"Na San Komai," Tsohon Gwamna Ya 'Tsoratar' da Yan Najeriya kan Shirin Dawo da Tallafin Fetur

"Na San Komai," Tsohon Gwamna Ya 'Tsoratar' da Yan Najeriya kan Shirin Dawo da Tallafin Fetur

  • Tsohon gwamnan Bauchi, Isa Yuguda, ya gargadi ’yan Najeriya su yi taka-tsantsan tare da bincikar alkawurran ’yan siyasa gabanin zaɓen 2027
  • Yuguda ya soki shirin Atiku Abubakar na dawo da tallafin man fetur, yana mai cewa tsarin ya kasance babban nauyi ga tattalin arzikin Najeriya
  • Tsohon ministan sufurin jiragen sama ya ce dawo da tallafin man fetur na iya mayar da ƙasar baya tare da rage kuɗaɗen shiga

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abuja - Tsohon gwamnan Bauchi, Mallam Isa Yuguda, ya shawarci ’yan Najeriya su yi nazari sosai tare da tantance manufofin tattalin arziki da ’yan siyasa ke gabatarwa yayin da ake tunkarar zaɓen 2027.

Yuguda ya yi wannan gargaɗin ne ranar Talata a jawabinsa na buɗe taron tattaunawa kan manufofi da kungiyar APC Professional Forum ta shirya.

Isa Yuguda.
Tsohon gwamnan jihar Bauchi, Mallak Isa Yuguda Hoto: Yuguda Associates
Source: Facebook

Tribune Nigeria ta rahoto cewa tsohon ministan sufurin jiragen sama ya soki sanarwar ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC, Atiku Abubakar, na cewa zai dawo da tsarin tallafin man fetur da aka cire.

Kara karanta wannan

Atiku ya ragargaji Tinubu kan tafiya hutu Turai 'Najeriya na ci da wuta'

Yuguda ya hango illar alkawarin Atiku

Yuguda, wanda ya kasance shugaban kwamitin binciken tallafin man fetur na shekarar 2009, ya tuna cewa tsarin tallafin ya kasance babban nauyi ga kuɗaɗen gwamnati.

Ya ce:

“A matsayina na shugaban kwamitin binciken tallafin man fetur na 2009, na jagoranci kwamitin da ya binciki tsarin tallafin, inda muka gano manyan kura-kurai, ayyukan damfara da kuma sulalewar kuɗaɗe da suka zame wa Najeriya babban nauyi.
“Tsarin tallafin ya zama mara inganci, yana cinye dimbin kuɗaɗen gwamnati da za a iya saka su wajen ilimi, tsaro, noma, kiwon lafiya, ababen more rayuwa da sauran ɓangarorin da ke samar da ci gaba.
“Saboda haka, cire tallafin wani gyara ne mai wahala amma ya zama dole, wanda aka yi niyyar karkatar da albarkatun ƙasa zuwa ci gaba na dogon lokaci."

Tsohon gwamnan ya ce Shugaba Tinubu ya nuna jarumta wajen aiwatar da wani gyara da gwamnatocin baya suka amince cewa ya zama dole, amma suka kasa aiwatar da shi gaba ɗaya.

Kara karanta wannan

Shirin dawo da tallafin man fetur ya firgita shugaban APC, ya fadi illar shirin Atiku

Yuguda ya ja hankalin yan Najeriya

Da yake ba yan Najeriya shawara, Isa Yuguda ya ce:

“Yayin da muke tunkarar zaɓen 2027, ya kamata ’yan Najeriya su yi taka-tsantsan wajen tantance alkawuran ’yan siyasa, musamman waɗanda suka shafi dawo da tallafin man fetur.
“Shawarar Atiku Abubakar ta dawo da tallafin na iya zama abin sha’awa ga ’yan ƙasa da ke neman sauƙin rayuwa nan take, amma ya kamata a auna ta bisa abin da ƙasar ta taɓa fuskanta.
“Kowane ɗan Najeriya yana da ’yancin dimokuraɗiyya na gabatar da wasu manufofi daban, amma ya kamata a jagoranci zaɓin tattalin arziki da hujjoji, tarihin baya, ɗorewa da kuma muradun ƙasar na dogon lokaci."
Atiku.
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar a taron kaddamar da hadakar yan adawa a ADC Hoto: @atiku
Source: Facebook

Sanata Yari ya soki shirin Atiku

Kun ji cewa Darakta Janar na kwamitin yakin neman zaben Bola Tinubu a 2027, Sanata Abdul'aziz Yari ya maida martani ga Atiku Abubakar kan dawo da tallafin mai.

Sanata Abdulaziz Yari ya ce duk wanda ya yi alkawarin dawo da tallafin man fetur yana yaudarar ’yan Najeriya ne kurum amma hakan ba zai yiwu ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262