2027: Gwamna Ya Fito Ya Nesanta Tinubu da Matsalolin Tsaron Arewa

2027: Gwamna Ya Fito Ya Nesanta Tinubu da Matsalolin Tsaron Arewa

  • Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri, ya yi kira ga shugabannin shiyyar Arewa da su daina ɗaura wa Bola Tinubu laifi kan matsalar tsaro da ke damun shiyyar
  • Fintiri ya ƙalubalanci shugabannin Arewacin ƙasar da su fuskanci gaskiya tare da neman mafita mai dorewa maimakon tsayawa suna zargin gwamnatin tarayya
  • Rahoto ya nuna cewa gwamnan ya yi waɗannan kalamai ne yayin taron masu ruwa da tsaki na jam'iyyar APC na jihar Adamawa da aka gudanar a garin Yola

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Yola – Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri, ya faɗa wa shugabannin shiyyar Arewa da su daina neman gudu daga nauyin da ke kansu tare da daina ɗaura wa shugaba Bola Tinubu laifin matsalar tsaro da ke addabar yankin.

Kara karanta wannan

Daliban ABU Zaria sun kera na'urar da makafi za su rika tafiya da ita cikin salama

Gwamnan ya ƙalubalanci shugabannin Arewacin ƙasar da su yarda cewa laifinsu ne tare da neman mafita mai dorewa kan matsalolin tsaron, maimakon neman wanda za su ɗaura wa laifi a ko da yaushe.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu Ahmadu Fintiri
Shugaba Bola Tinubu a hagu da Gwamna Ahmadu Fintiri a dama. Hoto: Adamawa State Government|Bayo Onanuga
Source: Facebook

Tribune ta rahoto cewa Fintiri ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis yayin wani taron masu ruwa da tsaki na jam'iyyar APC da aka gudanar a birnin Yola.

Fintiri ya wanke Tinubu

Fintiri ya bayyana cewa irin wannan zargi ne aka riƙa yi wa tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan na cewa shi ke ɗaukar nauyin Boko Haram, alhalin kowa ya sani cewa 'yan Boko Haram 'yan Arewa ne.

Daily Post ta rahoto ya ce:

"A matsayinmu na shugabanni daga Arewa, ya kamata mu daina guje wa matsalolinmu da kuma ɗaura wa waɗansu laifin rashin nasararmu. Tinubu, a ra'ayina, bai cuce mu ba, mutanen Karamar Hukumar Madagali inda na fito."

Gwamnan ya kuma kushe al'ada ta tura yara bara a tituna da sunan bara, inda ya bayyana cewa Musulunci ya hana bara amma wasu na ci gaba da tura yara roƙo kan tituna.

Taswirar jihar Adamawa
Taswirar jihar Adamawa a Najeriya. Hoto: Legit
Source: Original

Shiri da damar APC a zaɓen 2027

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta fadi yadda Arewa ta fi cin ribar gwamnatinsa

Da yake magana kan jam'iyyar APC da zaɓen 2027 a jihar Adamawa, Fintiri ya jaddada cewa APC ba jam'iyyar wata ƙabila ko addini ba ce, kuma jam'iyyar PDP ta riga ta rushe a jihar.

Ya gargaɗi cewa babu wani mutum da zai zo Adamawa ya tafka maguɗin zaɓe a 2027, inda ya ƙara da cewa:

"Na rantse da Allah Maɗaukakin Sarki babu wani mutum da zai zo Adamawa ya yi mana maguɗi."

Gwamna Sule ya kare Tinubu

A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnan Jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya bayyana cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu yana da cikakkiyar masaniyar halin ƙunci da 'yan Najeriya ke ciki.

A yayin taron masu ruwa da tsaki na jam'iyyar APC a Lafia, Gwamna Sule ya ce shugaban ƙasar ya amince cewa duk da cewa kididdigar tattalin arziƙi na inganta, har yanzu alfanun bai gamsar da talakawan ƙasa ba.

Gwamnan ya ƙara da cewa Tinubu ya umarci gwamnoni da su ci gaba da gina hanyoyin karkara, samar da ruwan sha, wutar lantarki, da tsare-tsaren tallafawa jama'a domin rage musu raɗaɗin halin da ake ciki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng