Tsohon Gwamnan da ake Zargi da Shirya wa Tinubu Juyin Mulki Ya Fita a APC

Tsohon Gwamnan da ake Zargi da Shirya wa Tinubu Juyin Mulki Ya Fita a APC

  • Rahotanni sun nuna cewa tsohon gwamnan jihar Bayelsa, Timipre Sylva, ya sanar da yin murabus daga jam’iyyar APC mai mmulki a Najeriya
  • Sylva, wanda ya kasance ɗaya daga cikin waɗanda suka kafa APC, ya ce ya ɗauki matakin ne bayan tuntubar iyalansa da abokan hulɗa
  • Murabus ɗin tsohon gwamnan ya zo ne yayin da ake zarginsa da hannu a wani shirin juyin mulki da kuma wani zargin karkatar da kuɗi sama da $14.8m

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Tsohon gwamnan jihar Bayelsa kuma jigo a jam’iyyar APC, Timipre Sylva, ya sanar da yin murabus daga jam’iyyar.

Sylva ya miƙa takardar murabus ɗinsa ga shugaban APC a ƙaramar hukumar Brass ta jihar Bayelsa, inda ya ce murabus ɗin zai fara aiki nan take.

Kara karanta wannan

"Gwamnatin mu ce"; Kwamishina ya yi barazanar guntile 'yan yatsun masu adawa da APC

Timipre Sylva da ya fita daga APC
Tsohon gwamnan Bayelsa, Timipre Sylva. Hoto: Timipre Sylva
Source: Facebook

The Cable ta ruwaito cewa tsohon gwamnan ya ce ya yanke shawarar barin jam’iyyar ne bayan ya tuntubi iyalansa, abokan hulɗa, abokan aiki da masu goyon bayansa.

Me ya sa Sylva ya bar APC

A cikin takardar murabus ɗin, Sylva ya bayyana cewa yana matuƙar baƙin cikin yadda aka sauya akidojin da suka kafa APC tun farko.

Ya ce yana cikin waɗanda suka kafa jam’iyyar tare da sauran ’yan Najeriya masu kishin ƙasa, inda suka bayar da lokaci da kuɗinsu wajen gina jam’iyyar.

Sylva ya ce ba zai iya ci gaba da kasancewa a jam’iyyar da shugabanninta ke ganin cewa “komai ya halatta a siyasa” ba.

Punch ta wallafa cewa ya ƙara da cewa:

“Abin takaici ne matuka ganin yadda aka murƙushe tare da sauya akidojin da muka yi imani da su gaba ɗaya.”

Sylva ya soki gwamnatin APC

Sylva ya bayyana gwamnatin APC ta yanzu a matsayin wadda ta ba yawancin ’yan Najeriya kunya, yana mai cewa bai ga wata sahihiyar alama ta sake farfaɗo da jam’iyyar ko gwamnati ba.

Kara karanta wannan

Kirista ya lashe gasar Kur'ani, ya samu kyautar kujerar Umrah

Ya ce ba zai iya ci gaba da kasancewa cikin abin da ya kira jam’iyya ko gwamnati da ta kasa cika manufofin da aka kafa ta a kansu ba.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Kashim Shettima
Shugaban kasa Bola Tinubu da mataimakinsa a wajen taron APC. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook
“Gwamnatin da aka kafa a ƙarƙashin tutar APC da muka taɓa ƙauna ta ba yawancin ’yan Najeriya kunya. Ban ga wata sahihiyar ƙoƙari ko wata dama ta sake farfaɗo da ita ba,”

In ji shi.

Maganar APC kan tallafin mai

A wani labarin, mun ruwaito cewa shugaban APC Farfesa Nentawe Yilwatda, ya yi gargaɗin cewa dawo da tallafin man fetur na iya lalata nasarorin da aka samu daga sauye-sauyen tattalin arziki na yanzu.

Yilwatda ya ce komawa tsarin tallafin man fetur na baya na iya shafar albashin ma’aikata, ilimi, kiwon lafiya, abubuwan more rayuwa da kuma ƙarfin kuɗin gwamnatocin jihohi.

Shugaban APC ya bayyana hakan ne a Abuja yayin da yake karɓar wata tawaga ta masu ruwa da tsaki kan tattalin arziki, inda ya soki matakin Atiku Abubakar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng