INEC Ta Fadi Abin da ake Tsoro Ya Hana Zaben 2027 Zama Sahihi
- INEC ta yi gargadin cewa yaɗa labaran ƙarya da fasahar basirar wucin gadi (AI) ke samarwa na iya yin barazana ga sahihancin zaɓen 2027
- Shugaban INEC ya ce hukumar na duba tsarin fasaharta na zaɓe tare da shirin gudanar da gwajin zaɓen shugaban ƙasa kafin babban zaɓen
- Ya ce amfani da AI wajen ƙirƙirar sauti, bidiyo da hotuna na ƙarya na ƙara wahalar gano bayanan bogi, lamarin da ka iya yaɗuwa ga jama'a
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru huɗu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Abuja – Hukumar INEC ta yi gargadin cewa yaɗa bayanan ƙarya da fasahar basirar AI ke samarwa na iya yin babbar barazana ga sahihancin zaɓen 2027.
Shugaban hukumar, Farfesa Joash Amupitan, ya bayyana hakan ne a ranar Laraba a Abuja, a wani jawabi da kwamishinan INEC, Sani Adam (SAN), ya gabatar a madadinsa.

Source: Twitter
Rahoton Punch ya nuna cewa jawabin na cikin taron ƙasa da ƙasa karo na 13 na Ƙungiyar Masana Sadarwa da Kwararrun Sadarwa ta Najeriya.
INEC na duba tsarin fasaharta
Amupitan ya bayyana cewa INEC na gudanar da cikakken bincike kan tsarin fasahar da take amfani da shi wajen gudanar da zaɓe domin tabbatar da shirin hukumar gabanin zaɓen 2027.
Ya ce binciken zai haɗa da duba hanyoyin kariya daga matsalolin tsarin, gwajin tsaro na na'urori da kuma tsare-tsaren farfaɗowa idan wata matsala ta faru.
AI na ƙara barazana ga 2027
Amupitan ya ce hukumar na damuwa matuƙa kan yadda ake ƙara amfani da fasahar AI wajen ƙirƙirar sauti, bidiyo da hotuna na ƙarya da za su iya ruɗar masu zaɓe.
Ya ce wannan fasaha ta sauƙaƙa samar da abubuwan bogi tare da ƙara wahalar gano su, yayin da irin waɗannan abubuwa suka fara bayyana a wasu zaɓukan da aka gudanar a Afirka ta Yamma da Gabashin Afirka.

Kara karanta wannan
Atiku ya ɗauki alkawarin da zai faranta wa ɗaliban Najeriya rai kan kuɗin NELFUND
Ya ce barazanar ba ta tsaya kan ƙirƙirar labaran ƙarya kai tsaye ba, domin ana iya amfani da AI wajen rarraba sakonni daban-daban na masu zaɓe.

Source: Facebook
Tsarin yaƙi da bayanan ƙarya
Arise News ta wallafa cewa Amupitan ya bayyana wasu matakai biyar da hukumar za ta yi amfani da su wajen ƙarfafa yaƙi da sababbin matsalolin sadarwa a lokacin zaɓe.
Matakan sun haɗa da haɗa tsarin fasaha da sadarwa, samar da tsarin mayar da martani cikin gaggawa kan bayanan ƙarya, sanar da jama'a tun da wuri kan matsalolin da za su iya faruwa da hanyoyin kariya daga gare su.
Sauran matakan sun haɗa da ƙarfafa haɗin gwiwa da masana harkar sadarwa, masu tantance gaskiya da kamfanonin fasaha, da kuma ci gaba da ilmantar da jama'a kan yadda za su tantance sahihancin bayanai.
Batur shari'ar Tinubu da Atiku
A wani labarin, mun ruwaito cewa babbar kotun tarayya da ke Abuja ta dage sauraron ƙarar da ke neman hana Shugaba Bola Ahmed Tinubu tsayawa takarar 2027 kan NYSC.
Lauyan mai ƙara, Joseph Onu, ya shaida wa kotun cewa bai samu damar miƙa wa wanda ake ƙara takardun ƙarar da kansa ba, inda ya nemi izinin kotu ya yi amfani da wata hanyar miƙa takardun.
Ƙarar da Atiku Abubakar ya shigar ta ƙalubalanci cancantar Tinubu na neman wani wa'adi, inda aka yi zargin cewa sunan da ke kan takardar NYSC da aka miƙa wa INEC ya bambanta da sunan shi.
Asali: Legit.ng
