Zargin Safarar Kwaya: Tinubu Ya Kawo Dalilai 4 ga Kotun Amurka kan Sakin Sirrinsa

Zargin Safarar Kwaya: Tinubu Ya Kawo Dalilai 4 ga Kotun Amurka kan Sakin Sirrinsa

  • Shugaba Bola Tinubu ya bukaci kotun Amurka ta hana sakin cikakkun bayanan FBI da DEA da suka shafe shi
  • Lauyoyin Tinubu sun ce bukatar sakin bayanan na da nasaba da siyasar Najeriya, kuma ba ta nuna wata hujja ta aikata laifi ko rashin bin doka ba
  • Jam’iyyun ADC da NDC sun ce ya kamata a saki bayanan domin ’yan Najeriya su san gaskiya, tare da bukatar Tinubu ya wanke kansa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Shugaba Bola Tinubu, ya gabatar da dalilai guda hudu ga Kotun Amurka kan dalilin da ya sa bai kamata a bayyana cikakkun bayanansa na zargin sadarar kwaya.

Tinubu, ta hannun lauyoyinsa, ya ce dokar Amurka ta yancin bayanai da sirri sun hana bayyana bayanan, sannan babu wata maslahar jama’a da ta isa ta tilasta fitar da su.

Kara karanta wannan

Da gaske hukumar Hisbah ta hana Kiristoci gudanar da ibada a Sokoto

Tinubu ya yi magana kan zarginsa da safarar kwaya a Amurka
Shugaba Bola Tinubu yayin taro a Abuja. Hoto: Aswaju Bola Tinubu.
Source: Facebook

Ya kuma ce babu wata maslahar jama’a da za a daidaita da bukatar bayyana bayanan, yayin da mai neman bayanan ke da wasu manufofi na siyasa da suka wuce bukatar samun bayanai, cewar Punch.

Wadanda suka tsayawa Tinubu a lamarin

Lauyoyin shugaban kasa Bola Tinubu sun hada da Christopher Carmichael, Victor Henderson da Oluwole Afolabi.

Matsayar Tinubu ta biyo bayan bukatar wani mai fafutukar neman gaskiya a Amurka, Aaron Greenspan, wanda ya nemi a bayyana bayanan bisa dokar.

Sai dai jam’iyyun adawa a Najeriya sun yi watsi da matakin, suna cewa ’yan Najeriya suna da hakkin sanin abubuwan da suka shafi tarihin shugaban kasar.

Dalilan Tinubu kan bayanan da za a sake

A cikin martanin da lauyoyin Tinubu suka gabatar, shugaban ya bukaci Kotun Tarayyar Amurka ta yi watsi da bukatar, yana cewa neman bayanan wani mutum ne na kashin kansa domin dalilan siyasa a Najeriya.

Lauyoyin sun ce Greenspan ya yi amfani da hujjar cewa bukatar ta shafi samun bayanai kan ayyukan gwamnati.

Kara karanta wannan

Fadar shugaban kasa ta sake gano lam'a a shirin Atiku na dawo da tallafin fetur

Sai dai sun yi watsi da ikirarin cewa sha’awar ’yan Najeriya kan tarihin Tinubu na cikin irin maslahar jama’a da dokokin Amurka suka amince da ita.

Lauyoyin sun kuma yi watsi da hujjar da ta shafi cancantar Tinubu na rike mukamin shugaban kasa, suna cewa maslahar jama’a kan cancantarsa ba wata maslaha ce da dokar FOIA ta amince da ita ba.

Sun ce manufar FOIA ita ce bai wa jama’a damar sanin abin da gwamnati ke yi, ba wai ba su damar samun bayanan sirrin wasu mutane ba.

A cewarsu, Greenspan yana neman bayanan wasu mutane da aka tattara a cikin fayilolin gwamnati, wadanda ba sa bayyana komai ko kadan game da yadda hukumar da kanta ta gudanar da aikinta.

Lauyoyin Tinubu sun kuma kalubalanci abin da suka bayyana a matsayin bangaren siyasa na bukatar Greenspan.

Sun ce bayanan da Greenspan ya gabatar sun nuna cewa babban burinsa shi ne samun takardun gwamnati da ke dauke da sunan Tinubu.

Sun kara da cewa Greenspan bai gabatar da hujjar da za ta tabbatar da cewa wani laifi ko rashin bin doka daga gwamnati ya faru ba.

Kara karanta wannan

Magana ta girma: Atiku na neman bahasi daga Tinubu kan kudaden cire tallafi

Tinubu ya kare kansa kan zargin safarar kwaya
Shugaba Bola Tinubu na Najeriya. Hoto: Bayo Onanuga.
Source: Facebook

Tinubu na neman a boye bayanansa

Lauyoyin shugaban sun kuma yi watsi da hujjar cewa sirrin Tinubu ya daina kasancewa sirri saboda wasu bayanai kan binciken da aka yi a baya sun taba bayyana a bainar jama’a.

Greenspan ya yi ikirarin cewa bayanan gaba daya game da binciken sun kasance cikin bayanan jama’a tun shekarar 1993.

Sai dai lauyoyin Tinubu sun ce shari’ar kwace kudin ta shekarar 1993, ciki har da takardar rantsuwa da aka gabatar, ba ta bayyana cikakkun bayanai ko sakamakon wani binciken laifi da zai iya shafar shugaban ba.

Sun ce ko da wasu bayanai sun taba bayyana a cikin takardun jama’a, mutum na iya ci gaba da samun hakkin sirri kan wasu bayanan da ba a bayyana ba.

ADC da NDC sun tsoma baki kan lamarinyan

Da yake tsokaci kan lamarin, jam’iyyun ADC da NDC sun ce kin sakin bayanan da Tinubu ya yi na da alamun shakku.

Kara karanta wannan

'Ba da yawun Musulmin Najeriya ba': ADC ta soki Malamai kan neman a zabi Tinubu

Mai magana da yawun ADC, Bolaji Abdullahi, ya bukaci shugaban ya amince da sakin bayanan domin kare mutuncinsa.

Shi ma Sakataren Yada Labarai na NDC, Osa Director, ya ce ’yan Najeriya sun cancanci sanin gaskiya, yana kira ga Tinubu da ya amince da sakin bayanansa da ke hannun hukumomin Amurka.

Zargin safarar kwaya: Buratai ya kare Tinubu

An ji cewa Laftanar Janar Tukur Buratai mai ritaya ya bukaci ’yan Najeriya su yi watsi da tsoma bakin ƙasashen waje.

Buratai ya ce zarge-zargen da suka shafi Shugaba Bola Tinubu tun shekaru 33 da suka wuce bai kamata su ayyana makomar Najeriya ba.

Ya kuma bukaci shugabannin siyasa su haɗa kai, yana gargadin cewa sakin takardun binciken na iya cutar da tattalin arziki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.