'Yadda Tinubu Ya Yi Ƴan Dabaru domin Farfaɗo da Tattalin Arzikin Najeriya'
- Ministan Kuɗi a Najeriya, Taiwo Oyedele ya yi magana game da yadda tattalin arzikin kasar ya daidaita a mulkin Bola Tinubu
- Oyedele ya ce hauhawar farashi ta ragu zuwa kashi 15.43, yayin da ajiyar kuɗin waje ya kai dala biliyan 51.96, mafi yawa tun 2009
- Majalisar Tattalin Arziki ta Ƙasa ta yi gargaɗin ka da a sauya manufofin gyaran tattalin arziki, musamman yayin da ayyukan siyasar 2027 ke ƙara ƙamari
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Ministan Kuɗi kuma Ministan da ke Kula da Tattalin Arziki, Taiwo Oyedele, ya bayyana wani rahoto mai daɗi game da halin tattalin arzikin Najeriya.
Oyedele ya fadi hanyoyin da gwamnatin Bola Tinubu ya bi domin farfaɗo da tattalin arzikin kasar.

Source: Twitter
'Tinubu ya farfaɗo da tattalin arzikin Najeriya'
Da yake yi wa ’yan jarida bayani bayan kammala taron Majalisar Tattalin Arziki ta Ƙasa karo na 160, Oyedele ya ce tattalin arzikin ƙasar ya samu daidaito, cewar TheCable.
Ya ce yanzu gwamnatin tarayya za ta mayar da hankali wajen amfani da wannan daidaito domin samar da ci gaban tattalin arziki da zai amfani kowa.
Ministan ya kawo ƙarin GDP, raguwar hauhawar farashi, ƙaruwa mai yawa a ajiyar kuɗin waje da raguwar kaso na kuɗin biyan bashin gwamnati.
Ya kuma ambaci ƙarin kuɗaɗen shiga na asusun tarayya a matsayin hujjojin da ke nuna cewa gyare-gyaren tattalin arzikin gwamnatin yanzu sun fara haifar da sakamako.
Ya ce:
“Tattalin arzikin Najeriya ya daidaita, kuma aikin da ke gabanmu yanzu shi ne mayar da wannan daidaito zuwa ci gaban tattalin arziki da zai amfani kowa, haƙiƙanin ƙimar ci gaban GDP ɗinmu ya kai kashi 3.89 cikin kwata na farko na 2026, daga kashi 3.13 a daidai wannan lokaci bara.
“Ana hasashen cewa GDP ɗin Najeriya zai haura kashi 4 cikin 100 a shekarar 2026, idan aka ci gaba da tafiya da wannan yanayin, jimillar hauhawar farashi ta sauka zuwa kashi 15.43 a ƙarshen watan Yuli, daga kashi 24.94 a daidai wannan lokaci na bara.
Ya kwatanta da kashi 26.2 a daidai wannan lokaci na bara, abin da ke nuna cewa matsin farashin abinci ya fara raguwa.

Source: Twitter
Shaidar da gwamnatin Tinubu ta samu
Ministan ya kuma bayyana cewa manyan hukumomin tantance darajar tattalin arziki a duniya sun amince da kyakkyawan sauyin da Najeriya ta samu, cewar Punch.
Ya ce:
“Dukkan manyan hukumomin tantance darajar bashi guda uku, Fitch, Moody’s da S&P, sun yi wa Najeriya ƙarin daraja tsakanin Afrilu 2025 da Mayu 2026, wannan shi ne karo na farko cikin fiye da shekaru goma da waɗannan hukumomi suka yi irin wannan matsaya mai kama da juna kan Najeriya.
“Najeriya ta kuma fice daga jerin ƙasashen da Financial Action Task Force ke sa ido na musamman a kansu tun watan Oktoban 2025, ta kuma fice daga jerin Tarayyar Turai na ƙasashen da ke da gibi wajen yaƙi da safarar kuɗaɗen haram da tallafin ta’addanci tun Janairun 2026."
Oyedele ya shaida wa wakilan Fadar Shugaban Ƙasa cewa FTSE Russell, wani babban kamfanin duniya da ke samar da bayanan kasuwannin hannayen jari, ya sake rarraba Najeriya.
A cewarsa, Majalisar Tattalin Arziki ta Ƙasa ta kuma yanke shawarar hanzarta bunƙasa noma, makamashi, masana’antu, ma’adinai da kuma tattalin arzikin dijital.
Atiku ya fadi shekarun Tinubu a duniya
An ji cewa dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar ADC a zaben 2027, Atiku Abubakar ya ce yana da hujjar da ke nun asalin shekarun Bola Tinubu.
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce yana da shaidar cewa Shugaba Bola Tinubu yana da shekara 90 a duniya.
Atiku ya ce a shirye yake ya gabatar da hujja a gaban kotu idan aka kai shi kara, yana mai jaddada bukatar magance matsalar tsaro.
Asali: Legit.ng


