Dangote Ya Bayyana Alherin da Yake Jiran Wadanda Suka Saye Hannun Jari a Matatarsa

Dangote Ya Bayyana Alherin da Yake Jiran Wadanda Suka Saye Hannun Jari a Matatarsa

  • Dangote ya kwantar wa masu zuba jari hankali cewa sauyin farashin danyen mai ba zai yin ta'annati ga ribarsa ba
  • Mataimakin shugaban kamfanin yace saida kayayyaki zuwa kasashen waje yana samar da dimbin kudi gare su
  • Kamfanin Dangote ya fara siyar da hannun jarin ne bayan matatarsa ta riga ta fara aiki gadan-gadan a shekarar bara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Lagos - Mataimakin shugaban kamfanonin Dangote Industries Limited, Edwin Devakumar ya yi magana game da hannun jarin da ke kasuwa.

Edwin Devakumar ya tabbatar wa wadanda suka saye hannun jarin matatarsu cewa ana sa ran za su samu riba nan da wani dogon lokaci.

Dangote IPO
Aliko Dangote da sauran manyan kamfanin wajen bude saida hannun jari Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Karfin matatar man Dangote

An rahoto Mista Edwin Devakumar a jaridar Leadership yana bayanin karfin matarsu da kuma irin matsayinsu a harkar makamashi a Afrika.

Kara karanta wannan

Matsayar addinin Musulunci kan sayen hannun jarin matatar Dangote

Shugaban kamfanin ya ce matatar Dangote ta fara cin riba kuma dama an kafa ta ne saboda Najeriya ta daina shigo da mai daga ketare.

Haka zalika ana so matatar ta samar da ayyukan yi a Najeriya kuma ta samar da kudin waje.

Hannun jarin Dangote zai kawo kudi

Saboda haka, Devakumar ya ce wadanda suka saye hannun jari a matatar mansu sun samu kamfani mai karfi wanda zai iya kawo kudi.

Kamfanin ya nanata ba saboda kawai a samu kudi aka saida hannun jarin ba, ana so miliyoyin ‘yan Najeriya da Afrika su zo a ci riba da su.

Za a yi amfani da kudin da aka samu wajen fadada matatar da kuma kara kutsawa cikin harkar kasuwancin mai a wasu kasashen Afrika.

Kamfanin yana da tsarin kasuwanci da ya game abubuwa da-dama, kuma yana amfani da fasahar zamani ga shirin sufuri mai fadi da babu a Afrika.

Kara karanta wannan

An fito da bayanin yadda duk wanda ya sayi hannun jarin matatar Dangote zai samu alheri

Matatar da ke Legas tana samar da mai a Najeriya, kasashen Afrika da fadin duniya.

Wannan matata tana iya tace fetur, dizil, man jirgin sama, LPG da ake amfani da shi wajen girki da kuma takin zamani da sauransu.

Idan duk aka yi la’akari da wadannan, Edwin Devakumar ya ce alheri ne yake jiran wadanda suka mallaki hannun jari a wajensu.

Kamfanin ya ce yana bin dokokin aiki na duniya tare da tabbatar da gaskiya, taka-tsan-tsan wadanda suke jawo darajar hannun jari.

Nan gaba hannun jarin zai kara daraja

The Sun ta rahoto shi ya ce da zarar an bayyana wadanda suka samu damar mallakar hannun jari, darajarsa za ta karu sosai a kasuwa.

Ana sa ran kudin da yake shigo wa matatar da kuma man da yake fitar wa zuwa kasashen waje zai sa ya cigaba da jawo masa alheri.

Baya ga juya masu kudi da za a yi, ya ce masu hannun jarin sun kafa tarihi a fadin Afrika.

Kara karanta wannan

Yadda Dangote ya yi shekara 36 yana zaune a gida 1 ba tare da sauya shi ba

Dangote IPO
Lokacin bikin bude saida hannun jarin matatar Dangote Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Hannun jarin Dangote ya yi kasuwa

An rahoto cewa an bude saida hannun jarin Dangote a ranar Litinin da ta wuce kuma an rahoto matatar ta samu $7m a kusan awa guda.

Sayar da hannun jarin na zuwa ne da nufin tara jimillar kudi dala biliyan 1.6 domin fadaɗa aikin matatar, ya nunka karfinsa nan da 2028.

Wannan shi ne shirin sayar da hannun jari mafi girma da aka taba yi a kasuwar hannun jari ta nahiyar Afirka kamar yadda aka ji labari a baya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng