Yadda Kirista Ya Gina Katafaren Masallacin Juma'a ga Musulmi a Plateau

Yadda Kirista Ya Gina Katafaren Masallacin Juma'a ga Musulmi a Plateau

  • Wani mabiyin addinin Kiristanci a jihar Plateau ya ba mutane mamaki bayan gina katafaren masallacin Juma'a a yankinsa
  • Mutumin da ake kira Peter Ibrahim Gyendyeng ya gina masallacin a garin Gana Ropp da ke Barkin Ladi, domin Musulmi
  • Gyendyeng, tsohon ɗan Majalisar Wakilai ne, ya ce ya gina masallacin ne a matsayin alamar haɗin kai tsakanin Kiristoci da Musulmi a Plateau

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Gana Ropp, Plateau - Wani Kirista mazaunin jihar Plateau, Peter Ibrahim Gyendyeng ya yi ƙoƙari bayan gina masallacin Juma'a.

Gyendyeng ya gina masallacin ne na Juma’a domin al’ummar Gana Ropp da ke ƙaramar hukumar Barkin Ladi.

Kirista ya gina masallacin Juma'a a Plateau
Tsohon ɗan majalisar wakilai, Peter Ibrahim Gyendyeng da masallacin Juma'a da ya gina a Plateau. Hoto: Peter Ibrahim Gyendyeng.
Source: Facebook

Wakilin Daily Trust ya ruwaito cewa wannan lamari ya zo ne a lokacin da ake fama da tashe-tashen hankula a wasu sassan Plateau, ciki har da Barkin Ladi, inda dangantakar Kiristoci da Musulmi ta kasance cikin wani hali a baya-bayan nan.

Kara karanta wannan

Da gaske hukumar Hisbah ta hana Kiristoci gudanar da ibada a Sokoto

Farin cikin da Musulmi suka yi a Plateau

Ginin masallacin ya faranta wa Musulmi sosai yankin, waɗanda suka bayyana wannan mataki a matsayin wata hanya ta nuna cewa ana damuwa da su.

Sai dai yayin ƙaddamar da masallacin, Gyendyeng, ya bayyana cewa ya gina wurin ibadar ne domin Musulmi su yi amfani da shi a matsayin alamar haɗin kai tsakanin mazauna yankin da jihar baki ɗaya, ciki har da Kiristoci da Musulmi.

A cewar Gyendyeng, duk wani kuɗi da aka bai wa wasu daga cikin al’ummar Musulmi zai iya ƙarewa cikin ɗan lokaci.

Ya ce ba za ka iya yin wani abu da zai faranta ran kowa ba, amma gina musu wurin ibada da za su riƙa yin addu’ar zaman lafiya da ci gaban ƙasa ya fi dacewa.

Ya ƙara da cewa wata hanyar taimaka wa mutane ita ce ba su abin da suke matuƙar buƙata ko kuma abin da suke darajawa.

Kara karanta wannan

Kirista ya lashe gasar Kur'ani, ya samu kyautar kujerar Umrah

Musulmai sun yi farin ciki da Kirista ya gina masallaci
Taswirar jihar Plateau da Kirista ya gina wa Musulmi masallacin Juma'a. Hoto: Legit.
Source: Original

Babban limamin masallacin ya yaba wa Gyendyeng

Da yake mayar da martani kan wannan ci gaba, Babban Limamin masallacin, Sheikh Ladan Gana Ropp, ya ce al’ummar yankin na farin ciki da aikin, kuma sun yi imanin cewa ya sa sun ji kamar suna gida.

Ya ce:

“A gaskiya, mun yi farin ciki lokacin da ya gina masallacin. A yanzu ba ya riƙe da wani mukamin siyasa, amma har yanzu ya iya aiwatar da irin wannan aiki, ba mu taɓa ganin wani aiki irin wannan a yankin ba har zuwa yanzu. Muna matuƙar godiya, kuma hakan ya ba mu damar jin cewa muna da muhimmanci.
“Idan ya ba mu kuɗi, za mu kashe su su ƙare, amma wannan aikin ba za mu taɓa mantawa da shi ba, lokacin ƙaddamar da masallacin, duk mun haɗu domin yin addu’a a gare shi, gwamnatin jihar da ƙasar baki ɗaya."

Babban Limamin ya yi kira ga Kiristoci da Musulmi a yankin da Plateau baki ɗaya da su rungumi zaman lafiya, haɗin kai da haƙuri domin ci gaban bil’adama.

Kara karanta wannan

Fin karfi: Ana zargin Kwamishina ya raba aure, ya lallaba ya auri matar a Zamfara

Majiyoyi sun ruwaito cewa fastoci, limamai, reverends da sauran mambobin al’ummar Kirista sun halarci bikin ƙaddamar da masallacin.

Matar Tinubu ta bude sabon masallacin Juma'a

An ji cewa uwargidan shugaban kasa, Sanata Oluremi Tinubu, tare da mataimakin gwamnan Lagos sun kaddamar da sabon babban masallaci.

An gina masallacin ne a Odo Noforija a garin Epe wanda Sarki Babatunde Ogunlaja da Alhaji Abdul Jelili Animashaun suka gina.

Jami’an gwamnati da manyan baki sun yabawa aikin, suna cewa hadin kai tsakanin Musulmi da Kiristoci alama ce ta zaman lafiya da ci gaba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.