Atiku Zai Bambanta da Tinubu, Ya Yi Albishir ga Matasa da Ya Gana da Yan N Power
- Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya yi alkawarin samar da shirin tallafin biliyoyin dala ga ’yan kasuwa
- Atiku ya ce matasan Najeriya na buƙatar gwamnati da za ta samar musu da damammaki, maimakon ba da tallafi marar amfani
- Ya bayyana cewa shirinsa zai mayar da matasa daga dogaro da tallafi zuwa kasuwanci, daga rashin aikin yi zuwa samar da ayyukan yi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya yi alkawarin ƙaddamar da shirin samar da dala biliyan 100 ga ’yan kasuwa idan aka zaɓe shi shugaban ƙasa.
Atiku ya ce matsalar tsadar rayuwa ta rage ƙarfin sayen kayayyaki na miliyoyin ’yan Najeriya, tare da raunana ƙananan sana’o’i da kasuwanci.

Source: Twitter
Atiku, wanda ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X ranar Asabar, ya ce matasan Najeriya na buƙatar gwamnati mai samar da damammaki.

Kara karanta wannan
Gwamnati ta hango matsala, Ribadu ya yi gargadi kan barazanar tsaro a wasu wurare
Gatan da Atiku zai yi ga matasa
Ya ce gwamnati ba za ta koya wa matasa yadda za su rayu cikin wahala ba, sai dai ta samar musu da damar bunƙasa da samun wadata.
Wazirin Adamawa ya ƙara da cewa halin da ake ciki ya sa samun ayyukan yi, jari da damar samun ’yancin kai ta fuskar tattalin arziki ya ƙara zama da wahala ga matasa.
Atiku ya ce idan aka zaɓe shi, gwamnatinsa za ta mayar da hankali wajen dawo da ƙarfin sayen ’yan Najeriya da rage tsadar rayuwa.
Haka kuma, ya ce za ta faɗaɗa damar tattalin arziki ga matasa ta hanyar shirye-shiryen samar da kuɗaɗen jari da tallafawa ’yan kasuwa.
“Manufarmu a bayyane take: mu sauya matasan Najeriya daga dogaro zuwa ƙirƙirar sana’o’i, daga rashin aikin yi zuwa haɓaka aiki da ƙwarewa, sannan daga tallafin gaggawa zuwa wadata,”.
- Atiku Abubakar

Source: UGC
Shirin Atiku kan makomar matasan Najeriya
Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya ce manufar shirin ita ce sauya matasa daga dogaro da tallafi zuwa dogaro da sana’o’i da kasuwanci.
Ya kuma ce za a mayar da matasa daga rashin aikin yi zuwa samar da ayyukan yi da ƙara bayar da gudunmawa wajen bunƙasar tattalin arziki.
Ta kara da cewa:
“Alƙawarina shi ne in sauya wannan yanayi. Za mu dawo da ƙarfin sayayya, rage tsadar rayuwa tare da faɗaɗa damammaki ga matasan Najeriya ta hanyar shirin samar da dala biliyan 100 domin tallafa wa sababbin kamfanoni da ’yan kasuwa."
Atiku ya bayyana cewa ya yi wannan alkawarin ne yayin da wata tawaga ta ƙasa baki ɗaya daga cikin waɗanda suka amfana da shirin N-Power ta kai masa ziyara.
Tawagar ta ziyarci Atiku ne domin bayyana goyon bayanta ga takararsa ta neman zama shugaban ƙasar Najeriya a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
'Atiku ne zai kayar da Tinubu' - Kwamred Murtala
A wani labarin, mun ba ku rahoton cewa matashi ya bayyana zaɓen Alhaji Atiku Abubakar a matsayin jihadi ga ƴan Najeriya.
Wani hadimin dan takarar gwamnan Accord a Kano, Mukhtar Gashash ya ce Atiku zai iya kayar da Shugaba Bola Tinubu.
Kwamred Murtala Mohammed ya kuma yaba da ƙoƙarin Alhaji Musa Ibrahim Na-banki wajen kafa Ƙungiyar Ƴan Dan-Gwalen Atiku, domin tallafa wa takarar Atiku.
Asali: Legit.ng

