Daraktan Yakin Neman Zaben Tinubu, Abdulaziz Yari Ya Yi Magana kan Dawo da Tallafin Fetur
- Darakta Janar na kwamitin yakin neman zaben Bola Tinubub a 2027, Sanata Abdul'aziz Yari ya maida martani ga Atiku Abubakar kan dawo da tallafin mai
- Sanata Abdulaziz Yari ya ce duk wanda ya yi alkawarin dawo da tallafin man fetur yana yaudarar ’yan Najeriya ne kurum amma hakan ba zai yiwu ba
- Yari ya ce APC za ta mayar da hankali kan nasarorin gwamnatin Bola Tinubu da shirye-shiryenta a yaƙin neman zaɓen 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Sanata Abdulaziz Yari, mai wakiltar mazabar Zamfara ta Yamma kuma Darakta-Janar na kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na APC, ya yi fatali da yunkurin dawo da tallafin mai.
Sanata Yari ya bayyana cewa duk wanda zai fito ya yi wa ’yan Najeriya alkawarin dawo da tallafin man fetur yana yaudararsu kawai.

Source: Facebook
The Cable ta ce Yari, wanda tsohon gwamnan Jihar Zamfara ne, ya bayyana hakan ne ranar Asabar lokacin da mambobin kwamitin gudanarwa na ƙasa (NWC) na APC suka kai masa ziyarar ban girma.
Ya mayar da martani ne kan alkawarin tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, na dawo da tallafin man fetur idan aka zaɓe shi shugaban ƙasa a 2027.
Atiku, wanda shi ne ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC, ya ce zai dawo da wani tallafi na musamman, yana mai cewa gwamnati ta gaza bayyana abin da ta yi da kuɗin da aka samu bayan cire tallafin.
Shin za a iya dawo da tallafin mai?
Yari ya ce babu tanadin tallafin man fetur a cikin kasafin kuɗin shekarar 2023 da Majalisar Dokoki ta Ƙasa ta amince da shi kafin Shugaba Bola Tinubu ya hau mulki.
“Kafin Asiwaju ya zo a 2023, babu kasafin kuɗin tallafi. Majalisar Dokoki ta Ƙasa ta amince da kasafin kuɗin a watan Maris, amma babu tanadin tallafi a kasafin kuɗin 2023. Ta yaya za a gudanar da shi?
“Duk wanda yake yaudarar ’yan Najeriya yana cewa zai dawo da wannan abu, yana yaudarar kansa, yana yaudarar ’yan Najeriya,” in ji shi.

Source: Facebook
Sanata Yari ya tuna kudin da ake kashewa
Daraktan-Janar na kwamitin yaƙin neman zaɓen APC ya kuma tambayi adadin kuɗin da ake kashewa kan tallafin man fetur da kuma rashin cikakken bayani kan ainihin yawan man da Najeriya ke amfani da shi a kowace rana.
Yari ya ce ana kashe kusan Naira tiriliyan 20 a shekara kan wannan tsari, amma babu wanda zai iya tabbatar da ainihin adadin litar man da ake buƙata a kullum.
Ya ce APC za ta gina yaƙin neman zaɓenta na 2027 ne kan abubuwan da gwamnatin Tinubu ta cimma da kuma shirye-shiryenta na gaba, maimakon tsayawa musayar yawu.
Minista ya maida martani ga Atiku
A wani labarin, kun ji cewa Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ya ce iyakokin Najeriya ba a rufe suke ba, don haka babu abin da za a sake budewa.
Ya kalubalanci Atiku Abubakar da ya gabatar da cikakkiyar manufa kan kula da iyakokin kasar maimakon hada batutuwan kasuwanci da tsaro.
Asali: Legit.ng

