Najeriya da Arewa Sun Yi Rashi da Shugaban AFAN da PAN Ya Rasu

Najeriya da Arewa Sun Yi Rashi da Shugaban AFAN da PAN Ya Rasu

  • Architect Kabir Ibrahim Faskari, tsohon shugaban AFAN da PAN, ya rasu a Istanbul, Turkiyya, bayan matsalolin da suka biyo bayan tiyatar prostate.
  • Faskari ya kasance fitaccen mai fafutukar bunƙasa noma, kiwon kaji, samar da abinci da kasuwancin noma a Najeriya.
  • Wata majiya ta ce za a binne Kabir Ibrahim Faskari a kasae Turkiyya, yayin da aka bayyana musabbabin mutuwarsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Istanbul, Turkiyya - Architect Kabir Ibrahim Faskari, tsohon shugaban kungiyar manoma ta Najeriya (AFAN) da kungiyar masu kiwon kaji ta Najeriya (PAN), ya rasu a Turkiyya.

Faskari, wanda kuma shi ne shugaban Agriculture Business Group na yanzu, ya rasu a birnin Istanbul bayan fama da matsalolin lafiya da suka biyo bayan tiyatar prostate.

Allah ya yi wa Kabir Ibrahim Faskari rasuwa
Marigayi Architect Kabir Ibrahim Faskari Hoto: Mobile Media Crew
Source: Facebook

Matsalolin da suka biyo bayan tiyata

Wani abokin marigayin ne ya tabbatar da rasuwarsa, inda ya bayyana cewa wasu daga cikin abokan aikinsa sun ziyarce shi a Istanbul kwanakin baya, cewar rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Da gaske hukumar Hisbah ta hana Kiristoci gudanar da ibada a Sokoto

A cewar abokin nasa, mutanen sun samu damar tattaunawa da Faskari kafin su dawo Najeriya, amma daga baya lafiyarsa ta samu matsala sakamakon tiyatar da aka yi masa.

Wata majiya ta kuma bayyana cewa za a binne marigayin a Turkiyya, sai dai ba a samu cikakken bayani kan ranar da wurin da za a gudanar da jana’izarsa ba.

Fitaccen mai fafutukar noma

Faskari ya kasance ɗaya daga cikin fitattun muryoyi a fannin noma da samar da abinci a Najeriya.

Ya taka muhimmiyar rawa a ƙungiyoyin manoma, musamman a lokacin da yake jagorantar AFAN da PAN.

A tsawon rayuwarsa, ya yi fice wajen magana kan matsalolin da ke addabar manoma da masu kiwon kaji, da kuma hanyoyin bunƙasa samar da abinci a Najeriya.

Ya kuma kasance mai bayar da shawarwari kan harkokin kasuwancin noma da manufofin da suka shafi samar da abinci a ƙasar.

Gudunmawarsa ga fannin noma

Faskari ya sha tattaunawa da kafafen yaɗa labarai kan batutuwan noma da samar da abinci.

Kara karanta wannan

'Ban da Atiku,' Dan takara 1 da ya bugu kirji kan shi kadai zai iya maido tallafin mai

A cikin hirarrakin nasa, ya rika bayyana matsalolin da manoma ke fuskanta tare da bayar da shawarwari kan yadda za a inganta fannin noma da rage dogaro da kayan abinci daga ƙasashen waje.

Rasuwarsa ta jawo alhini a tsakanin masu ruwa da tsaki a harkar noma, musamman waɗanda suka yi aiki tare da shi a ƙungiyoyin manoma da kasuwancin noma.

Ibrahim Kabir Faskari ya rasu
Taswirar jihar Katsina, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Ana sa ran za a fitar da ƙarin bayanai kan rasuwarsa da shirye-shiryen binne shi a Turkiyya.

Katsina Post ta kawo rahoton cewa za a gudanar da salatul Gha’ib gudanar da Sallar Gha’ib (Salatul Gha’ib) ga marigayin a birnin Katsina.

Za a gudanar da sallar a masallacin Imran Islamic Centre, kusa da Sabon Gari Police Station, Katsina a ranar Lahadi, 30 ga watan Agustan 2026 da karfe 5:00 na yamma.

Tsohon sanata ya rasu

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon sanatan Borno ta Tsakiya a Majalisar dattawan Najeriya, Kaka Mallam Yale, ya riga mu gidan gaskiya bayan fama da rashin lafiya.

Marigayi Sanata Kaka Yale ya rasu ne a safiyar Juma’a, 28 ga watan Agusta, 2026 a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri da ke birnin Maiduguri na jihar Borno.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng