Tirkashi: An Hango Abin da Zai Hana Atiku Zama Shugaban Kasa a 2027
- Nyesom Wike ya yi magana kan burin Atiku Abubakar na neman shugabancin Najeriya a ƙarƙashin ADC a zaben 2027
- Ministan na Abuja ya ce ya kasance cikin G5 da suka yi adawa da takarar Atiku a PDP a 2023, saboda rashin bin tsarin rabon mulki na karba-karba
- Wike ya sake jaddada goyon bayansa ga sake zaɓen Bola Tinubu, yana cewa ba zai zauna ya zura ido ya bar Atiku ya ci zaɓen 2027 ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT Abuja, Najeriya - Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya yi magana kan burin Atiku na zama shugaban kasa a zaben 2027.
Nyesom Wike ya bayyana dalilin da ya sa yake ganin Atiku Abubakar ba zai iya lashe zaɓen shugaban ƙasa da za a gudanar a ranar 16 ga Janairu 2027 ba.

Source: Twitter
Meyasa Atiku ba zai ci zabe ba a 2027?
Ministan ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da manema labarai a ranar Laraba, 2 ga watan Satumban 2026, cewar rahoton jaridar The Nation.
Wike ya ce burin Atiku na neman shugabancin ƙasar ƙarƙashin jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ya saɓa wa tsarin karba-karba na mulki tsakanin Arewa da Kudu.
A cewarsa, tsarin karba-karba na mulki ya samo asali ne daga buƙatar tabbatar da adalci, daidaito da kuma gaskiya wajen raba madafun iko tsakanin yankunan ƙasar.
Wike ya tuna da rikicin PDP da Atiku
Ministan ya tuna cewa shi ma yana cikin G5, wato ƙungiyar gwamnoni biyar na PDP da suka yi adawa da takarar Atiku a zaɓen 2023 saboda irin wannan dalili.
Ya ce a lokacin, G5 ta yi amanna cewa PDP ta gaza bin tsarin daidaita rabon shugabanci tsakanin Arewa da Kudu.
Wike ya ce har yanzu yana nan kan matsayinsa, kuma ya yanke shawarar kasancewa cikin sahun gaba wajen yaƙin ganin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sake lashe zaɓen 2027.

Kara karanta wannan
Zaben 2027: Wike ya yi hasashen kuri'un da Atiku, Tinubu za su samu a Arewa da Kudu
Ya ƙara da cewa idan jam’iyyun adawa suka kafa gwamnati bayan zaɓen 2027, shi ne zai kasance cikin manyan mutanen da za su fara fuskantar matsala, The Punch ta kawo labarin.
‘Ba zan zuba ido na bar Atiku ya ci ba’
Wike ya bayyana cewa ba zai zauna hannu bibbiyu ya zura ido Atiku ya lashe zaɓen shugaban ƙasa na 2027 ba.
Ya tuna yadda G5 ta haɗa kai da tsohon Gwamnan Jihar Benue, Samuel Ortom, wajen dakile burin Atiku a jihar Benue a zaɓen 2023.
Ministan ya ce ba ya nadamar matakin da suka ɗauka a lokacin, yana mai cewa babu wani uzuri da zai bayar kan adawar da suka yi da takarar Atiku.

Source: Twitter
Wike ya yi hasashe kan Atiku da Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya yi hasashen cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai samu akalla kashi 25 cikin 100 na ƙuri’u a kowace jiha ta Arewa a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
Wike ya kuma bayyana cewa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ba zai samu kashi 10 cikin 100 na ƙuri’u a wasu jihohin Kudancin Najeriya ba.
Asali: Legit.ng
