Aiki ja: An Bayyana Abin da Gwamnonin APC 31 Za Su Yi wa Tinubu a 2027

Aiki ja: An Bayyana Abin da Gwamnonin APC 31 Za Su Yi wa Tinubu a 2027

  • Gwamna Hope Uzodinma ya ce dukkan gwamnonin APC 31 sun amince su tabbatar da samun nasarar Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027
  • Gwamnonin sun kuma amince da kafa kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa, tare da ɗaukar alhakin tattara goyon baya a jihohinsu
  • Uzodinma ya ce taron ya kuma mayar da hankali kan rage tsadar rayuwa, farashin sufuri, samar da abinci da bunƙasa noma a Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Gwamnan Imo, Hope Uzodinma, ya bayyana abin da ake tsammani daga dukkan gwamnonin jam’iyyar APC 31 a Najeriya.

Uzodinma ya sun kuduri aniyar tabbatar da nasarar Shugaba Bola Tinubu a jihohinsu yayin babban zaɓen 2027.

Aikin da gwamnonin APC za su yi wa Tinubu a 2027
Gwamnonin APC suna ganawa da Bola Tinubu. Hoto: Bayo Onanuga.
Source: Twitter

Uzodinma ya bayyana hakan ne bayan ganawar da gwamnonin suka yi da Shugaba Tinubu, inda suka cimma matsaya kan goyon bayan ƙoƙarin shugaban na neman sake zaɓe, cewar Punch.

Kara karanta wannan

Sanata Yari ya bayyana mutanen da za su taka muhimmiyar rawa a tazarcen Tinubu

Ya ce gwamnonin sun haɗu kan manufar tallafa wa Tinubu, tare da tabbatar da cewa za su yi aiki domin samun nasarar jam’iyyar a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Uzodinma ya ce:

“Dukkan gwamnonin APC suna tare da Mai Girma Shugaban Ƙasa. Saboda haka, ana sa ran gwamnonin za su tabbatar da nasarar sa a jihohinsu.
“Babu ɗaya daga cikinmu da ba shi da cikakken ra’ayi iri ɗaya, amma mun haɗa kai. Muna goyon bayan sake zaɓen Mai Girma Shugaban Ƙasa. Muna kuma goyon bayan nasarar zaɓen.”

Gwamnonin sun amince da kwamitin yaƙin neman zaɓe

Uzodinma ya bayyana cewa Shugaba Tinubu ya sanar da gwamnonin game da kafa kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa yayin taron, kuma dukkaninsu sun amince da shirin.

Ya ce:

“Zaɓen da ke tafe, kafa kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa, wanda shugaban ya sanar da mu a hukumance, mun amince da shi gaba ɗaya. Abin da muka amince da shi da Mai Girma Shugaban Ƙasa shi ne cewa za a tabbatar da nasararsa.”

Wannan matsaya ta nuna cewa gwamnonin jam’iyyar APC na shirin haɗa kai wajen tunkarar zaɓen 2027, inda kowanne gwamna zai jagoranci ƙoƙarin neman goyon bayan Tinubu a jiharsa.

Kara karanta wannan

'Ya mana rana': Waɗanda Tinubu ya ba muƙamai sun shirya saka masa a 2027

Rage tsadar rayuwa abubuwan da aka tattauna

Baya ga batun siyasa da zaɓe, Uzodinma ya ce gwamnonin sun kuma tattauna matsalolin tattalin arziƙin da talakawan Najeriya ke fuskanta.

Ya bayyana cewa rage tsadar rayuwa na daga cikin muhimman abubuwan da suka fi jan hankalinsu, musamman yadda hauhawar farashin kayayyaki ke shafar al’umma.

Matsayar gwamnonin APC kan tikitin takara

An ji cewa Gwamnonin jam'iyyar APC sun zauna sun yi nazari kan zabukatar fitar da 'yan takara da jam'iyya mai mulki ta gudanar a makonnin da suka shige.

Bayan kammala nazari kan sakamakon zabukan, gwamnonin sun yanke shawarar ganawa da shugaban APC na kasa, Farfesa Nentwe Yilwatda.

Sun kuma kuduri aniyar hada kai domin magance matsalolin da ke fuskantar ƙasa da kuma tabbatar da cewa rayuwar ’yan Najeriya ta inganta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.