Bayan Tinubu, Ana Zargin Amurka na da Bayanan Manyan Yan Takarar Shugaban Kasa a Najeriya

Bayan Tinubu, Ana Zargin Amurka na da Bayanan Manyan Yan Takarar Shugaban Kasa a Najeriya

  • Reno Omokri ya ce dukkan manyan ’yan takarar shugaban kasa a zaben 2027 suna da bayanai a hukumar FBI ta Amurka
  • Tsohon mai magana da yawun shugaban kasa ya ce kasancewar mutum yana da bayanai a FBI ba yana nufin yana da tarihin aikata laifi ba
  • Omokri ya ce babu wani bayanin aikata laifi da FBI ke da shi kan Shugaba Bola Ahmed Tinubu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Jakadan Najeriya mai jiran zuwa Mexico, Reno Omokri, ya ce akwai bayanan dukkan ’yan takarar shugaban kasa a zaben 2027 a Hukumar Binciken Manyan Laifuffuka ta Amurka (FBI).

Reno Omokri ya ce kasancewar mutum yana da bayanai a hukumar FBI ba yana nufin yana da tarihin aikata laifi ba.

Reno Omokri.
Jakadan Najeriya mai jiran gado da aka tura kasar Mexico, Reno Omokri Hoto: Reno Omokri
Source: Facebook

Ya bayyana hakan ne yayin wata hira a shirin City Boy Movement Podcast da ya wallafa a X, yayin da yake amsa tambayoyi kan takardun da suka shafi Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Kara karanta wannan

Wasikar da Amurka ta aiko Najeriya ta bayyana ainihin shekarun Tinubu a duniya

Bambanci tsakanin bayanai da tarihin laifi

Omokri ya ce wajibi ne ’yan Najeriya su fahimci bambanci tsakanin bayanan da FBI ke da su kan mutum da kuma tarihin aikata laifi. Ya zargi masu yada ikirarin cewa Tinubu yana da tarihin laifi da kokarin rikita jama’a.

Ya ce:

“Dukkan ’yan takarar wannan zabe suna da bayanai a FBI, har da Atiku Abubakar da Peter Obi. Abin da suke cewa game da Shugaba Bola Ahmed Tinubu, shin ikirari ne kawai? Ba ikirari ba ne. Gaskiya ce. Idan kuna son in tabbatar da hakan, zan tabbatar.”

Ya bayyana cewa kasancewar sunan mutum ko bayanansa suna cikin bayanan FBI bai kamata kai tsaye a fassara hakan a matsayin hujjar aikata laifi ba.

“Bayanan mutum dai bayanai ne kawai. Akwai bambanci tsakanin bayanai da tarihin aikata laifi," in ji shi.

Dalilan samun bayanai a FBI

A cewar Omokri, akwai hanyoyi daban-daban da bayanan mutum za su iya shiga tsarin FBI sakamakon mu’amalarsa da hukumomin Amurka daga ciki akwai neman bizar Amurka da kuma binciken tarihin mutum.

Kara karanta wannan

"Zan fadi abin da zai iya girgiza kasar"; Omokri ya fayyace bayanan Tinubu da ke hannun FBI

Omokri ya ce:

“FBI tana da wani nauyi da ya shafi duk wanda ya nemi bizar Amurka ko kuma aka yi masa binciken tarihinsa a Amurka, za a iya samun bayanansa a FBI.”

Ya zargi masu amfani da batun bayanan FBI a muhawarar siyasa da anfani da rashin fahimtar jama’a game da bambanci tsakanin bayanan mutum na yau da kullum da tarihin aikata laifi.

Ya ce wasu suna amfani da yanayin yadda jama’a ke saurin ɗaukar batutuwa da muhimmanci wajen tayar da hankali idan aka ambaci FBI.

Omokri da Tinubu.
Remo Omokri tare da Shugaba Bola Ahmed Tinubu lokacin da ya kai masa ziyara a fadar Aso Rock, Abuja Hoto: Reno Omokri
Source: Facebook

Omokri ya kare Shugaba Tinubu

Omokri ya kuma nace cewa babu wani rahoton aikata laifi da hukumar FBI ke da shi kan Shugaba Tinubu.

Ya yi nuni da wata takarda da ya ce ta fito daga FBI ta hannun Ofishin Jakadancin Amurka, wadda ta shafi binciken bayanan Tinubu bisa buƙatar hukumomin Najeriya.

A cewarsa, takardar ta nuna cewa binciken bai gano wani tarihin kama Tinubu bisa laifi ko wani sammacin kama shi ba.

Kara karanta wannan

Lauya ya tsage gaskiya, an ji dalilin da ya sa Amurka ba ta kama Shugaba Tinubu ba

Waiskar Amurka ta nuna shekarun Tinubu

Kun ji cewa Reno Omokri ya fitar da wata wasika da Amurka ta aiko Najeriya tun 2003, wacce ke dauki da ranar haihuwar shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu.

Wasikar ta ƙunshi sakamakon binciken bayanan laifuffuka da hukumar binciken manyan laifuffuka ta Amurka, FBI ta gudanar kan Tinubu ta hanyar cibiyar NCIC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262