Shugaban APC Ya Firgita kan Dawo da Tallafin Fetur, Ya Fadi Illar Shirin Atiku

Shugaban APC Ya Firgita kan Dawo da Tallafin Fetur, Ya Fadi Illar Shirin Atiku

  • ShaFarfesa Nentawe Yilwatda ya yi magana kan illolin da ke tattare da shirin sake dawo da tallafin man fetur
  • Shugaban na APC ya yi gargadin cewa ƙarancin kuɗaɗen gwamnati na iya shafar biyan albashi, fansho, ilimi, lafiya da sauran ayyuka
  • Yilwatda ya ce ya kamata a tantance tasirin tallafin kafin a mayar da shi domin tabbatar da cewa gwamnati za ta iya biyan sabon mafi ƙarancin albashi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Shugaban jam’iyyar APC, Nentawe Yilwatda, ya gargadi cewa shirin tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, na dawo da tallafin man fetur na iya dawo da dogayen layukan mai.

Yilwatda ya kuma ce hakan na iya raunana ƙarfin gwamnatoci wajen biyan sabon mafi ƙarancin albashi da kuma gudanar da wasu muhimman ayyuka.

Nentawe ya soki shirin Atiku na dawo da tallafi
Farfesa Nentawe Yilwatda na jawabi a wajen taro Hoto: Senator Uba Sani
Source: Facebook

Shugaban APC ya bayyana hakan ne a Abuja yayin da yake karɓar wata tawaga ta masu ruwa da tsaki kan tattalin arziki da ta kai masa ziyara domin tattauna halin tattalin arzikin Najeriya da sauye-sauyen da ake yi, cewar rahoton jaridar TheCable.

Kara karanta wannan

Daraktan yakin neman zaben Tinubu, Abdulaziz Yari ya yi magana kan dawo da tallafin fetur

Atiku na son dawo da tallafin mai

Atiku, wanda ke neman shugabancin Najeriya a ƙarƙashin African Democratic Congress (ADC), ya bayyana cewa zai dawo da tallafin man fetur idan aka zaɓe shi shugaban ƙasa a 2027.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya kuma zargi gwamnatin tarayya da kasa bayyana yadda aka yi amfani da kuɗaɗen da aka samu bayan cire tallafin.

Sai dai Yilwatda ya ce ya kamata ‘yan Najeriya su duba abin da zai biyo bayan rage farashin man fetur, musamman yadda hakan zai shafi kuɗaɗen shiga da kashe-kashen gwamnati.

“Wa zai biya kuɗin tallafin?”

Yilwatda ya ce duk da cewa tallafi na iya sa farashin man fetur ya yi sauƙi, ya kamata a tambayi wanda zai ɗauki nauyin kuɗin tallafin da kuma ayyukan da za a iya rasa kuɗinsu.

“Tallafi na iya zama abin jan hankali saboda yana alkawarin man fetur mai rahusa, amma ya kamata ‘yan Najeriya su tambayi babbar tambaya: wa zai biya kuɗin tallafin?” in ji shi.

Kara karanta wannan

Atiku zai rattaba hannu kan dawo da tallafin man fetur da yan Najeriya

Ya ce bai kamata a auna wata manufar tattalin arziki bisa fa’idarta a tashar mai kawai ba, domin tana iya shafar kuɗaɗen gwamnati, albashi, fansho, ilimi, lafiya da ababen more rayuwa.

Ya danganta tallafi da sabon mafi ƙarancin albashi

Shugaban APC ya ce cire tallafin man fetur ya ƙara yawan kuɗaɗen da ake ware wa jihohi, lamarin da ya taimaka wajen inganta harkokin kuɗin wasu gwamnatocin jihohi.

Ya ce a baya wasu jihohi sun kasance suna fama da matsalar biyan albashi da fansho, yayin da wasu ke biyan wani ɓangare kawai.

Yilwatda ya ce dawo da tallafin zai iya sake jefa gwamnati cikin matsin tattalin arziki, musamman wajen ci gaba da biyan sabon mafi ƙarancin albashi.

Ya ce ƙara albashi kaɗai bai isa ba, domin gwamnati na buƙatar samar da yanayin tattalin arziki da zai ba ta damar ci gaba da biyan albashi ba tare da rage kuɗaɗen ilimi, lafiya da ababen more rayuwa ba.

An kuma yi gargadi kan ilimi

Yilwatda ya kuma bayyana damuwa kan yadda dawo da tallafin zai iya shafar kuɗaɗen da gwamnati ke warewa fannin ilimi.

Kara karanta wannan

Tirkashi: APC ta dauka da zafi bayan Atiku ya yi wasu kalamai

Ya tuna da yadda aka samu dogon tsaiko a ayyukan jami’o’in Najeriya a ƙarƙashin gwamnatin da ta gabata, yana mai cewa bai kamata a sake aiwatar da manufofin da za su rage ƙarfin gwamnati wajen tallafa wa ilimi ba.

Ya ce idan aka koma tsarin tallafin da ba zai iya ɗorewa ta fuskar kuɗi ba, illarsa za ta wuce farashin man fetur.

A cewarsa, idan kuɗaɗen shiga gwamnati suka ragu, muhimman fannoni da suka shafi jin daɗin jama’a da makomar ƙasar na iya kasancewa cikin haɗari.

Nentawe ya soki shirin dawo da tallafin fetur
Farfesa Nentawe Yilwatda na jawabi a wajen taro Hoto: Senator Uba Sani
Source: Facebook

Jigo a APC ya goyi bayan Atiku kan tallafi

A wani labarin kuma, kun ji cewa jigo a APC a jihar Neja, Jonathan Vatsa, ya goyi bayan Atiku Abubakar, kan batun tallafin mai.

Jonathan Vatsa, wanda tsohon Kwamishinan Yada Labarai, Al’adu da Yawon Bude Ido na Jihar Neja, ya ce manufar cire tallafin ta jefa ’yan Najeriya cikin wahala.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng