Yadda Tinubu Ya Yi Amfani da Obi Ya Raunata Atiku a Zaben 2023 a Najeriya
- Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya bayyana yadda shi da abokansa suka yi dabarun siyasa wajen rage damar Atiku da Obi a zaɓen 2023
- Wike ya ce sun tallafa wa Peter Obi a Kudu maso Gabas domin hana Atiku samun ƙuri’u masu yawa, inda ya bayyana hakan a matsayin dabarar siyasa
- Ministan ya ce zai goyi bayan sake zaɓen Tinubu a 2027, yana hasashen shugaban zai samu akalla kashi 25 cikin 100 a kowace jiha.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Miinistan Abuja, Nyesom Wike, ya bayyana yadda shi da wasu abokan siyasarsa suka yi aiki wajen dakile burin Atiku Abubakar da Peter Obi a zaɓen 2023.
Wike ya ce wannan matakin ya taimaka wajen buɗe hanyar samun nasarar Shugaba Bola Tinubu a zaɓen shugaban ƙasa na 2023.

Kara karanta wannan
Zaben 2027: Wike ya yi hasashen kuri'un da Atiku, Tinubu za su samu a Arewa da Kudu

Source: Twitter
Ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da manema labarai a Fatakwal, Rivers, wadda aka bibiyi a Abuja ranar Laraba.
Wike ya kuma ce idan Atiku, ɗan takarar ADC, ko Obi, ɗan takarar NDC, ya kayar da Tinubu a 2027, shi zai kasance cikin ‘yan siyasar farko da za su fuskanci ramuwar siyasa.
Ministan ya ce goyon bayan da yake bai wa Tinubu a fili ya sa ‘yan adawa ke kallonsa a matsayin makiyi, amma bai yi nadamar matsayinsa ba.
Daga nan Wike ya bayyana yadda shi da abokansa suka yi ƙoƙarin rage damar Atiku a zaɓen 2023, musamman a yankin Kudu maso Gabas.
Ya ce:
"Manta da duk surutun da za a yi kan Obi, mun ba shi Kudu maso Gabas ne'"
Ya ce tsohon gwamnan Benue, Samuel Ortom, yana cikin muhimman mutanen da dabarar ta shafa, saboda rashin jin daɗinsa da tikitin Musulmi da Musulmi na APC.
Ministan Abuja ya ce wannan dabara ta hana Atiku samun gagarumar goyon baya a wasu sassan Kudu, kuma ta taimaka wajen kayar da shi.
Ya ce sakamakon zaɓen ya samo asali ne daga dabarun siyasa da aka yi a cikin jam’iyyar PDP, musamman yadda wasu ‘yan cikinta suka yi siyasa bisa muradunsu.
Rikicin Wike da wasu gwamnoni
Dangane da alaƙarsa da wasu gwamnoni gabanin zaɓen 2027, Wike ya zargi gwamnonin Kwara da Imo, AbdulRahman AbdulRazaq da Hope Uzodimma, da aiki a kansa.
Wike ya ce AbdulRazaq ne ya jagoranci abin da ya kira kamfen na adawa da shi a wurare daban-daban, kuma ya ce ya taɓa tunkarar gwamnan kai tsaye.
A cewar Wike, AbdulRazaq ya zarge shi da ɗaukar nauyin ‘yan takarar da ke hamayya da waɗanda gwamnan yake so su samu nasara a Kwara.
Wike ya kuma tuna da rashin jituwa tsakaninsa da Uzodimma, yana cewa gwamnan Imo ya san irin taimakon siyasar da ya taɓa ba shi.
'Matsalar da zan fuskanta daga Obi, Atiku' - Wike
An ji cewa Ministan Abuja, Nyesom Wike ya ce zai zama ɗan siyasar farko da Atiku Abubakar ko Peter Obi za su far wa bayan zaben 2027.
Wike ya ce duk da kasancewarsa ɗan PDP, zai ci gaba da goyon bayan sake zaɓen Bola Tinubu kuma bai yi nadama ba.
Ministan Abuja ya ce duk suka da kiraye-kirayen abokan hamayyarsa ba za su sa ya janye goyon bayansa ga Tinubu ba.
Asali: Legit.ng

