Duniyar Musulmi Ta Yi Rashi: Malamin Musulunci Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

Duniyar Musulmi Ta Yi Rashi: Malamin Musulunci Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

  • Rahotanni sun tabbatar da rasuwar Sheikh Tirmidhy UsamatAn wani fitaccen malamin Musulunci a Kudu maso Yammacin Najeriya ya
  • An gudanar da sallar jana’izar marigayin ranar Lahadi, 30 ga Agusta, a Idiagblumo, yankin Kelebe, Osogbo, babban birnin Osun
  • Sheikh Onisuru Imotola da wasu majiyoyi daga cikin al’ummar Musulmi sun tabbatar da rasuwar, inda suka bayyana shi a matsayin malami mai kishin addini

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Osogbo, Osun - Al'ummar Musulmi a Najeriya sun tafka babban rashi bayan sanar da rasuwar malamin Musulunci a Osun.

Sheikh Tirmidhy Usamat, fitaccen malamin Musulunci da ke zaune a Kudu maso Yammacin Najeriya, ya rasu ranar Asabar, 29 ga Agusta, 2026.

Babban malamin Musulunci ya rasu a Osun
Taswirar jihar Osun da ke Kudancin Najeriya. Hoto: Legit.
Source: Original

Wani malamin addini, Sheikh Onisuru Imotola ne ya sanar da rasuwar marigayin a wani sakon Facebook a yau Lahadi 30 ga watan Agustan 2026.

Kara karanta wannan

Mazauna kwaryar Gombe sun shiga jimami da aka sanar da mutuwar Sarki

An yi rashin babban malamin Musulunci

Majiyoyi da dama daga cikin al’ummar Musulmi sun tabbatar da rasuwar malamin, tare da bayyana alhininsu kan wannan babban rashi.

Sheikh Onisuru Imotola ya bayyana cikakken mukamin marigayin a cikin sakon ta’aziyyar da Minhaju-l-Mubarak TV ta sake wallafawa.

Ya ce:

“Cike da alhini muke sanar da rasuwar masoyinmu Fadheelatu Sheikh Tirmidhy Usamat, Mudeeru-l-Minhaj, Nakeebu-l-Ashrof - babban malamin Musulunci, malami kuma bawan Addini.”
Malamin Musulunci ya rasu a Osun
Marigayi Sheikh Tirmidhy Usamat a jihar Osun. Hoto: Minhaju-I-Mubarak TV.
Source: Facebook

An bayyana gudunmawar marigayin da Musulunci

Imotola ya yaba da irin gudunmawar Sheikh Tirmidhy Usamat wajen neman ilimin addini da koyar da Musulunci ga al’umma.

Ya bayyana cewa iliminsa, shawarwarinsa da abubuwan alheri da ya bari za su ci gaba da amfani ga mutanen da ya koyar.

Ya ce:

“Allah Ya gafarta masa, Ya sanya shi cikin Aljannar Firdausi, Ya kuma sanya ilimin da ya bari ya zama Sadakatul Jariya.”

Malamin ya kuma yi kira ga Musulmi da su ci gaba da tuna marigayin a cikin addu’o’insu bayan rasuwarsa.

Kara karanta wannan

Babban malamin Musulunci, Sheikh Anchau ya rasu, Jingir ya masa jana'iza

Har yanzu ba a bayyana musabbabin mutuwar Sheikh Tirmidhy Usamat ba, yayin da aka gudanar da sallar jana’izarsa ranar Lahadi 30 ga watan Agustan shekarar 2026 da rana.

An gudanar da sallar jana’izar ne a yankin Idiagblumo, Kelebe, da ke Osogbo, babban birnin Osun, kamar yadda rahotanni suka bayyana.

Mutuwar marigayin ta tayar da hankalin mutanen yankin da sauran yan uwa Musulmi musamman waɗanda suka sanshi ko suka yi mu'amala da shi kafin rasuwarsa.

Marigayin ya sha ruwan addu'o'i daga mutane da dama inda suka bayyana shi a matsayin mutumin kirki da ya ba Musulmi da sauran al'umma gudummawa a rayuwarsu.

Babban limamin Shonga ya bar duniya

A wani labari makamancin haka, Alhaji Jibril Baba Nnatakun, babban limamin Shonga, ya rasu bayan shekaru da dama yana jagorantar al’ummar Musulmi.

Shonga tsohuwar al’ummar Nupe ce da ke cikin ƙaramar hukumar Edu ta Kwara, kuma tana kusa da gabar Kogin Neja.

Rasuwar shugaban addinin ta jawo jimamin al’ummar Musulmi da shugabannin yankin, ciki har da Mohammed Baba Ibrahim, wanda aka fi sani da MBI.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.