Yunkurin Hada Irinsu Atiku da Obi Ya Samu Cigaba, an Samu Dan Takarar da Ya Shirya Janyewa

Yunkurin Hada Irinsu Atiku da Obi Ya Samu Cigaba, an Samu Dan Takarar da Ya Shirya Janyewa

Donald Duke ya bayyana cewa zai iya janye takararsa idan ‘yan adawa suka cimma matsaya kan ɗan takara guda da zai iya samun nasara a 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Tsohon gwamnan na Cross River ya ce rashin haɗin kan ‘yan adawa na iya bai wa Bola Tinubu damar lashe zaɓen 2027

Duke ya amince cewa Tinubu ƙwararren ɗan siyasa ne, amma ya soki salon mulkinsa, yana mai cewa ya yi rauni wajen tafiyar da gwamnati

FCT, Abuja – Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Peoples Redemption Party (PRP), Donald Duke, ya bayyana matsayarsa kan janyewa daga takara.

Donald Duke ya bayyana cewa a shirye yake ya janye takararsa domin mara wa ɗan takarar haɗin gwiwar ‘yan adawa baya a zaɓen 2027.

Donald Duke ya shirya janyewa
Tsohon gwamnan Cross River, Donald Duke Hoto: Donald Duke
Source: Facebook

Duke, wanda tsohon gwamnan Cross River ne, ya bayyana hakan ne yayin wata hira da Channels Tv a ranar Litinin, 31 ga watan Agustan 2026.

Kara karanta wannan

Atiku ko Obi: Yan adawa sun fara ɗaukar matsayan da za ta iya kayar da Tinubu a zaben 2027

Ya ce abin da ya kamata ‘yan adawa su fi mayar da hankali a kai shi ne zaɓen mutumin da ya fi dacewa da cimma manufar haɗakar da suka kafa.

Duke ya ce zai iya janye takararsa

Da aka tambaye shi ko zai iya janye takararsa domin wani ɗan takarar shugaban ƙasa, Duke ya amsa da cewa babu shakka zai iya yin hakan.

Ya ce idan ‘yan adawa suka samu manufa guda, abin da zai biyo baya shi ne tantance wanda ya fi cancanta ya jagorance su domin cimma burinsu.

Duke ya kwatanta siyasa da wasanni, inda ya ce duk da cewa dubban mutane na iya kallon wasa su ɗauka sun fi kowa sanin yadda ake buga shi, mutane kaɗan ne ke cikin filin da ke da alhakin yanke hukunci.

Ya ce yana son kasancewa cikin masu fafutukar ganin an samar da wata murya mai hankali a tsakanin ‘yan siyasar da ke fafutukar ganin an samu sauyi.

Duke ya yi gargadi ‘yan adawa

Tsohon gwamnan ya yi gargadin cewa idan ‘yan adawa ba su haɗa kansu ba kafin zaɓen 2027, Shugaba Bola Tinubu na iya samun damar sake lashe zaɓen.

Kara karanta wannan

Tsohon gwamnan da ake zargi da shirya wa Tinubu juyin mulki ya fita a APC

Duke ya ce tarihin zaɓubbukan Najeriya ya nuna cewa bai kamata ‘yan adawa su jira sai an kammala zaɓe sannan su fara zargin an yi musu magudi ba.

A cewarsa, ya kamata ‘yan adawa su yi tunanin matsalolin da ka iya tasowa tun kafin ranar zaɓe, tare da ɗaukar matakan da za su rage tasirinsu.

Ya ce haɗin kai shi ne hanya mafi dacewa da ‘yan adawa za su bi idan suna son samun nasara a kan jam’iyyar APC mai mulki.

Ya soki salon mulkin Tinubu

Duke ya amince cewa Tinubu ƙwararren ɗan siyasa ne kuma yana da ƙwarewar gina tasiri a siyasa.

Sai dai ya ce babban matsalarsa da Shugaban ƙasar ba siyasa ba ce, illa salon mulkin da yake gudanarwa.

Ya ce a ganinsa, Tinubu ya yi rauni wajen shugabanci idan aka yi la’akari da yadda al’amuran ƙasar suka kasance cikin shekaru uku da suka gabata.

Duke ya bayyana cewa bai kamata Tinubu ya samu damar sake yin wa’adin mulki ba, yana mai cewa ƙasar na fuskantar matsalolin tattalin arziki da talauci sakamakon abin da ya kira gazawar shugabanci.

Kara karanta wannan

Rikicin ADC: An gargadi Atiku kan tsoma baki sha'anin jam'iyyar a Adamawa

Ya yi gargadin cewa ci gaba da barin talauci yana ƙaruwa a Najeriya zai iya ƙara jefa ƙasar cikin mawuyacin hali.

Yan adawa na son kifar da Shugaba Bola Tinubu
Shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu Hoto: Bayo Onanuga
Source: Twitter

Shugabannin 'yan adawa sun yi taro

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugabannin manyan jam’iyyun adawa shida a Najeriya sun taru a Abuja domin ƙulla tsarin haɗin gwiwa da nufin kayar da Shugaba Bola Tinubu a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Sai dai ’yan takarar shugaban ƙasa na ADC, Atiku Abubakar; Peter Obi na NDC; da Seyi Makinde na Oyo da ke APM, ba su halarci taron ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng