'A Bar 'Yan Najeriya Su Yanke Hukunci': Bashir Ahmad Ya Kalubalanci Kwankwaso

'A Bar 'Yan Najeriya Su Yanke Hukunci': Bashir Ahmad Ya Kalubalanci Kwankwaso

  • Bashir Ahmad ya ce bai yarda da kallon kwamitin yakin neman zaben APC a 2027 a matsayin yaƙi tsakanin masu danniya da wadanda ake zalunta ba
  • Bashir wanda jigo ne a tafiyar City Boys Movement ya ce ya kamata a tantance APC ne bisa manufofinta, shirye-shiryenta, tarihinta da ƙwarewar shugabanninta
  • Ya bayyana haka ne a matsayin martani ga Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, dan takarar mataimakin shugaban kasa a jam'iyyar NDC a zaben 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Darakta na kasa kan yada labarai na City Movement, Bashir Ahmad ya ce bai amince da yadda Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ke kwatanta kwamitin yakin neman zaben APC ba.

Ya ce batun zaben 2027 da Kwankwas ta ce tsakanin 'masu danniya da wadanda ake yi wa mulkin danniya ne' ba haka batun ya ke ba.

Kara karanta wannan

APC, ADC da jam'iyyun da suka bayyana shirinsu na fara yakin neman zaben shugaban kasa

Bashir Ahmad ya yi martani ga Kwankwaso
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, Bashir Ahmad Hoto; Hon Saifullahi Hassan/Bashir Ahmad
Source: Facebook

Bashir Ahmad ya bayyana haka ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na X jim kadan bayan Sanata Rabiu Musa Kwankwasi ya yi fata-fata da kwamitin yakin neman zaben APC.

Martanin Bashir Ahmad ga Kwankwaso

A cikin sakon, Bashir Ahmad ya ce yana ganin ya dace a riƙa bibiyar ayyukan kowace gwamnati tare da buƙatar ingantaccen shugabanci.

Ya ce:

“Ina mutunta ra’ayin da ya bayyana kwamitin yakin neman zaben APC da wannan salo, amma ina da bambancin ra’ayi da shi. Ya dace a binciki kowace gwamnati tare da buƙatar ingantaccen shugabanci, amma mayar da fafatawar 2027 zuwa yaƙi tsakanin masu danniya da waɗanda ake danniya ba zai taimaka wajen inganta muhawara mai ma’ana kan makomar ƙasa ba.”

Yan Najeriya za su yanke hukunci - Bashir

A cewarsa, ya kamata a yi wa kwamitin APC hukunci ne bisa manufofi, shirye-shirye da hangen nesan da za ta gabatar wa ’yan Najeriya, ba wai kawai bisa siyasar ko matsayin mutanen da ke cikinta ba.

Kara karanta wannan

Ainihin dalilin gwamna Nasir Idris na sauya mataimakinsa a 2027

Bashir Ahmad ya ce a bar yan Najeriya su yi APC alkalanci
Bashir Ahmad, tsohon hadimin shugaban kasar Najeriya Hoto: Bashir Ahmad
Source: Twitter

Bashir Ahmad ya ce:

“Ya kamata a tantance kwamitin yakin neman zaben APC ne bisa manufofi, shirye-shirye da hangen nesan da take gabatar wa ’yan Najeriya, ba wai kawai bisa siyasar mutanen da ke cikinta ba. Zaɓen 2027 kuma ya kamata ya zama fafatawa ta ra’ayoyi, tarihin ayyuka, ƙwarewa da mabambantan hangen nesa kan makomar Najeriya."

Da yake magana kan tsohon gwamnan Jihar Zamfara, Sanata Abdul’aziz Yari, Bashir Ahmad ya ce ya kamata a ba shi damar yanke shawarar kansa kan ko zai karɓi wani nauyi na ƙasa.

Ya ƙara da cewa ’yan Najeriya ba mutanen da ke jiran ’yan siyasa su gaya musu abin da za su zaɓa ba ne, yana mai cewa suna da ƙwarewar tantance tarihin gwamnatoci da kwatanta hanyoyin da ake gabatar musu.

Bashir ya ce saboda haka ya kamata zaɓen 2027 ya fi mayar da hankali kan ayyukan gwamnati, ra’ayoyi da makomar Najeriya, maimakon amfani da kalmomin da za su iya rura wutar rikici kamar “masu danniya” da “waɗanda ake danniya”.

Kara karanta wannan

"Jama'a sun waye": Jigo a APC ya hango abin da zai sanya Tinubu ya fadi a 2027

“Bari ’yan Najeriya su yanke hukunci,” in ji shi.

Kwankwaso ya soki kwamitin APC

A baya, kun ji cewa Rabi’u Musa Kwankwaso ya soki tsarin kwamitin yakin neman zaben APC ta 2027, yana cewa ya ƙunshi mutanen da suka goyi bayan gwamnatin yanzu.

Ya buƙaci Sanata Abdul’aziz Yari ya sake tunanin karɓar shugabancin kwamitin yaƙin neman zaɓen APC da sake nazari game da goyin bayan Bola Ahmed Tinubu.

Sanata Kwankwaso ya kuma 'diga ayar tambaya game da dacewar shigar manyan jami’an gwamnati tsarin tara kuɗin yaƙin neman zaɓen jam’iyya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng