An Fadi Dalilin da Ya Sa Atiku bai Hallara Taron G 100 na Kifar da Tinubu ba

An Fadi Dalilin da Ya Sa Atiku bai Hallara Taron G 100 na Kifar da Tinubu ba

  • Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ta bayyana dalilin da ya sa ɗan takararta na shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, bai halarci taron G-100 na jam’iyyun adawa da aka gudanar a Abuja ba.
  • Jam’iyyar ta ce taron ya fi mayar da hankali ne kan tattaunawa tsakanin jam’iyyun siyasa da neman hanyoyin haɗin gwiwa, ba tattaunawar ’yan takarar shugaban ƙasa ba.
  • Sakataren yaɗa labarai na ADC na ƙasa, Bolaji Abdullahi, ya ce rashin halartar Atiku bai shafi wakilcin jam’iyyar ba, domin ADC ta samu cikakken wakilci a taron.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abuja – Jam’iyyar ADC ta yi bayani kan dalilin da ya sa ɗan takararta na shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, bai halarci taron G-100 na jam’iyyun adawa da aka gudanar a Abuja ranar Litinin ba.

Kara karanta wannan

2027: An samu matsala a taron hadakar jam'iyun adawa domin kifar da Tinubu

Sakataren yaɗa labarai na ADC na ƙasa, Bolaji Abdullahi, ya bayyana hakan ne ranar Talata yayin wata hira da manema labarai a Abuja.

Atiku Abubakar a wani taro
Dan takarar shugaban kasa na ADC, Atiku Abubakar. Hoto: Paul O. Ibe
Source: Facebook

Me ya sa Atiku bai je taron ba?

Punch ta wallafa cewa Bolaji Abdullahi ya ce taron G-100 ya fi mayar da hankali kan tattaunawa tsakanin jam’iyyun siyasa da kuma gano damar haɗin gwiwa, maimakon tattaunawa tsakanin ’yan takarar shugaban ƙasa.

Ya ce saboda haka, rashin halartar Atiku bai kamata ya zama babban batu ba, domin jam’iyyar ta samu cikakken wakilci a taron.

“Yadda muka fahimci taron, ya fi kasancewa tattaunawa tsakanin jam’iyyun siyasa ne, ba tsakanin ’yan takara ba.
“Ya fi mayar da hankali kan gano damar haɗin gwiwa tsakanin jam’iyyun siyasa. Saboda haka, rashin halartar Alhaji Atiku Abubakar ba shi da wani tasiri,”

In ji shi.

ADC ta ce ta samu cikakken wakilci

Tribune ta wallafa cewa Bolaji Abdullahi ya bayyana cewa shi da kansa ya halarci taron tare da mataimakan shugabannin jam’iyyar guda huɗu.

Ya ce kasancewar wakilai da dama daga ADC ya tabbatar da cewa jam’iyyar ta shiga cikin tattaunawar G-100 yadda ya kamata.

Kara karanta wannan

'Yan adawa sun fitar da tsarin kafa gwamnati a 2027 da kifar da Tinubu

“Ni na je, jam’iyyar ta samu cikakken wakilci, muna da mataimakan shugabanni kusan huɗu a taron G-100. Saboda haka, ADC ta samu cikakken wakilci kuma mun shiga cikin tsarin,”

In ji shi.

Taron dai ya gudana ne a ranar Litinin a Shehu Musa Yar’Adua Centre da ke Abuja, inda wakilan jam’iyyun adawa shida suka tattauna kan yiwuwar haɗin gwiwa gabanin zaɓen 2027.

Bolaji Abdullahi a wajen taro
Kakakin ADC, Bolaji Abdullahi. Hoto: Malam Bolaji Abdullahi
Source: Facebook

An kafa kwamitocin 'yan adawa

A wani labarin, mun ruwaito cewa jam’iyyun adawa sun kafa kwamitoci biyar na musamman domin samar da tsarin da zai taimaka wajen samun ɗan takarar shugaban ƙasa na bai ɗaya a zaɓen 2027.

Kwamitocin sun haɗa da na Yarjejeniyar Ƙasa domin Farfaɗo da Dimokuraɗiyya, Yarjejeniyar Gwamnatin Sauyi ta Wa’adi Guda, Shirin Gyaran Ƙasa, Tsarin Haɗin Kan Jam’iyyun Adawa da Taswirar Samun Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa na Bai Ɗaya.

An bai wa kwamitocin kwanaki 30 domin gabatar da rahotanninsu, wanda za a yi amfani da shi wajen shirya taron tuntuba na biyu na jam’iyyun adawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng