabukan da suka gabata ya nuna cewa gwamnati mai ci na iya rasa zabe duk da kasancewarta mai iko da jihohi da dama.

Ya gargadi masu tunanin cewa samun goyon bayan gwamnoni sama da 30 zai tabbatar musu da nasara a zaben 2027.

Ya ce:

“An taba kayar da shugaban kasa mai ci a kasar nan. Ina ba da wannan misali ne musamman ga wadanda suke tunanin saboda suna da gwamnoni sama da 30 ba za su yi rashin nasara ba. Wannan babban kuskure ne.”

Ya yi hasashen makomar gwamnoni

Tsohon gwamnan Kano ya yi hasashen cewa wasu gwamnoni, musamman wadanda ke Arewa, za su fuskanci matsala wajen fitowa su yi yakin neman zabe saboda abin da ya bayyana a matsayin gazawarsu wajen gudanar da gwamnati.

Ya ce:

“Da yardar Allah, musamman wadanda ke Arewa, za su sha wahala domin na yi nazarin yadda al'amura ke tafiya. Abin da na gani shi ne wadannan gwamnoni da jam'iyyunsu sun yi matukar gazawa, har ya kai ga zai yi musu wahala su fito su yi kamfe.”

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun addabi Kano, Abba ya fadi matakan da za a dauka a murkushe su

Ya soki kashe kudaden gwamnati

Kwankwaso ya kuma soki yadda wasu gwamnatocin jihohi da gwamnatin tarayya ke tafiyar da kudaden jama'a.

Ya ce kudaden shiga na gwamnati sun karu sosai idan aka kwatanta da shekarun baya, kamar yadda Daily Post ta rahoto.

Kwankwaso.
Jagoran Kwankwasiyya na Najeriya kuma dan takarar mataimakin shugaban kasa, Rabiu Kwankwaso Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso
Source: Facebook

Da yake tuna lokacin da ya zama gwamnan Kano a shekarar 1999, Kwankwaso ya ce a lokacin jihohi da kananan hukumomi kan samu kusan Naira biliyan 4 kowanne.

Sai dai ya ce karin kudaden da gwamnatoci ke samu a yanzu bai bayyana yadda ya kamata a rayuwar talakawan Najeriya ba.

Dalilin hadakar Kwankwaso da Obi

A wani rahoton, kun ji cewa tsohon gwamnan Kano, Rabiu Kwankwaso ya bayyana kwarin gwiwarsa cewa Najeriya za ta shawo kan ƙalubalen da take fuskanta.

Kwankwaso ya ce haɗin gwiwarsa da Peter Obi ya samo asali ne daga matsayar da suke da ita ta neman inganta rayuwar ’yan Najeriya masu fama da matsaloli.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262