Wike Ya Rasa Babban Abokinsa a PDP, Ministan Ya Tuna Zaman da Suka Yi a Baya

Wike Ya Rasa Babban Abokinsa a PDP, Ministan Ya Tuna Zaman da Suka Yi a Baya

  • Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya bayyana kaduwarsa bayan samun labarin rasuwar jigon PDP, Daniel Osi Orbih
  • Orbih, Mataimakin Shugaban PDP na Kudu maso Kudu, ya rasu ranar Litinin, 31 ga Agusta 2026, ya bar mata, ’ya’ya da ’yan’uwa
  • Wike ya ce Orbih ya kasance babban mutum a siyasar Edo, yana mai mika ta’aziyyarsa ga iyalansa tare da addu’ar Ubangiji Ya jikansa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya yi alhini bayan bayan samun rasuwar wani jigon PDP a yau Talata 1 ga watan Agustan 2026.

An sanar da rasuwar Mataimakin Shugaban Jam’iyyar PDP na Kudu maso Kudu, Cif Daniel Osi Orbih bayan fama da jinya.

Jigon PDP a Najeriya ya mutu
Marigayi jigon jam'iyyar adawa ta PDP a jihar Edo, Daniel Osi Orbih Hoto: Nuru Shehu.
Source: Facebook

Hadimin Wike kan Harkokin Sadarwar Jama’a da Kafofin Sadarwa, Lere Olayinka ya ce ministan ya bayyana haka a cikin wata sanarwa a Facebook.

Kara karanta wannan

Yan adawan Najeriya sun yi rashi, wani babban jigo a PDP ya riga mu gidan gaskiya

An yi rashin jigon PDP a Najeriya

Cif Daniel Osi Orbih ya rasu ranar Litinin, 31 ga Agusta 2026, ya bar matarsa, Misis Florence Orbih, da ’ya’yansa Winifred Anwosiobor Orbih da Dr Mildred Omonemi Orbih.

Orbih ya kuma bar ’yan’uwansa maza da mata, da sauran ’yan uwa. Wike ya bayyana marigayin a matsayin “aboki na gaskiya,” yana mai cewa za a yi kewarsa sosai.

Rahotanni sun nuna cewa Orbih, yana da alaka ta kut-da-kut da Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Abuja, Nyesom Wike.

Iyalan marigayin sun roki ’yan uwa, abokai da masoya da su ci gaba da tunawa da su a cikin addu’o’insu yayin da suke cikin jimamin wannan babban rashi.

Sanarwar ta ce:

“A wannan lokaci mai matukar wahala, muna rokon ’yan uwa, abokai da masoya da su tuna da daukacin iyalan mu a cikin addu’o’insu yayin da muke jimamin wannan babban rashi."
Wike ya yi jimamin rasuwar Orbih
Marigayi jigon jam'iyyar adawa ta PDP, Daniel Osi Orbih da Nyesom Wike. Hoto: Nuru Shehu, Lere Olayinka.
Source: Facebook

Wike ya yi jimamin rasuwar jigon PDP

Kara karanta wannan

Shugaban jam’iyyar NDC a Arewa ya rabu da Obi, ya koma tallar takarar Atiku

Ministan ya bayyana rasuwar Orbih a matsayin “rashindaya daga cikin manyan jiga-jigai a fagen siyasar Edo,” yana mai cewa kowa zai yi kewarsa.

Wike ya ce:

“Na rasa aboki kuma amintaccen abokin siyasa. Dan Osi Orbih ya kasance duk abin da mutum zai iya bukata a wajen aboki da abokin siyasa.
“Amma ba za mu iya tambayar Allah ba; Shi Yake bayarwa, kuma Shi Yake karɓa.”
“A madadina, da iyalina da abokan siyasa, ina mika ta’aziyyata ga iyalan Cif M.C.K. Orbih bisa rasuwar Cif Dan Orbih, aboki nagari, babban ɗan siyasa, kuma mutum mai imani da Allah Maɗaukaki, “Ubangiji Ya jikansa, Ya gafarta masa.”

Wike ya fadi yadda Tinubu zai ci zabe

A wani labarin, kun ji cewa Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya bayyana yadda zaben Shugaba Bola Tinubu zai kasance a shekarar 2027.

ike ya ce rarrabuwar kawunan jam’iyyun adawa da yawan sauya sheka sun raunana su, don haka ba za su iya kalubalantar Tinubu yadda ya kamata ba.

inistan ya kuma umarci hukumomin Abuja su rusa gidajen da aka gina kan hanyoyin ruwa, yana mai cewa gwamnati na da cikakken ikon siyasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.