Ministan Tinubu Ya Debo da Girma, Ya Ce ba Zai Bari Atiku Ya Lashe Zaben Shugaban Kasa ba
- Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya ce zai ci gaba da taka rawar gani a siyasar jihar Rivers gabanin zaben shugaban kasa na 2027
- Tsohon gwamnan ya ce ba zai zauna ya rike hannu bibbiyu ya bar Atiku Abubakar ya lashe zaben shugaban kasa ba
- Wike ya ce yawan zuwa jiharsa ta Rivers da yake yi ba yana nufin zai bari Abuja ya dawo gida ua zauna ba ne
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Port Harcourt, Rivers - Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya ce zai ci gaba da shiga harkokin siyasa a jihar Rivers gabanin zaben shugaban kasa na 2027.
Wike ya ce ba zai zauna ya rike hannu bibbiyu ya bar tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya lashe zaben shugaban kasar mai zuwa ba.

Source: UGC
Leadership ta ruwaito cewa Ministan ya bayyana hakan ne ranar Laraba, 2 ga watan Satumba, 2026 yayin ganawarsa da wasu zababbun manema labarai a Port Harcourt, jihar Rivers.

Kara karanta wannan
Tsohon gwamna ya fito ya fadi gaskiyar dalilin da ya sa yake neman mulkin Najeriya a 2027
Wike ya kuma yi watsi da rade-radin cewa yawan zuwansa jihar Rivers na nuna cewa yana shirin barin Abuja ya koma zama a jiharsa.
Dalilin Wike na yawan zuwa Rivers
Tsohon gwamnan jihar Rivers ya ce zuwansa jihar akai-akai na da alaka da bukatar ci gaba da tuntubar magoya bayansa tare da bibiyar abubuwan da ke faruwa a siyasance yayin da ake tunkarar zaben 2027.
Wike ya ce:
“Kuna so ne in zauna hannu bibbiyu Atiku Abubakar ya zo ya lashe zabe?”
Ya nace cewa yawan kasancewarsa a jihar Rivers ba yana nufin ya yi watsi da aikinsa na Ministan Abuja ko kuma yana shirin barin babban birnin tarayya ba ne.
Ya ce:
“Ba batun komawa zama ba ne, batun shi ne zuwa gida domin saduwa da jama’a, yin magana da su da kuma gudanar da abubuwan da kuka san kun iya yi sosai, ba tare da yin sakaci ba.
“Saboda haka, ba na dawo zama ba ne, ba na bukatar dawowa nan gida da zama, amma dole ne kuma in kasance tare da jama’ata domin kada kawai in zauna a Abuja ana gaya min cewa komai yana tafiya lafiya.”
Wike zai bibiyi harkokin siyasa da kansa
Wike ya ce ba zai dogara kacokan kan tabbacin da abokan siyasarsa ke ba shi cewa komai yana tafiya daidai a jihar Rivers ba, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Source: Facebook
Ya ce akwai bukatar ya rika zuwa jihar da kansa domin duba halin da ake ciki yayin da shirye-shiryen zaben 2027 ke kara kankama.
Ya ce:
“Ba na son in zauna a Abuja ’yan takara suna cewa, ‘Kada ka damu, komai yana tafiya lafiya.’ Dole ne in zo gida in gani da kaina cewa abubuwan suna tafiya yadda ya kamata. ‘Kun yi wannan? Yaya batun wancan?’”
Wike ya maida martani ga Peter Obi
A wani labarin, kun ji cewa Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya ce Shugaba Bola Tinubu ba shi da ikon tambayar yadda jihohi da ƙananan hukumomi ke kashe kudadensu.
Wike ya ce ya kamata Peter Obi ya tambayi yadda jihohi da ƙananan hukumomi ke amfani da kuɗaɗen da suke samu bayan cire tallafin mai
Asali: Legit.ng
