Sirrin Yadda Sojoji ke Ceto Mutane a Daji ba tare da Kashe 'Yan Ta'adda ba
- Ministan tsaro, Christopher Musa, ya bayyana dabarun da rundunonin tsaro ke amfani da su wajen ceto mutanen da aka sace ba tare da sun kashe 'yan ta'addan ba
- Ya bayyana cewa dabarar ta haɗa da kewaye 'yan ta ta'adda, katse musu hanyoyin gudu da kuma hana su samun abinci, ruwa, fetur da sauran kayan masarufi
- Ministan ya yi waɗannan kalamai ne yayin da yake jawabi game da halin da kasa ke ciki da kokarin da ake domin tabbatar da zaman lafiya a Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Abuja – Ministan tsaro, Janar Christopher Musa, ya fadi yadda dakarun tsaro ke samun nasarar ceto mutanen da aka yi garkuwa da su a lokuta da dama ba tare da an zubda jini ko an biya kudin fansa ba.
Bayanai na fitowa ne sakamakon tambayoyi da damuwa da jama'a ke bayyanawa kan ayyukan sojoji na baya-bayan nan, kamar yadda aka gani a jihar Kwara da sauran sassan Arewacin ƙasar, inda ake ceto mutane ba tare da an kashe 'yan ta'addan ba.

Source: Facebook
Ministan tsaron ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis yayin da yake magana a shirin 'Politics Today' na gidan talabijin na Channels TV.
Dabarun da sojoji ke aiki da su
Ministan ya bayyana cewa babban shirin sojoji shi ne gano inda 'yan ta'addan suke, katse musu hanyoyin tserewa, da kuma dakile samar musu da ruwa, abinci, da fetur.
Ya bayyana cewa sau da yawa 'yan ta'addan kan gudu su bar mutanen da suka sace idan sun fuskanci barazana.
Ya bayyana cewa cewa:
"Wani abin ban mamaki shi ne, su ma 'yan ta'addan ba sa son mutuwa. Ina fatan kun sani. Dukkan waɗannan abubuwan da suke yi da ɗaukar makamai, ba sa son mutuwa.
"Saboda haka zarar an samu wani abu, ko da jirgi masar matuki ne ya nufe su, za ka gan su sun tarwatse sun bar kowa. Abin da ke faruwa kenan."

Source: Twitter
Punch ta wallafa cewa ya ƙara da cewa:
"Abin da muke yi yawanci shi ne zarar mun gano inda suke, mukan rufe musu hanyoyi. Kamar yadda na faɗa, idan ka ɗauke musu numfashi, za su mutu. Wannan shi ne ya sa muke ƙalubalantar waɗanda ke tallafa musu ta hanyar samar masu da fetur, ruwa da abinci."
Gargaɗi kan rabon babur
A wani labarin, mun ruwaito cewa Ministan Tsaro Christopher Musa ya yi kira ga gwamnonin jihohi da su sake duba batun rarraba babura a matsayin tallafi ga al'umma.
Musa ya gargaɗi cewa baburan da ake rarrabawa ta hanyar tallafi ko ayyukan mazabu galibi suna gaba ne su fada hannun 'yan ta'adda, wanda ke basu damar gudanar da sace-sace da tserewa cikin sauƙi.
Ya buƙaci cewa idan ma har za a rarraba babura din, to a riƙa bayar da ƙananan babura maimakon manya, domin hana 'yan ta'adda amfani da su wajen gudanar da ayyukansu.
Asali: Legit.ng

