An Fadi Jihohi 3 da APC Za Ta Sha Wahala, Za Ta ‘Lashe’ Wasu 18 cikin Sauki
- Bashir Ahmad ya ware jihohin Najeriya zuwa rukuni uku, inda ya ce APC za ta lashe jihohi 18 cikin sauki a zaɓen 2027
- Ya bayyana Kano, Adamawa, Taraba, Enugu, Ebonyi, Plateau, Rivers, Bayelsa, Abuja da Oyo a matsayin jihohin da za a fafata sosai
- Ahmad ya ce akwai jihohi uku da APC za ta fuskanci matsala mafi girma wajen samun nasara a 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Tsohon hadimin shugaban ƙasa kuma babban jigo a jam’iyyar APC, Bashir Ahmad ya yi hasashen zaben 2027.
Bashir Ahmad ya bayyana hasashensa kan yadda jam’iyyar APC za ta kasance a zaɓen 2027.

Source: Facebook
Ya wallafa wannan hasashe ne a shafinsa na X, inda ya bayyana jihohi 18 da yake ganin APC za ta iya lashewa, 10 da za a fafata sosai, da kuma uku masu wahala.
Ahmad ya raba jihohin Najeriya zuwa rukuni uku, wato jihohin da APC ke da tabbacin samun nasara, waɗanda za a fafata sosai da kuma waɗanda za su kasance masu wahala.
'Jihohin da APC za ta iya lashewa'
A cewar Ahmad, APC na iya dogaro da Kaduna, Borno, Yobe, Jigawa, Katsina, Kebbi, Ekiti, Lagos, Osun, Ondo, Niger, Nasarawa, Cross River, Akwa Ibom, Ogun, Sokoto da Zamfara.
Jerin ya fi karkata ne zuwa jihohin Arewa maso Yamma da Arewa maso Gabas, yankunan da suka kasance suna bai wa jam’iyyar APC ƙuri’u masu yawa a baya.
Haka kuma, wasu jihohin Kudu maso Yamma suna cikin jerin jihohin da Ahmad ya yi hasashen APC za ta samu nasara.
Jihohin da za a fafata sosai
Ahmad ya sanya Kano, Adamawa, Taraba, Enugu, Ebonyi, Plateau, Rivers, Bayelsa, Abuja da Oyo cikin jihohin da za a fafata sosai.
Wannan na nufin APC za ta buƙaci yin aiki tukuru domin riƙe wasu daga cikin waɗannan jihohi ko kuma samun nasara a wuraren da ba ta mulki.

Source: Twitter
Jihohin da APC za ta sha wahala
Bashir Ahmad ya bayyana Anambra, Abia da Bauchi a matsayin jihohi uku da APC za ta fuskanci babban ƙalubale wajen samun nasara a zaɓen 2027.
Jihohin Anambra da Abia da ke Kudu maso Gabas sun daɗe suna zama ƙalubale ga APC, yayin da Bauchi ke nuna yiwuwar fuskantar matsin lamba daga ‘yan adawa ko rikicin cikin gida.
Sai dai Ahmad bai bayyana jihohin da yake ganin APC za ta yi rashin nasara kai tsaye ba, domin ya mayar da hankali ne kan matakin wahalar da jam’iyyar za ta fuskanta.
Wannan hasashe ya zo ne yayin da harkokin siyasa ke ƙara ƙamari a Najeriya gabanin babban zaɓen 2027, yayin da jam’iyyu ke fara tsara dabarunsu.
An sace shugaban APC a Kano
A wani labarin, mun ruwaito cewa wasu ‘yan bindiga sun kai hari garin Beli da ke Kano a daren Litinin 31 ga watan Agustan 2027.

Kara karanta wannan
Zaben 2027: Wike ya yi hasashen kuri'un da Atiku, Tinubu za su samu a Arewa da Kudu
‘Yan bindigar sun yi garkuwa da shugaban APC na ƙaramar hukumar Rogo, Alhaji Abdullahi Fanka.
Mazauna yankin sun ce maharan sun tsere zuwa ƙauyen Babbarika, inda suka bar babura uku, sannan daga baya aka kama wani mutum da ake zargi da hannu.
Asali: Legit.ng

