Manyan Dalilai4 da Suka Sa Tinubu Ke Neman FBI Ta Killace Sirrinsa na Amurka
- Shugaban Najeriya Bola Ahmad Tinubu ya roki kotun Amurka ta dakatar da fitar da takardunsa na FBI da DEA domin kariya ta sirri
- Lauyoyinsa sun ce babu wata fa'ida ga jama'a a lamarin kuma suna zarginsa ne da neman kulla masa makarkasiya ta siyasa
- Rigimar ta sake rura wutar cece-kuce kan tarihi da rayuwar baya ta Tinubu yayin da 'yan adawa ke neman gaskiyar yadda lamarin yake
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Washington - Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya bukaci Babban Kotun Tarayya ta Amurka da ke Gundumar Columbia da ta dakatar da fitar da takardunsa na sirri da ke hannun hukumomin FBI da DEA.
Lauyoyin shugaban kasar, Christopher Carmichael da Victor Henderson da kuma Oluwole Afolabi sun gabatar da manyan dalilai guda hudu a takardun da suka shigar a kotu kamar yadda rahotanni suka tabbatar.

Source: Getty Images
1. Dokokin FOIA da hakkin sirri sun hana fitar da takardun
Tawagar lauyoyin Tinubu ta bayyana cewa dokar 'yancin samun bayanai ta Amurka (FOIA) da Dokar Sirri sun hana fitar da bayanan sirrin mutum.

Kara karanta wannan
Zargin safarar kwaya: Tinubu ya kawo dalilai 4 ga kotun Amurka kan sakin sirrinsa
Sun dogara ne da sashe na Exemption 7(C) wanda ke kare bayanan sirrin mutum a cikin takardun hukumomin tsaro.
2. Babu muradin jama'a wajen fitar da bayanan
Lauyoyin sun jaddada cewa babu wani muradi na jama'a da za a kwatanta da hakkin shugaban kasa na sirri, musamman irin wannan.
Sun yi watsi da ikirarin cewa sha'awar 'yan Najeriya ta sanin takardunsa ta kai matsayin muradin jama'a a karkashin dokar Amurka.
3. Muradin siyasa kan batun sakin takardun
Lauyoyin sun zargi dan rajin kare gaskiya na kasar Amurka, Aaron Greenspan, da neman takardun bisa dalilai na siyasar Najeriya.
Lauyoyin Tinubu sun ce babban burin Greenspan kawai shi ne samun takardun da ke dauke da sunan shugaban kasar saboda wata manufa kan siyasar Najeriya.
4. Zarge-zargen da ba su da tabbas ba su wadatar ba
Lauyoyin sun yi fatali da zarge-zargen cewa takardun na iya bayyana wata shari'ar sirri ko yarjejeniya da hukumomin Amurka.
Sun bayyana cewa irin wadannan zarge-zarge na hasashe ne kawai kuma ba su da wata hujja ta shari'a.
Kitimurmurar sanin tarihin baya na Tinubu
Tattaunawa kan tarihin Tinubu da hukumomin tsaron Amurka ta yi zafi ne tun lokacin zaben shugaban kasa na watan Fabrairun 2023.
Takardun wata shari'a ta 1993 sun nuna cewa kotun Amurka ta sa a kwace dala $460,000 daga asusun Tinubu saboda zargin alaka da harkar kwayoyi.
Jam'iyyar APC ta kafe kan cewa hakan ya kasance ne ta hanyar kwace dukiyoyi bisa wani la'akarin daban, ba hukuncin laifin aikata laifin ta'addanci ba. Sai dai jam'iyyun adawa irin su Labour Party da dan takararta Peter Obi sun rika cewa wannan ya kai matsayin laifin da zai hana shi takara.
A watan Satumban 2023, Kotun Sauraron Kararakin Zaben Shugaban Kasa ta yanke hukuncin cewa masu shigar da kara sun gaza tabbatar da cewa an kama Tinubu ko an tura shi kotu ko daure shi a Amurka.
Sai dai, har yanzu ana ci gaba da bayyana zargi da rashin gamsuwa da ingancin Tinubu na ya mulki kasa mai bin doka da oda kamar Najeriya.
Wanda ya tantance Salisu Ibrahim, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
