Rahoton FBI: APM Ta Tura Sako Amurka, Tana Neman Kara Kunno Wa Shugaba Tinubu Wuta
- Jam’iyyar APM ta bukaci hukumomin Amurka su bayyana sakamakon rahoton FBI kan zarge-zargen safarar miyagun kwayoyi da ake wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu
- APM ta ce za a iya fitar da wasu sassan rahoton da ba za su jefa rayuka cikin hadari ko tona asirin shaidu da masu bincike ba
- Jam’iyyar ta ce kokarin Tinubu na hana fitar da rahoton na kara haifar da zargin cewa yana kokarin boye gaskiya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Jam’iyyar APM ta bukaci hukumomin Amurka da su bayyana wa jama’a sakamakon rahoton FBI kan safarar miyagun kwayoyi da ake zargin suna da alaka da Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
APM ta ce hukumomin Amurka za su iya fitar da sassan rahoton da ba za su “jefa rayuka cikin hadari, tona asirin shaidu, masu bincike ko hanyoyin da aka yi amfani da su wajen gudanar da binciken” ba.

Source: Twitter
Jam’iyyar ta yi wannan kiran ne cikin wata sanarwa da Yusuf Abubakar, sakataren yada labaranta na kasa, ya fitar ranar Lahadi, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
APM ta yi magana kan rahoton FBI
Jam’iyyar ta ce kokarin da Shugaba Tinubu na hana jama’a samun rahoton ya kara sanya shakku kan ko yana da hannu a lamarin, tare da nuna cewa ana kokarin rufe batun.
APM ta bukaci hukumomin Amurka su fahimci cewa boye irin wannan bayani na iya haifar da babbar illa ga tsaron Najeriya, martabar kasar da ci gaban dimokuradiyya.
Jam'iyyar ta ce:
“Kasancewar Amurka na daya daga cikin manyan kasashen dimokuradiyya a duniya, ya kamata a ko da yaushe a gan ta tana taimakawa wajen karfafa dimokuradiya a yakin duniya da ake yi da safarar miyagun kwayoyi da cin hanci da rashawa.
APM ta tabo batun kwace Dala 460,000
APM ta ce hakan ya kara zama abin damuwa musamman ganin cewa jama’a sun riga sun san da hukuncin kwace Dala 460,000 da aka yanke a 1993 kan asusun da kotun Amurka ta danganta da Tinubu,.
A rahoton Vanguard, sanarwar ta ce
“Sakamakon hukuncin kwace dala 460,000, bisa sashe na 137 na Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Najeriya na shekarar 1999, Shugaba Tinubu bai cancanci tsayawa takara a Najeriya ba.
"Bugu da kari, Najeriya ta rattaba hannu kan yarjejeniyoyin kasa da kasa kan miyagun kwayoyi da safarar kudaden haram.”

Source: UGC
Yayin da zaben shugaban kasa ke kara karatowa, APM ta bukaci hukumomin Amurka su taimaka wa ’yan Najeriya wajen yanke shawarar zaben shugaba wanda ba shi da nauyin zarge-zarge da shari’o’in cin hanci da rashawa.
Tinubu ya shigar da kara a kotun Amurka
A wani labarin, kun ji cewa Shugaba Bola Tinubu ya shigar da ƙara a wata kotun Amurka domin hana hukumomin ƙasar fitar da wasu bayanai da suka shafi zarge-zargen safarar ƙwayoyi.
Tinubu na ƙalubalantar Ma’aikatar Shari’a ta Amurka, FBI da DEA kan sakin bayanan da wani mai fafutukar ganin an samu gaskiya, Aaron Greenspan, ya nema.
Asali: Legit.ng

