2027: An Fadi wanda Ya Kamata Yan Adawa Su Tsayar Takara tsakanin Atiku da Obi

2027: An Fadi wanda Ya Kamata Yan Adawa Su Tsayar Takara tsakanin Atiku da Obi

  • Gidauniyar Igbo Heroes and Icons Foundation ta ba shawarci kwamitin jam’iyyun adawa ya amince da Peter Obi
  • Ta ce ƙwarewar Obi, gaskiyarsa da manufofinsa, da kuma tarihin mulkinsa a Anambra sun tabbatar da cancantarsa
  • IHIF ta ce Kudu maso Gabas ba ta samar da zababben shugaban Najeriya tun 1999 ba, tana ganin lokaci ya yi da za a gyara tsarin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja — Gidauniyar Igbo Heroes and Icons Foundation, IHIF, ta bukaci kwamitin jam’iyyun adawa ya amince da Peter Obi.

Gidauniyar ta nemi a amince da ɗan takarar shugaban ƙasa na Nigeria Democratic Congress, NDC, Peter Obi, a matsayin ɗan takarar haɗin gwiwa.

Ana son tsayar da Obi takarar adawa a 2027
Dan takarar shugaban kasa a NDC, Peter Obi da na ADC, Atiku Abubakar. Hoto: Mr Peter Obi, Atiku Abubakar.
Source: Facebook

A cikin wata sanarwa da Kodinetan ƙasa na gidauniyar, Chinedu Nsofor, ya amince da ita, ta ce Obi ya cancanta, cewar Vanguard.

Kara karanta wannan

Miyetti Allah ta kaɗa hantar Tinubu, ta fada masa sharaɗin sake zaɓensa a 2027

Ta ce ya kamata Obi ya zama ɗan takarar da jam’iyyun adawa za su mara wa baya a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Gidauniyar ta ce ƙwarewar Obi, gaskiyarsa da kuma tsayawarsa kan ƙa’idoji sun sa ta ganin shi ne wanda ya fi cancanta.

Kudu maso Gabas da shugabancin Najeriya

Gidauniyar ta kuma ce Kudu maso Gabas ita ce babbar shiyya ɗaya tilo da ba ta samar da zababben shugaban Najeriya ba tun shekarar 1999.

Ta bayyana hakan a matsayin rashin daidaito da ya kamata a gyara domin ƙarfafa haɗin kan ƙasa da kuma tabbatar da adalci.

Ta ce:

“Tsawon shekaru, al’ummar Igbo sun goyi bayan ’yan takarar shugaban ƙasa daga wasu yankuna domin haɗin kan ƙasa.”
“Mun yi imanin cewa lokaci ya yi da sauran yankuna za su rama wannan alheri ta hanyar goyon bayan ɗan takara mai nagarta daga Kudu maso Gabas, wannan ɗan takarar shi ne Peter Obi."

Kara karanta wannan

Ana batun zaben 2027, Kwankwaso ya aika sako kan makomar Najeriya

Dalilin da ya sa suka goyi bayan Obi

Ƙungiyar ta kuma ambaci tarihin Obi a harkar kasuwanci, tana mai cewa hakan ya ƙara mata kwarin gwiwar cewa zai iya sauya tattalin arzikin Najeriya.

Ta ce Obi zai iya sauya Najeriya daga tattalin arzikin da ya fi dogaro da amfani zuwa tattalin arzikin da ya fi karkata ga samarwa.

Gidauniyar ta ce za a iya cimma hakan ta hanyar bunƙasa noma, masana’antu da ƙirƙirar ƙarin darajar kayayyaki.

IHIF ta bayyana goyon bayanta ga Obi a matsayin “ba wai kawai manufar Igbo ba ce”, tana kira ga kowa ya mara masa baya.

Ta bukaci jam’iyyun siyasa, masu ruwa da tsaki da ’yan Najeriya daga kabilu da addinai daban-daban su goyi bayan Obi.

Gidauniyar ta ce:

“Mun yi imanin cewa shi ne shugaban da ya fi dacewa ya ceto Najeriya daga matsalolin tattalin arzikinta na yanzu.”

Ta ƙara da cewa Obi zai taimaka wajen hana ƙasar ci gaba da fadawa cikin bashi, talauci da koma bayan hukumomi.

Kara karanta wannan

Mummunan hatsarin mota ya laƙume ran shugaban Miyetti Allah a Abuja

'Bambancin Atiku, Obi da Tinubu'

Mun ba ku labarin cewa jigon NDC, Ibrahim Abdulkarim ya ce Shugaba Bola Tinubu da Atiku Abubakar suna neman ikon siyasa, yayin da Peter Obi ke neman damar yi wa Najeriya hidima.

Dan NDC ya ce matsalar Najeriya ba rashin sanin ƙalubalen ƙasar ba ce, illa rashin ƙarfin zuciya wajen aiwatar da hanyoyin magance su.

Ibrahim Abdulkarim ya kira matasa da su mallaki harkar siyasa tare da mara wa Obi baya, yana cewa goyon bayansa tamkar goyon bayan kansu ne.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.