Abinda yasa ake yawan samun mutuwar aure a tsakanin Musulmai - Ustaz Sa'eed

Abinda yasa ake yawan samun mutuwar aure a tsakanin Musulmai - Ustaz Sa'eed

Wani malamin addinin Musulunci, Ustaz Sa'eed AbdurRauf ya bayyana rasin saka tsoron Allah a zuciya da kuma rashin kudi a matsayin tushen lalacewar aure a kasar nan.

AbdurRauf ya sanar da hakan ne a ranar Litinin a Ibadan yayin jawabi a wani taro da aka shirya na wata kungiyar mata Musulmai kuma 'yan kasuwa.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya ruwaito cewa an yi jawabin ne a kan shawo kan kalubalen lalacewa auren zamani.

Malamin wanda ya ce ba sabon abu bane samun rashin jituwa a aure, ya kara da cewa duk wata dangantaka ko ma'amala da aka gina da tsoron Allah ba ya karewa da saki.

"Mu gina alakarmu da tsorn Allah. Idan ma'aurata na tsoron Allah, komai na zuwa da sauki. Su yi ibada a tare, zaman lafiya da kuma soyayyar juna duk don Allah," a cewarsa.

Abinda yasa ake yawan samun mutuwar aure a tsakanin Musulmai - Ustaz Sa'eed
Ustaz Sa'eed AbdurRauf
Asali: Twitter

Malamain ya kara da lissafo wasu dalilai da suke haduwa wajen wargaza aure. Sun hada da tara mata da yawa da kuma rashin soyayya a yayin da auren ke kara dadewa.

DUBA WANNAN: Abinda yasa aka tsige Sarki Sanusi - Tanko Yakasai

"Rashin kudi a aure na faruwa ne a yayin da miji ya kasa samar da abubuwab da ake bukata a gida. Hakan na samar da matsaloli a cikin gida kuma matukar matar ba ta da fahimta matsala kan kunni kai.

"A rayuwar auren musulmai, akwai matsallin da suka danganci tara mata da yawa. A tunani na ya kamata mata su fara sabwa da yadda halayyar namiji take. Namiji ya saba tara mata kuma babu abinda mace za ta iya yi a kai.

"Wata matsalar kuwa ita ce matsalar rashin soyayya. Wasu sun yarda cewa a yayin da mace ke tsufa, a daina nuna mata soyayya. Wannan ba haka bane kuma ya kamata maza su gyara," AbdulRauf ya ce.

Ya yi kira ga ma'aurata da su so juna tun daga farkon aure har zuwa karshensa komai rintsi da tsananin kalubalen da ake fuskanta a gidan aure.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel