Mummunan Hatsarin Mota Ya Laƙume Ran Shugaban Miyetti Allah a Abuja

Mummunan Hatsarin Mota Ya Laƙume Ran Shugaban Miyetti Allah a Abuja

  • Shugaban MACBAN na Abuja, Alhaji Ardo Wokili Madugu, ya rasu bayan tirela ta faɗa kan motar da yake ciki a hanyar Lambata-Izom.
  • Hatsarin ya faru da misalin ƙarfe 4:38 na yammacin Lahadi, lokacin da tirela ta faɗa cikin rami, ta faɗa kan motar kasuwanci
  • An birne marigayin a gidansa da ke Gwako, inda shugabannin MACBAN da sauran manyan jami’ai suka halarci sallar jana’izarsa tare da iyalansa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Shugaban reshen MACBAN na Babban Birnin Tarayya Abuja, Alhaji Ardo Wokili Madugu, ya rasu sakamakon wani hatsarin mota da ya faru a jihar Neja.

Hatsarin ya afku ne a hanyar Lambata-Izom, inda wata tirela ta faɗa cikin wani babban rami, sannan ta faɗa kan motar da Madugu ke ciki.

Shugaban Miyetti Allah a Abuja ya rasu
Taswirar babban birnin tarayyar Najeriya, Abuja. Hoto: Legit.
Source: Original

Alhaji Ahmed Dahiru, mataimaki na musamman kan yaɗa labarai da hulɗa da jama’a na MACBAN a Abuja, shi ne ya tabbatar da rasuwar, cewar Daily Trust.

Kara karanta wannan

Atiku ya ɗauki alkawarin da zai faranta wa ɗaliban Najeriya rai kan kuɗin NELFUND

Dahiru ya ce hatsarin ya faru ne da misalin ƙarfe 4:38 na yammacin Lahadi, a kusa da ƙauyen Malam-Karo, kusa da Maje.

Ya bayyana cewa Madugu ya makale a cikin motar, inda ya mutu nan take bayan tirelar ta faɗa kan motar kasuwancin da yake ciki.

Dahiru ya ce har yanzu bai iya tabbatar da adadin sauran mutanen da suka shiga cikin hatsarin ba, ko kuma wadanda suka samu raunuka.

Jami’an Hukumar Kiyaye Haɗurra ta Ƙasa (FRSC), reshen Sabon-Wuse, sun ɗauki gawar marigayin cikin motar asibiti zuwa gidansa da ke ƙauyen Gwako.

An kai gawar ne zuwa Gwako, Gwagwalada, a daren Lahadi, inda daga bisani aka yi jana’izarsa a gidansa da ke yankin.

Shugaban ƙasa na MACBAN, Alhaji Baba Usman Ngelzarma, ya halarci sallar jana’izar tare da tsohon shugaban ƙungiyar na Abuja, Alhaji Yahaya Isah.

Haka kuma, shugabannin MACBAN na ƙananan hukumomi shida da ke Abuja sun halarci jana’izar tare da sauran mambobin ƙungiyar.

Aguma na Gwagwalada, Mai Martaba Alhaji Muhammad Magaji, shi ma ya halarci jana’izar tare da shugaban Gwagwalada, Hon. Kasim Mohammed Ikwa.

Kara karanta wannan

Shin da gaske Atiku zai sayar da bankin CBN idan ya zama shugaban kasa?

Haka nan, Ardo da ke wakiltar al’ummomin Fulani daban-daban a Abuja sun halarci jana’izar domin nuna goyon baya ga iyalan marigayin.

A wani labari, shugaban Gwagwalada, Hon. Kasim Mohammed Ikwa, ya mika ta’aziyyarsa ga iyalan Madugu da al’ummar Fulani bisa rasuwar shugaban MACBAN.

A cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara kan yaɗa labarai da hulɗa da jama’a, Mohammed Isah Hassan, ya fitar, Ikwa ya bayyana kaduwa.

Ikwa ya ce ya karɓi labarin rasuwar Madugu cikin matuƙar kaduwa da baƙin ciki, yana mai bayyana rasuwar a matsayin babban rashi.

Shugaban ya bayyana marigayin a matsayin mutum mai gaskiya da sauƙin kai, sannan ya yi addu’ar Allah Ya jiƙan shi da rahama.

An kashe shugaban Miyetti Allah a Benue

A baya, an ji cewa rundunar ‘yan sandan jihar Benue ta kama mutum 10 da ake zargi da hannu a kisan shugaban Miyetti Allah, Alhaji Ardo Risku Muhammad.

An kama waɗanda ake zargin ne bayan cikakken binciken sirri da sintiri na musamman da aka ƙaddamar bayan kashe shugaban Fulani.

Kwamishinan ‘yan sandan Benue ya ce ana cigaba da bincike domin ganowa da kama sauran mutanen da ake zargi da kashe Ardo Risku.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.