Atiku Ya Sake Yi Wa 'Yan Najeriya Babban Alkawari idan Ya Zama Shugaban Kasa
- Atiku Abubakar ya ce zai tabbatar da biyan kuɗaɗen ƙananan hukumomi kai tsaye idan ya zama shugaban Najeriya
- Dan takarar shugaban kasar na jam'iyyar ADC ya ce gwamnatinsa za ta mutunta hukuncin kotu tare da kare cin gashin kan ƙananan hukumomin Najeriya
- Atiku ya zargi gwamnatin Tinubu da jinkirta aiwatar da hukuncin Kotun Ƙoli kan ‘yancin kuɗaɗen ƙananan hukumomi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), Atiku Abubakar, ya yi alkawari kan kananan hukumomi.
Atiku ya yi alkawarin tabbatar da cewa kuɗaɗen da aka ware wa ƙananan hukumomin Najeriya suna isa gare su kai tsaye idan ya lashe zaɓen 2027.

Source: Facebook
Atiku ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Kenneth Okonkwo, ya sanya wa hannu tare da wallafawa a shafinsa na X a ranar Talata, 1 ga watan Satumban 2026.
Atiku ya yi alkawarin kan ƙananan hukumomi
Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya ce idan ya zama shugaban ƙasa, gwamnatinsa za ta mutunta tsarin mulki tare da tabbatar da ‘yancin cin gashin kai na dukkan matakan gwamnati.
Ya ce wannan zai haɗa da ƙananan hukumomi, waɗanda ya ce suna da muhimmiyar rawa wajen samar da ci gaba da ayyukan gwamnati ga jama’a a matakin ƙasa.
Atiku ya yi nuni da hukuncin Kotun Ƙoli na watan Yulin 2024 kan ‘yancin kuɗaɗen ƙananan hukumomi.
Ya zargi gwamnatin Shugaba Bola Tinubu da kasa aiwatar da hukuncin kotun, yana mai cewa hakan na hana ƙananan hukumomi samun cikakken iko kan kuɗaɗen da aka ware musu.
‘Kuɗaɗen gwamnati su isa ga jama’a’
Atiku ya ce gwamnatinsa za ta mutunta hukuncin kotu, ta kare cin gashin kan ƙananan hukumomi, sannan ta tabbatar da cewa kuɗaɗen jama’a sun isa ga waɗanda aka ware su domin amfanarwa.

Kara karanta wannan
Shirin dawo da tallafin man fetur ya firgita shugaban APC, ya fadi illar shirin Atiku
Dan takarar shugaban kasar ya ce hakan zai taimaka wajen dawo da ingantaccen tsarin tarayya a Najeriya.
A cewarsa, biyan kuɗaɗen ƙananan hukumomi kai tsaye zai taimaka wajen kawo ayyukan ci gaba kusa da jama’a, rage talauci da kuma ƙara wa ƙananan hukumomi ƙarfin gudanar da ayyukansu.
Atiku ya zargi Tinubu da siyasa
Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya kuma zargi gwamnatin Tinubu da yin la’akari da siyasa wajen aiwatar da hukuncin Kotun Ƙoli.
Ya yi iƙirarin cewa gwamnoni na ci gaba da samun iko kan kuɗaɗen ƙananan hukumomi domin samun goyon bayansu ga sake zaɓen Shugaba Tinubu a 2027.
Atiku ya ce bai kamata a bar irin wannan tsari ya ci gaba da gudana ba.
“Wannan ba ita ce Najeriya da ya kamata mu amince da ita ba,” in ji tsohon mataimakin shugaban ƙasar.
An ware N10.48tn ga ƙananan hukumomi
Rahotanni sun nuna cewa shekaru biyu bayan Kotun Ƙoli ta bayar da umarnin biyan kuɗaɗen ƙananan hukumomi kai tsaye, har yanzu ba a samu cikakken aiwatar da hukuncin ba.
A cewar rahoton jaridar The Punch an ware jimillar N10.48tn ga ƙananan hukumomi cikin lokacin da ake magana a kai.
Atiku ya ce tabbatar da cikakken ‘yancin kuɗaɗen ƙananan hukumomi zai ba su damar gudanar da ayyukan ci gaba, da kuma taimakawa wajen yaƙi da laifuka da ta’addanci a matakin ƙasa.

Source: Twitter
Dalilin da ya sa Atiku bai je taron G-100 ba
A wani labarin kuma, kun ji cewa jam’iyyar ADC ta yi bayani kan dalilin da ya sa ɗan takararta na shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, bai halarci taron G-100.
Bolaji Abdullahi ya ce taron G-100 ya fi mayar da hankali kan tattaunawa tsakanin jam’iyyun siyasa da kuma gano damar haɗin gwiwa, maimakon tattaunawa tsakanin ’yan takarar shugaban ƙasa.
Asali: Legit.ng

